Chapter 28
Chapter 28
y'ar 17years ba, Dan itace autarsu suma. Hajiya yalwa ta dakama masu aikin tsawa tana tambayarsu ina su Rahma?. A rikice sukace suma dawowarta suke jira tun d'azun (Dan sunsan inhar ta iske sunyi barci zasu yabama aya zak'inta, maybe ma yazama sanadin barin aikinsu). Alhaji Abdul-Naseer yana k'ok'arin gwada kiran Rahma shima irin sak'on Alhaji Mansur ya shigo masa. Ai sai suka kuma rikicewa, Ashe sak'o dukya jema sauran abokansu, dan dannan suka Shiga kiran juna kowa yana tabbatarwa d'an uwansa Galadima ya d'auke masa d'a ko y'a. A wannan Daren suka sanarma police, gidajennan 11 babu Wanda ya rintsa barci, dukda yaran 8 ne a hannun Galadima, biyu basuda sauran yara a gabansu, duk sunyi aure, Galadima kuma yakafa musu nasu tarkon ne daban, biyu kuma a ciki bamasu ta6a haihuwa ba, biyar sun mutu yace bashida matsala da matacce, shi wannan saisunje babbar Court ALLAH zaimusu nasu hisabin. Sauran yaransu irinsu Alh halliru kuma yace nasu mai sauk'ine tunda manyansa suna hannunsa. Tun a wannan daren manyan police suka Shiga Neman ina Galadima yake, tunda kai tsaye yasaka sunansa a sak'on messages d'in daya turama iyayen yaran. Galadima yarigada ya tsara komai yanda ya dace, duk wata waya dazata fita a wayarsu saiya ganta yakumayi recoding d'in maganar, wannan yasa duk abinda suka fad'ama police yaji, murmushi kawai yaytayi, yayinda su Nuren sudai hankalinsu bai wani kwantaba, dukda sunji dad'in rikicewar da mak'iyar Galadima sukayi. Abinka ga manya, tun a labaran 12am Na daren ranar aka fara saka maganar, labari yafara shiga kunnuwan wad'anda basuyi barciba. Ciki kuwa harda y'an masarautar gagara badau. Hankalin mai martaba ya tashi, a Daren ya aika jakadiya data rako matarsa turakarsa kiran Galadima, danya kira wayarsa switch up. Lokacin da jakadiya taje sark'in k'ofa ya tabbatar mata Galadima ya fita tun farkon dare. Komawa jakadiya tayi ta sanarma mai martaba, aiko yakuma shiga tashin hankali, minene haka Sameer dayake kallo mai nutsuwa da hankali ya aikata?. Yana cikin wannan damuwa Waziri ya kirashi, ya tabbatarmasa Sameer ya turo masa sak'o shima Harun yana hannunsa. Zuface ta shiga jik'a mai martaba, yanzunan duk jajen da akeyi Na 6atan Harun d'an waziri dama Sameer yasani amma yay kunnen uwar shegu da kowa, hazbinallahu wa ni'imal wakil, shikam baya fata wannan mummunan labarin yaje kunnen 'Dan uwansa dake kwance cikin halin matsananciyar jiyya (kunsanfa har yanzu babu Wanda yasan samun sauk'i da Abie yakeyi, bayan ahalinsa dasu papi) a gagara badau babu Wanda yasani. Su Galadima duk suna ganin abinda ke faruwa a TV suma, amma ko'a kwalar rigarsa, damuwa d'aya kecin ransa halinda Abban Munaya ya tsinci kansa a ciki, amma sauran matsalolin dama dukya dad'e da shirya abinsa, komi zai biyo baya dama zuciyarsa ta shirya d'auka. Yau dai kam kusan a zaune suka kwana, abin tausayi saiga Galadima da kwannan kujera, aiko yasha wahala, Dan tashi yayi jikinsa Na matuk'ar masa ciwo, d'akin da aka saka masa kayansa yashiga, yasamu yay wanka sannan yayo alwala sukayi salla a jam'i, Dan har yaran duk kwancesu akayi, wad'anda kuma basayi suna zaune daga gefe. Galadima yace Ameer yaje da y'ammatan su had'a musu breakfast, cikin cika umarni yatasasu gaba suka fice, saidai kuma Farhat ce kawai ta iya girkin a cikinsu, gashi tanada Asthma, bakomai take iya sakewa wajen yiba, haka dai Ameer ya saka Nerh-nerh da Rahma suka taimaka mata da Abu mai sauk'i, dayake a tsorace suke, komai aka saka su yi sukeyi, sunga zuk'ek'iyar bindiga ahannun Ameer yo🤭😂. Koda aka kawo abincin dukda tashin k'amshi da yakeyi Galadima cayay bazai ciba, sudai su Muftahu kam ci sukayi, shikuwa yak'are dacin cake da tea, Wanda dama da kayayyakinsa yazo caf (Galadima fa da shirin zama yazo🤣 fans). Tun'a daren jiya gidan da su Galadima suke aka zagayeshi da y'an sanda, yasan kuma da hakan Dan CCTV Na nuna masa komai, amma saiyayi tamkar baima San da zuwansuba. Harun dai yak'i ci shima, hasalima sai yankama Galadima magana yake, wai inhar ya isa shid'in shegene ya kwanceshi mana, Ashe shid'in matsoracine ma, Dan ba'a sake d'aure kowaba bayan sunyi salla saishi Harun d'in daya nemi yin gardamar k'in nutsuwa waje d'aya. Ko inda yake Galadima bai kallaba. Nuren yay gyaran murya, duk suka maida attentions d'insu garesa. Yace, “inhar kun shirya bamu had'inkai kowa zai fita a gidannan lafiya babu ko kwarzane a jikinsa, Dan bamuda matsala daku, da iyayenku mukeyi, Wanda yaza6i kuma tafiya barzahu babu shiri saiya nuna jarumtarsa ko rashin kunya, wannan wawanma ya isheku izna”. Yay maganar yana nuna Harun daketa bige-bige yana kumfar baki masifa. Duk suka amsa da zasu bada had'inkai. Yau dai Darma kam shima yashiga hankalinsa, Dan yaga lamarin yafi k'arfinsa. Galadima ya d'auki k'aramar wata waya dake kusa dashi yafara dannawa yana shan tea d'insa hankali kwance, yayinda k'afarsa ke hard'e d'aya kan d'aya. Munaya ya kira, wadda itama batayi isashen barciba, gashi suna a yanayin rashin tsarki balle ta duk'ufa gayama ubangiji itama, amma dukda hakan bata fasaba, zuwa dare kuma kowa ya ankara da rashin dawowar Abba akwai matsala, dan around 7:30pm Baba k'arami ya dawo gida, babu dad'ewa kuma saiga Dady shima, dawowarsu yasaka kowa Sanin mi ake ciki, innaro ce kawai aka hana kowa ya sanar mata. Babu Wanda yay barcin kwanciyar hankali a gidan su Munaya, saidai yaran k'anana dabasu San dawan garinba, irinsu Inna ma ai akan sallaya suka kwana suna gayama ALLAH kukansu😭. Basuda wuta a daren jiya, shiyyasa basuga abinda yake faruwaba, rashin kwanciyar hankali ya hana a kunna musu gen..., Gasu Abdurraheem kwana sukayi kuka.🤦🏻♀ Cikin sanyin jiki Munaya ta d'aga kiran, muryarta ta dushe saboda kuka, ahaka ta gaisheshi. Ya amsa a sanyaye shima yana tambayar yaranshi, tace, barci sukeyi. Cikin lumshe ido yace, “karki damu daduk abinda zaki gani, sannan karki kirani, dan duk kiran dazakiyi nasan baizama lallai nikad'aine zan jishiba, zan dinga kiranki dakaina insha ALLAH. Please take care of yourself”. Kitt ya yanke wayar batare da yajira cewarta ba. Kanta ta cusa cikin k'afafu ta fashe da kuka, yayinda Munubiya ma ke gefenta tana nata da shayar da Ameen daya tashi barci. Galadima kuwa yana yanke wayar ya mik'e cikin takun izza da k'asaita ya k'arasa gaban Harun da bakinsa yakasa yin shiru. Izzarsa da k'asaitarsa Na burge matasan samarin nan, hakan yasa duk suka bishi da idanu har y'ammatan, ga fuska a cakud'e babu alamar yasan minenema dariya. Gaban Harun ya tsaya hannayensa duka a cikin aljihun wandonsa, babu Wanda yakula da lokacinda Galadima yaciro hannunsa d'aya a aljihu, saidai k'arar mazgar Harun dayayi abaki sukaji kawai, kafin Harun ya farfad'o Galadima yakuma k'ara masa ta d'ayan gefen. Sannan ya d'an risuno yanama bakinsa alamar zip da yatsunsa biyu🤐, Harun yamasa shiru kenan🤣. Kutt, gaskiyafa Harun ya mazgu babu k'arya🤭🤣. Amma d'an bala'in naku bakinsa bai mutuba, bayan ya farfad'o daga azabar dukan saiya cigaba da magana cikin haki da huci. Sharesa Galadima yayi yakoma ya zauna dan fuskantar abinda ke a gabansa, a fusace ya d'auki k'aramar bindigar daya fiddo yanzu yafara Harbin inda Harun yake, ta saitin k'afafunsa. Rikicewa kowa yayi, Harun yashiga mutsu-mutsu da k'afafu yanasan d'agewa Dan kar Harbin ya sameshi. K'aramin d'an iska Ashe kanajin tsoron mutuwa🤣?. Wannan harbi ya kid'ima police d'in
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83