Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

babu tambaya nasan Munaya ce wannan, fetsararriya anzo a d'ora daga inda aka tsaya kenan?”. Murmushi nayi, Na kar6i Abdurraheem da Munubiya ta d'oramin a cinya, saida Na fara shayar dashi sannan Na kalli innaro, nace, “Innaro inhar kin shirya d'orawa daga inda kika tsaya muje zuwa mana, indai bazaki canjaba Munaya ma har abada zabata canjaba, miye laifin Innarmu danta d'akkoshi yana kuka?, rawa kika tarar tana masa ko wata tsiya? Yo nagama kema haka kikaita ma mutane kuka saikinje jiyyar abbanmu India, halan kema kunyar d'an farince.......”. Bankai k'arshen zancenba innaro ta d'ora hannu bisa ka ta aza mana kuka. Ni da Munubiya muka kuwa kwashe da dariya abinmu, a haka abbanmu ya shigo ya samemu, Innarmu tanata bama innaro hak'uri tak'i saurarenta. Girgiza kai kawai Abba yayi, Dan akan idonsa komi ya faru, hannu ya d'agama Innarmu alamar ta barta, zata fara magana ya girgiza mata kai. Shiru tayi takoma gefe, innaro saita k'ara k'arfin kukanta wanda harya fara jawo hankalin matan gidanmu, saidai babu damar zuwa kallon kwaf tunda a d'akine. Hannun innaro Abba ya kama ya zaunar da ita, cikin kwantar da harshe yace, “haba dai inna, yanzu dan ALLAH abinda akayi yarannan Na k'anana yanzuma shi za'a sake azaman dazasuyi Na wata 1 kacal dawasu kwanaki? Haba inna, minene Dan yaro yayi kuka Ai'sha ta d'akkoshi? Inna ina dad'i irin wad'annan abubuwan haka?”. Share hawaye innaro tayi, tace, “to naji Auwalu, indai nice bazan sake magana akan y'ay'anka da matarka ba....”. “da yafi”. Nafad'a ina murgud'a baki. Hararata Abba da Innarmu sukayi, Abba ya rik'e hannun innaro da sauri saboda k'ok'arin tashi da takeyi, “kiyi hak'uri Dan ALLAH inna, niba haka nake nufiba, da ni da abinda Na mallaka ai duk mallakinkine, nafad'a ne dan kawai a zauna lafiya yarannan sugama wanka kowa takoma gidan mijinta cikin salama, tunda kinga dai da yaran d'akinnan ne kawai irin wannan sa6anin ke shiga, yanzufa kika fito d'akin can kina tsokanar yarinyar Haleematu, mizaisa anan kuma hakan bazata kasanceba?”. “shikenan naji”. Abinda innaro tace kenan kawai ta mik'e ta fice. Abba ya bita da kallon kawai cike da takaici. Gaidashi mukayi, ya amsa yana had'iye 6acin ransa, ya tambayemu ya yara?, duk shiru mukayi muka kasa amsashi saboda kunya. Murmushi yayi, ya kar6i Abdurraheem daya gama shan nono, bayan Innarmu yabi d'akinta d'auke da yaron, dan tunda yamata magana tabar falon ta shige d'akinta. Zaune ya isketa a bakin gado tayi tagumi tana hawaye. Ya zauna kusada ita rungume da Abdurraheem, shiru yay yana kallonta, kusan mintuna biyu ya kwantar da yaron a bayansu yamatsa jikinta sosai yana kwantota jikinsa, “kiyi hak'uri Ai'sha, a halin inna babu wanda baki saniba yanzu, tunkan kizama mata a gareni kinsan wannan, to mizaisa hakan yasakaki kuka a yanzu? wani abin nata harda tsufa yanzu, amma kiyi hak'uri dan ALLAH”. “Ni ba kuka nakeyi saboda abinda inna takeminba, ina kukane saboda rashin jituwar da kullum take k'ara tasiri tsakaninta da yarannan, duk yanda naso hana girmamar irin wad'annan abubuwa n abun ya gagara, bai kamata ace laifina yana shafar jikokinta ba, jinintane fa su, idan ni tace banda asali sukuma ai itace asalinsu ko? wlhy Abbansu banason wad'annan abubuwan, wani lokacin zuciyata takan gaza d'auka”. “kiyi hak'uri, insha ALLAH komai mai wucewane, yakamata kuma zuwa yanzu kufad'a mana Ku su wanene? Kodan yaranki, dangin mahaifiya sunada matuk'ar tasiri a rayuwar yaro, banason zuwa nan gaba su zargi abinda ba haka yakeba, kodan gudun suma y'ay'ansu su taso suyi musu irin wannan tambayar”. Murmushin takaici inna tayi, ta d'ago daga jikinsa tana share hawayenta, suduka kallon Abdurraheem daketa motse-motse da k'afafu yana dungurin bayansu sukayi, Abba yay murmushi yana shafa kansa, sannan ya kalli inna yana fad'in “Ai'sha kodan wad'annan yaran, dolene watan watarana sai tarihinsu ya shafi tsokaci dangane da usilin mahaifiya, dukda nawa za'a kawo saifa naki ya taka rawar gani shima”. Inna tayi murmushi itama tana shafar kumatun Abdurraheem d'in, ta mik'e tsaye tana cewa “karka damu, a bani lokaci, da izinin ALLAH saisun taka tushena da k'afafunsu”. Abba ya d'auki Abdurraheem ya rungume yana fad'in “ALLAH ya tabbatar”. Mukan bamusan wainar da ake toyawaba, muna falo yara suna Neman haukatamu da kukansu, dukfa barci suke, amma Meena Na tashi kamar jira suma duk suka tashi masu kawunan kwakwar.😏 Haushi ya isheni nakusa make Amaturrahman datafi kowa daddagewa, saida Munubiya ta rik'e hannuna, “Sweetheart wai baki da hankaline? Uwarmi zaki daka ananne?”. Cikin tura baki nace, “yo Sweetheart haukatamu zasuyine?”. Daga inna har Abba dake fitowa baki suka gumtse suna dariya, “A lallai akwai aiki babba a gaban mata ashe?”. Inna tafad'a tana kallon Abba. Murmushi yayi shima yace, “babba kuwa Ai'sha”. Sai sukayi dariya. Hakanne yasakamu farga dasu, muka juyo muna kallonsu kowa fuska a tur6une, saboda haushin da yaran suka bamu. %%%%%%%%%%%%%%%% Bayan kammala gyara da Sauban yayi, Galadima ya mik'e zuwa cikin d'akin, zama yay ya kunna dukkan Computers d'in d'akin, saida komai ya dai-daita sannan yafara aikinsa cike da kwarewa, har lokacin sallar la'asar yana a d'akin, shiko gajiyar zaman jirginma bata damesa ba, bedroom d'insa ya dawo yay salla sannan ya sauka k'asa, Samha yabama Umarnin abinda yake buk'ata ya dawo yacigaba da aikinsa. Mintuna kad'an sai gata takawo masa. takan shiga shauk'i idan taga Uncle Sam yana sarrafa Computers d'innan, saitaji tamkar yafi kowa ilimin sarrafa Computer a duniya, amma tasan dole sai ansamu wanda suka fishi, badan karya maketa ba data tsaya taita kallonsa kawai. Shi baimasan tanayiba, hankalinsa nakan aikinsa gaba d'aya, dukda kansa daya fara ciwo kad'an-kad'an burinsa yakai inda yake hari. Saida duhun magriba ya gabato sannan yasamu kansa, yanzu ma a d'akin yay sallar magrib, ya zauna karatun Qur'an har time d'in isha'i yayi. Yana idarwa ya d'ora da shafa'i da wutiri, saboda barcin dake damunsa, soyake ya kwanta da wuri, duk abinda yakeyi kafin barci saida yay k'ok'arin kammalashi da k'yar sannan ya kwanta, dukda tunani da kewar yaransa Na neman 6atar da barcin nashi haka yayta yak'i da shi har barcin yaci Galadima akan tunanin. Samha tazo kawo masa dinner ta iske yanata barci cikin bargo, yama kashe hasken d'akin saina fitilar gefen gadon kawai itakuma haske kad'anne. Ajiye abincin tayi, dukda mawuyacine ya tashi domin cinsa, musamman da saida yamma yamaci d'azun.. (((+)))★(((+)))★(((+))) Yau kwananmu biyu kenan da dawowa gida, nayi waya dasu Samha duka amma banda uban gayya Galadima, bai nemini ba nima ban nemeshiba, Momma kam kullum sau biyu take kira muyi video call itada Abie, safe da yamma duk takan kirani. Muna kwance a gado ni da Munubiya, sai kuma mak'e murya takeyi suna waya itada yaa Marwan, koni dake kusa da ita ba komai nakejiba, nayi murmushin takaici ina juya kwanciyata zuwa d'ayan 6arin, danma Na daina jinta gaba d'aya, wata kwalla ta tararmin a ido, ba bak'in cikin kasancewar y'ar uwata a farin cikin nakeba, a', tausayin kainane ya kamani, maybe ita kad'aice zata koma gidan nata mijin banda ni, Na kalli yaranmu da laraba keta musu shirin barci, Aiyaan da Aryaan nata jagwalgwalasu, saurin d'auke k'ananun kwallar dake Neman zubomin nayi. Ni dai har barci ya d'aukeni bansan lokacin da Munubiya tagama wayarnanba, ban farkaba saida yaran suka farka da kuka, yanzu sabon iskancin da suka tsiro dashi kenan

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});