Chapter 67
Chapter 67
a 9ja bai dawoba a yanda ya hasaso, inma ya shigo India bazai dinga wuce sati biyu zuwa uku ba zai barta, shima saboda Company nasune, danma yanata k'ok'arin ganin sunzo sun kafa reshe a Nigeria dan shima yabada gunmawa ga k'asarsa. Muma dake cikin gidan bawani zaman mukeba, munata kimtse-kimtsen kayan gidan waje d'ayane. Da sallama da mak'wafta da abokan arzik'i da akai sabo. A wannan yanayinne na gane Ashe yayan Dhibya Gopal soyayya suke da Samha, wannan ne kusancin dake k'ara k'arfi tsakanin Dhinya da Samha, ban sanarma kowaba, haka itama ban mata maganaba, tunda gashi ALLAH ya kawo sanadin da zasu nisanci juna cikin sauk'i, babu yanda za'ayi aure ya iya yuwuwa a tsakaninsu, yaudarar juna kawai sukeyi, Su Dhibya y'an k'abilar Hindu ne, kuma mabiya wannan addini masu tsananin ak'ida, Galadima ya ta6a sanarmin iyayensu sun dad'e basu saki jiki dasuba saboda kasancewarsu musulmai kawai, Gopal kusan sa'anni suke dashi amma babu wata shak'uwa tsakaninsu. To tayaya suke tunanin k'ulluwar aure a tsakaninsu inba Gopal musulunta zaiyiba, hakan kuma abune mai wuyar gaske, dukda ba'a yanke hujunci da ikon ALLAH. Ana gobe zamu wuce saudia Galadima ya sallami Khumar da kuku, wad'anda suke kuka da idanunsu na bak'in cikin rabuwa damu, muma kuma hakanne, sai da Galadima yamusu bayani akan badan shima bayason rayuwa dasu ya sallamesuba, sai dan karya tauye hak'insune, yabasu Dama suje su nemi wasu ayyukan, duk sanda ya shigo k'asar zai nemesu su dawo kan aikinsu insha ALLAH. Sunyi murna sosai da bayaninsa, haka muma munji dad'in hakan, domin kuwa dai ba'a rabuba kenan. *_KOMAI YAY FARKO...😭👎🏻_* Zai iya zama k'arshe watan watarana, yau ga Abie daya shigo India cikin tsananin ciwo da fidda rai daga rayuwa zai barta cikin farin ciki da k'warin gwiwar rahma da falalar ubangijin al'arshi. Fuskokinmu kawai sun isa shaida maka muna cikin farin ciki muma. Mun tafi cikin kewar India da jama'ar cikinta, musamman ma Momma da Abie da tunda suka shigota sai yaune zasu barta. Tunkan mu Isa Galadima ya sanya Sultan nema mana masauki. Muna sauka kuwa cikin mutunci akazo aka d'aukemu zuwa matsakaicin gida dazai d'aukemu babu wata takura. Har kuka saida nayi a 6oye ganina a inda ban ta6a zato ko tsammaniba, kasa mai tsarki. Hutun wannan ranar kawai muka samu, washe gari muka duk'ufa ibada da godiyar Ubangiji bisa ga ni'imomi dayay mana badan munfi sauran bayinsa da komaiba. Tsawon kwana goma muna bautar Ubangiji, a randa ake saran ganin wata jirginmu ya d'aga zuwa k'asarmu ta haihuwa, Abie da Momma sunfi kowa zumud'i da k'aguwa. Babu wanda yasan da zuwanmu sai Sarkin Mota, shima kuma bashi da tabbacin dawa za'azo d'in, Galadima dai yace ya saka a gyara masa 6angarensa da inda su Aunty Mimi ke sauka. *************** Jirginmu ya sauka 9ja k'arfe 11:30pm. Mu muka fara fitowa, Abie da Galadima suka zama k'arshe. Abie na sauka a jirgin yana Murmushi da hawaye, tareda shak'ar iskar k'asarsa daya bari tsawon shekaru, yama fidda ransa da kuma dawowa cikinta har Abadan. Sarkin Mota da dogaran Galadima suna zaune a airport d'in suna jiran isowarmu. Ganinmu da yawa yabasu mamaki, amma saisuka zube suna gaishemu, a cikinsu babu Wanda ya gane momma da Abie, Bama zai yuwu su ganesu d'inba, tunda sanda yabar k'arsar duk basa a wannan matsayin, sai dai iyayensu, wanda a halin yanzu mafi yawa acikinsu duksun rasu ma. Dole saida muka k'ara da motocin haya, Momma da Abie suka shiga wadda sarkin Mota ke ja, Ni da Galadima da Samha muka shiga ta haya d'aya, Aunty Mimi da Yaa Sauban da yara suka shiga d'aya. Mun Isa Masarautar tsit babu yawan hayaniya alamar mafi yawan al'ummar cikinta sun nutsu waje d'aya, sai wasu tsirarun hadimai dake kai kawo mussamman masu tsaro. Duk muka fito amma banda su Momma, Galadima ya nufi mortar dan son taimakawa Abie fiwo, Sarkin Mota kuma na k'ok'arin biyan masu motarnan kud'insu. Fir Abie yak'i fita, yace d'an uwansa mai martaba ne kad'ai zai fiddashi a motar, duk rok'on da sukai masa fir yak'i, gashi yanata sharar hawaye da handkerchief. Galadima yasan yanzu Mai martaba ya shiga ciki, maybe ma matar dake dashi taje. Rasa yama zaiyi yayi. Momma Ce tabashi shawarar kiran wayar mai martaba, cikin damuwa Galadima ya kar6a wayan Sauban dabe dad'e da barin k'asarba, sim card d'insa zaifi saurin aiki fiye da nashi. Hadiman gidan sund'an fara fuskantar akwai matsala gameda tsayuwar su Galadima, dan wannan ba halinsa bane. ALLAH ma ya taimaka Mai martaba baiyi barciba, yana zaune ne yana duba wasu takardu, matarsa ta biyu na tare dashi dan yau kwanantane. Ya dad'e yana kallon wayar da nazarin mai kiransa, dan ba kowane keda Number mai martaba, sai jiga-jigai irinsu Galadima d'in. Tamkar bazai d'aukaba yad'ai d'auka tana gab da katsewa a kira karo na biyu. Cikeda girmamawa Galadima ya gaishesa sanann yay masa bayanin shine. Da farko mai martaba tsorata yayi, dan babu Wanda yasanar masa Galadima ya dawo, cikin hikima da girmamawa Galadima yayma mai martaba bayanin yafito yaga abin mamaki a k'ofar sashensa. Sosai mai martaba yayta juya kalmar abin mamakin, hakama matarsa, alk'yabba ta d'akko masa ya saka sannan suka fito a tare. Jakadiya na niyyar tafiya makwancinta taci karo da mota a k'ofar turakar mai martaba, mamaki ya kamata, zatayi magana saitaga Galadima dake tsaye a jikin motor, ta rusuna tana gaisheshi, kamar yanda yasaba ya d'aga mata hannu cikeda izzar mulki. Bata fita a mamakinba taga mai martaba da matarsa sun fito. Galadima baice komaiba sai bud'e murfin motar da yay yana nunama mai martaba ciki da hannu. Jikin baiwar mama Fulani mai kai mata rahoton motsin kowa na rawa ta nufi sashenta, hartayi shirin barci ma ta sallami Kuyanginta, amma dayake baiwar tanada fada sosai a wajen ta saita mata knocking k'ofa. Cikeda masifa da izza mama Fulani ta bud'e k'ofar, jikin baiwarnan na rawa ta zube k'asa tana fad'in “Ki gafarceni ranki ya dad'e, abinda nagano yafi k'arfin barinsa zuwa safiya, yalla6ai Galadima ya shigo fada shida sauran iyalan tsohon sarki, maimakon yawuce sashensa tamkar yanda ya saba saiya nufi turakar mai martaba kai tsaye, gashi can naga yana nuna masa Abu amota, ban tsaya ganiba na nufo gareki ya uwar gijiyata”. Ai mama Fulani bata tsaya bata amsaba ta figi alk'yabba ta saka tana fitowa, baiwarnan ta take mata baya. A can kuwa Mai martaba da mamaki ya kalli Galadima, amma sai Galadima ya girgiza masa kai yana sake nuna masa cikin motar. Matsawa mai martaba yayi sosai domin ganema idonsa abinda d'an d'an uwansa keson ya gani, Momma ta kunna fitilar dake motar dukda haske mai k'ayatarwa daya haske ko ina na masarautar. Koda mai martaba ya lek'a saiyay baya a zabure, cikin rawar baki da nuna motar yace, “Sameer yaushe kuma ka fara shirya min wasa da hankali har irin haka?”. “Ka gafarceni ranka ya dad'e, abinda kagani zahirin gaskiyane, wannan d'an uwankane ya dawo gareka cikin k'oshin lafiya da hukuntawar Ubangiji”. Galadima ya k'are maganar da rank'wafawa ya taimakama Abie ya fito, itama Momma ta fito. Hakan sai yayi dai-dai da isowar mama Fulani wajan. Da fuskar Momma mai d'auke da k'asaitaccen murmushi tafara tozali, ta k'araso gabanta da sassarfa tana rik'o hanunta da fad'in “Zeenah!”.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83