Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 23

Chapter 23

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Ya d'an dara batare daya shiryaba. Yace, “one-one kenan?”. Munaya tayi dariya tana fad'in “nidai bada manufa na fad'aba”. “Fad'i gaskiya dai yalla6iya tsiwa”. “Gara mai tsiwa da miskili, koba komai akansan muna waje ai saboda tsiwarmu”. Galadima ya kuma Murmusawa. Yace, “ki kiyayi randa zan kamaki ALLAH”. Itama dariyar tayi. Tace, “yalla6ai ka fad'i wani Abu nabaka k'yauta mana”. Yay d'an jimm tunanin mikenan?, saikuma yayi ajiyar zuciya yace, “mikenan?”. Cikin wani salo Munaya tace, “R. Ita kawai nakeson ji a harshenka”. Lallai yarinyarnan taga gadon barcinsa wlhy, yay maganar a zuciya fuskarsa na k'awatuwa da murmushi. yace, “Okay, kibari sai ina gabanki”. “Tab, Indai ba yanzuba na fasa”. “uhmyim, miye na karayar hajiyar tsiwa?”. “Aiba karaya nayiba, lokacin kawai kabari ya wuce, ni karmafa yarannan suma su gadoka”. “Dai-dai kenan ai y'ammata, kokin manta k'yan d'a ya gaji ubansa”. “Humm Alfahari kenan, ita uwa an rainata”. Dariya tabashi, amma ya daure baiyiba. Yace, “keda kike gudunsu mizaisa su gadoki?”. Munaya ta d'an ta6e baki, cikin juya idanu tamkar tana gabansa tace, “yanzu kana ina?”. Murmusawa yayi saboda basar da maganar da tayi. Yace, “kinason ganinane?”. “A'a, son sani kawai nake”. “Humm, naje tad'i to”. Shiru munaya tayi, sai kuma ta d'an dara, “Yalla6ai kasan wani Abu kuwa?”. “Saikin fad'a”. Cikin danne dariya tace, “irinku kwantai kukeyifa, sai anyima y'ammata tallarku asamo mai taimakonku ta aura, kaima nasan saisu takawa sunmaka haka.....”. Sai yaji kitt, ta yanke wayar. Wani k'asaitaccen murmushi ya saki yana shafa kumatunsa, ya d'ora wayar saman cikin sa yana fad'in “lallai yarinyarnan kin girma, zaki tabbatar nayi kwantai kuwa”. Daga canma Munaya dariya taketa k'yalk'yatawa, harta tada Meenal, Mununiya datun d'azun take kallonta ta bayan labule bata saniba tayi murmushin jin dad'i itama tana share hawaye, tanason y'ar uwarta sosai, sannan wayonta da iya mu'amullarta na birgeta, tabbas Munaya tanada tsiwa, amma tanada wayo, inhar zaka takurata bazata ta6a raga makaba, amma tanada tausayi dason ganin farincikin wani koda ita zata rasa nata farincikine, gakuma son girma uwa gyambo, tanason komi zaka mata ka nuna muhimmancinta a gareka, a fili tace, “ALLAH yakawo farinciki mai d'orewa a ratuwarki kema y'ar uwata”. Amin munu😘☺. ★★★★★★★★ Tunda Muftahu ya shigo yakebin Galadima da kallon mamaki, ganin yasake yanata fara'a tamkar ba shine a matsananciyar damuwa yanzunba, ya zauna zuciyarsa na addu'ar samun mace tagari, dan lallai *MATAN KWARAI RABIN ADDINI ce*. Galadima ya hararesa yana tashi zaune, “malam lafiya ka k'uramin ido?”. Dariya Muftahu yayi sosai, yace, “to miye na tsarguwar ranka ya dad'e, wlhy kuna sha'aninku kaida gimbiyarka, yanzu nan harta saukeka daga hawa saman da kayi”. Filo Galadima ya jefama Muftahu, shikuma ya cafe yana dariya. Galadima ma murmushin yayi yana danna kiran Sauban. Dan yasan har yanzu yanacan cikin damuwa. Hasashen nasa kuwa yayi dai-dai, Dan har yanzu muryarsa a cinkushe take. Amma jin ta Galadima a sake sai farinciki ya kamashi, cike da zumud'i yace, “yaya an dace ne?”. Murmushi Galadima yayi mai sauti, yace, “muna fatan hakan autan Momma”. Alhmdllh Sauban yashiga jerowa, saiya saki jikinsa kuma harda tsokanar Galadima yana dariyar k'eta. Galadima dai murmushi yakeyi yana girgiza kai, ya yanke wayar zuciyarsa na addu'ar ALLAH ya saka farinciki a zuciyar Munaya fiye da yanda ta sakasu. Massage ya tura mata sannan ya kalli Muftahu yana gyara zama. Munaya na kwance har yanzu takasa fita, tunda tasamu Meenal ta koma barci saita lumshe ido tana dulmiya duniyar nazari, shigowar sak'one ya sata bud'e ido ta jawo wayar. Ganin Galadima ne saita mik'e zaune babu shiri, sak'on ta bud'e. _“Kin yaudareni da zance banko tambayi yaya jinin jikina sukeba yalla6iya, to ki shafamin kansu._ *_ALLAH ya sanya farinciki a rayuwarki fiye da yanda kika Sani_*. Wasu hawayen farinciki suka gangaro a kumatun Munaya, bata ta6a tunanin shirmen datake masa yanayin tasiri a zuciyarsa ba, Dan bai ta6a nuna mataba, a fili ta furta “ALLAH na gode maka dana zama sanadin saka wani bawa naka farinciki a lokacin jarabawar damuwa ta lullu6e jinsa da ganinsa da zuciyarsa”. Amin munaya, muma Ya ALLAH kabamu ikon bama bayinka muminai gudunmawar farinciki mai amfani koyaya ne, amma bata hanyar sa6onka ba ko take k'a'idar daka shinfid'a mana, amin👏🏻😭. ************************* Muftahu da Galadima suka fito, yauma bai zauna bayaba duk yanda Muftahu yaso hakan, dama yay masa maganar zama bayan hararsa yayi, dole yaja bakinsa yay shiru yana murmushi. Wani wajen cin abinci Muftahu ya tsaya, ya kalli Galadima dake kwance jikin seat ya lumshe ido yace, “ranka ya dad'e Dan ALLAH ina zuwa”. Kai Galadima ya jinjina masa kawai batareda ya bud'e idoba, Muftahu ya fita, mintuna 15 saigashi ya dawo hannunsa d'auke da ledoji, ya bud'e seat d'in baya ya ajiye, sannan yadawo mazaunin driver yana maba Galadima hak'urin jira. Baice dashi komaiba, Dan tuni yama lula wata duniyar. Gidan gonar Nuren suka nufa, inda su Harun suke a ajiye, a falo suka yada zango, ko ina k'al yake a tsaftace ga k'amshi, cikin masu kula da gidan gonar ya shigo d'auke da wankakkun y'ay'an itatuwa masu k'yau, zubewa yay yana kuma kwasar gaisuwa, Muftahu ne kawai ya amsa, Galadima hannu ya d'aga masa. Muftahu ya bud'e abinda ya siyo yana fad'in “Ranka ya dad'e mizakaci?”. Cikin d'an ta6e baki ya girgiza masa kai alamar bazaici komaiba. “Okay, to bara na kira Gimbiya meybe ita ta saka kaci”. Bud'e ido yayi yana zubama Muftahu harara, shikuma ya fuske tamkar bai ganiba. Saida Muftahu yasha fama kafin Galadima ya yarda yad'anci abinci, rabima duk fura da kayan itatuwan ne yasha. Sunkai 1hour da shigowa ya buk'aci ganin Harun da SD. Sun fara shiga d'akin da harun yake, bayan Muftahu ya saka key ya bud'e matsawa yay yabama Galadima hanya yafara shiga, takun takalmansa ya saka Harun dake zaune bakin gadon d'akin kansa a duk'e d'agowa, kallon ido cikin ido sukaima juna, Galadima ya janye nasa cike da basarwa yana wani miskilin murmushi mai k'ona zuciyar mak'iyi. Harun ma janye idanunsa yayi yanajan tsaki, Muftahu kuma ya ta6e baki yana gyarama Galadima kujerar zama. Galadima ya zauna idonsa akan harun, hannunsa ya mik'a ya kar6i lap-top d'insa dake wajen Muftahu, ya d'orata bisa cinya sannan ya janye idonsa ga harun dayak'i sake kallonsa, lap-top d'in yafara dannawa cikeda kwarewa, cikin seconds dabasufi 10 ba ya d'ora lap-top d'in saman stool d'in da Muftahu ya sake ajiyewa, sannan yay playing abinda ya kunna yana hard'e hannaye a k'irji da zubama Harun ido. Harun har yayi tamkar zai share sai dai ya kalla lap-top d'in, Wato shine a ranar sunan y'an uku gab da za'a sace yaran shida d'aya daga cikin kidnapers d'in. “Bibo inaso Ku tabbatar da kun kwashe yaran, karku kar6i wad'anda suke hannun k'annen matarsa, Dan na bogine, baby dolls ne aka sakama kaya irin na yaran domin kauda hankali, Sameer yanada wayo fiye da yanda kuke tsammani, Dan haka kuyi komai cikin kulawa da taka tsantsan, dai-dai lokacin da wutar hotel d'innan zata d'auke, zan kwashe yaran insha ALLAH, harsai nabar cikin hotel d'in ni da ku sannan za'a kunna, ina fata ka fahimta”. “Eh na fahimta ranka ya dad'e, namaka alk'awarin ko y'ay'an sarkine bana Galadima ba yau saisun kwana a alahira”. “No, banason su mutu yanzu, sai shi ubansu ya d'and'ana d'acin rashinsu,

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});