Chapter 33
Chapter 33
suka zaune, lauyan wad'anda ake k'ara shima ya mik'e, ya rissina tamkar yanda Baffi yayi, sannan yace, “ya mai girma mai shari'a sunana Barrister Adam Sadiq Adam, nine lauya mai kare wad'anda ake k'ara, tare dani akwai Barrister Aliyu Sa'adu yaro”. Barrister Aliyu ma ya mik'a gaisuwa ga alk'ali sannan suka zauna. Alk'ali yabama Baffi damar tashi domin yin magana. ALLAH Sarki dattijon kwarai kenan, masu wahalar samu cikin k'asa a halin yanzu, ya gyara hularsu ta lauyeyi dake Kansa, tare da farin eyeglasses d'insa dan rayuwa taja, ijiya duk sun raunana, ya kalli jama'ar cikin Court d'in sannan ya dawo da kallonsa ga alk'ali, yace, “yamai girma mai shari'a! Kamar yanda kowa yasani Muhammad Sameer Saifuddin Abubakar (Galadima) shine yake Neman son sanin miya saka wad'annan mutanen 11 yin gamayya wajen kama surukinsa harsu wahal dashi? Bayan kuma shikeda alak'a dasu bawai surukinsa ba?”. Kai Alk'ali ya jinjina, cikin sauke numfashi yace, “Lauyan wanda ake k'ara gareka”. Barrister Adam Sadiq Adam ya mik'e shima yana fitowa fili, yayinda Baffi Yakoma ma zauninsa ya zauna, Brr Adam Sadiq Adam yace, “yamai girma mai shari'a wace irin tambayace ke fitowa daga bakin lauyan mai k'ara? Ai sune yakamata ayima tambayar minene dalilin shi Galadima Na kama yaran wad'annan mutane 11 yayi Garkuwa dasu yau tsawon kwana biyu? harma da kisan wani a cikin su......... A hanzarce Baffi ya d'aga hannu sama yana mik'e da fad'in “yamai shari'a tambaya akaima lauyan mai k'ara, amsa kuma yakamata ya bamu baya sakko tashi tambayarba”. Hannu Alk'ali ya d'agama Brr Adam Sadiq Adam, yace, “Brr Adam ka gyara, amsa muke buk'ata, kanada dama kaima kayi taka tambayar daga baya”. Brr Adam Sadiq Adam ya risinar dakai alamun ban hak'uri sannan ya gyara tsayuwarsa yana fad'in “Yamai girma mai shari'a akwai abinda ke hannun Alhaji Auwal Fharuk Wanda mallakin su wad'annan mutane 11 ne, shine sukeda buk'atar kar6a”. Baffi yamik'e yana fad'in “yamai girma mai shari'a ko zamu iya sanin minene wannan Abu da suke tuhumar Alhaji Auwal Fharuk akansa, dahar suka kasa mik'ashi ga sharia domin kar6a har sai sunbi ta hanyar nuna k'arfin ikonsu?”. Brr Adam Sadiq Adam yay shiru yakasa cewa uffan, dan ganin tun a tashin farko yana shirin zurmawa. Ganin yak'i cewa komai Baffi ya kuma cewa “ya mai girma mai shari'a idan baza'a samu amsaba ina buk'atar d'aya daga cikin y'an wad'annan tawaga domin ya amsamin tambayata idan shi Barrister bai saniba”. Alk'ali ya jinjina kai yana bada Umarnin tasowar d'aya daga cikin su Alhaji Mansur. Dukfa abinnan dake faruwa Galadima yana kallon komai kai tsaye ta Computer, danshi baizo Court d'inba, babu damar hakan, yana fitowa a gidan police kamashi zasuyi, wannan yasa tukan zaman Shari'a Alk'ali yabada wannan damar ta had'a video call d'in da Galadima zai iya ganin komai da za'ayi kamar yanda IG ya buk'ata bisa umarnin shi Galadima d'in, kamar yanda ya shard'anta ko amasa hakan koya jeho gawar yaro d'aya ko yarinya. Hakan yasa sukai masa babu gardama. Alhaji Abdul-Naseer dake farkone ya taso, ya shiga inda aka tanada domin buk'atar hakan, ya fad'i sunansa da matsayinsa, sannan Alk'ali yabama Baffi damar masa tambayar. Baffi ya k'arasa jikin katakon d'aya shiga tsakaninsa da Alhaji Abdul-Naseer, idonsa a kansa yace, “Alhaji Abdul-Naseer, nasan kana d'aya daga cikin y'an wad'annan tawaga, shin kozaka iya amsa mana tambayar da lauyanku ya kasa?”. Murmushin Alhaji Abdul-Naseer yayi, cikin kwarin gwiwa yace, “Brr Usman, a ganina wannan sirrinmu ne, koma mi muke buk'ata a hannun Alhaji Auwal Fharuk mukeda alak'a dashi ai ba kowaba ko?”. Baffi yashiga jinjina kai yana murmushi, yayi taku d'aya biyu saikuma ya juyo ga Alhaji Abdul-Naseer, yace, “lallai wannan gaskiyane Alhaji Abdul saidai kuma dalilin sanin Court yanada alak'a da samo Alhaji Auwal Fharuk a hannunku, wanda ta silar kama y'ay'anku da surukinsa yayine kowa yasan hakan, saikuma gashi shi wannan bawan ALLAH Alhaji Auwal Fharuk a jiya daya farfad'o dukda baya cikin hayyacinsa, amma yana ambatar sunan Alhaji Halluru da jaddada lallai koda zaku kasheshi bazai bada wannan camera ba, domin shekarunma da kuka d'auka kuna ma rayuwarsa barazana bai bakuba balle kuma yanzu da lokacin Isar da ita ga Wanda akace ya Isar yayi, kenan Alhaji Auwal Fharuk k'arya yayi?”. Da sauri Brr Adam Sadiq Adam ya mik'e yana fad'in “ya mai shari'a wannan ai tamkar titsiyene Brr kema Wanda ake zargi, dan babu yanda za'ai la'akari da mutumin da baya cikin hankalinsa kamar yanda ya fad'a.....”. Shima Baffi azamar dakatar dashi yayi, yace, “yamai girma mai shari'a Barrister Adam bashida hurumin yanke hukunci akan yanayin Alhaji Auwal, sai ya bari bayanin likitoci ya tabatar mana hakan”. Alk'ali yay gyaran Murya da buk'atar ganin likitan dake kula da Alhaji Auwal Fharuk (Abba). Cikin mintuna 3 saiga doctor ya shigo. An sakashi d'ayan wajen, ya fad'i sunansa da aikinsa, sannan Alk'ali yace, “kaine likitan da ke duba lafiyar Alhaji Auwal Fharuk? ”. “eh nine yamai shari'a”. Alk'ali yace, “kozamu iya sanin wani Abu dangane da jikin Alhaji Auwal Fharuk? ”. “kwarai kuwa ya mai shari'a, an kawo mana Alhaji Auwal Fharuk cikin hali irinna suma, amma babu wani alamar duka ko harbi a jikinsa, saidai bincikenmu ya nuna an shak'a masa wani Abu. Daya saka numfashinsa Nisan zango, sai ajiyane bisa hukuncin ubangiji ya farfad'o, wad'annan kalamai sune abinda ya farka dasu a bakinsa, kuma kwakwalwarsa ras take, abinda aka shak'a masanne kawai bai sakesaba har yanzun, danma yanada jini mai k'arfine”. Cikin wad'anda suke zaune ma'aikatan Court d'in d'aya yaje ya kar6i wayar doctor da yay recording ya kaima alk'ali. Alk'ali ya kunna recording ya saurara, ya ajiye wayar gefe da sallamar doctor cikeda gamsuwar abinda yaji. Sannan shima yabada Umarnin sanin ita camera ta micece?. Baffi yakuma mik'ewa tsaye yana gyara k'atuwar rigarsa, yace, “ya mai shari'a, ita wannan Camera da wad'annan gamayyar mutane suke farautar rayuwar Alhaji Auwal Fharuk a kanta tanada alak'a da Muhammad Sameer Saifuddin Galadima ne, itace kuma musabbabin d'aukar yaran wad'annan mutane 11 dayayi yake tsare dasu a gida mai labba 67 dake anguwar tudun na ALLAH a tsakiyar binni, damin camera dai k'unshe take da abinda ya faru da tsohon Sarki dake jiyya a India, wato Mai martaba Saifuddin Abubakar tsawon shekaru 26 kenan ba'asan wad'anda suka aikata masa abinda ya kaisa da jiyyarba”. Turk'ashi, kallon kallo kenan, to lallai shine aka shigayi a wannan Court, nanfa k'ananun magana suka fara tashi tsakanin manya, Court ta harmutse da hayaniya babu maijin zancen wani, saida alk'ali ya tsawatar sannan akayi tsit. Inda kuma a gefe tsantsar rud'ani da rikita ta mamaye su Alhaji Balala, ko kad'an basuyi zaton shigowar wannan maganar da wuri ba cikin shari'ar, shima kansa lauyansu haka, tunda wawantar dasu Galadima yayi akan Shari'ar ta shafi d'aukar Alhaji Auwal Fharuk ne da farko. Alk'ali da shima kansa ya shiga wani yanayi ya buk'aci ganin Muhammad Sameer a Court. Baffi ya kuma mik'ewa yana fad'in “ya mai shari'a, ai Muhammad Sameer Saifuddin Galadima bashida ikon zuwa court a yanzu, domin kuwa yana can tsare da yaran wad'annan mutane 11 ne, kuma yana fitowa y'an sanda zasuyi ram da shine a matsayin mai laifi babbama kuwa, dan yanzu akwai laifin garkuwa da yara d'in a kansa, saidai munada hanya sassauk'a ta had'a wannan adalar kotu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83