Chapter 39
Chapter 39
d'in ne, d'aya kuma wadda mutumin farko d'an uwan baba Rabilu daya bada camera d'in ne ya rubuta ce. Ita kad'ai alk'ali yabada umarnin karantawa, yayinda masana keta k'ok'arin saita camera da TV dake kotu suma, Wanda Galadima ne ke k'ara sanar musu dukkan dabarun daya kamata suyi daga inda yake tsaye. Abinda takarda ta k'unsa shine..... *_Assalamu alaikum_* _Sunana Habu, wannan takarda ina fatan ta iso agareku, ko yarima, ko gimbiya ko matar Sarki mahaifiyar su yarima, Ku duba wannan camera d'in, duk yanda aka k'ulla faruwar ciwon mai martaba da wad'anda suka kulla suna a ciki, nidai nasan tawa ta k'are, dan tunda suka ganni ina d'oukar sirrinsu saisun kasheni, wata uku kenan ina 6oye-6oye, yaudai Na yanke shawarar fito fili Na baku koda hakan yana nufin zan mutu, dama can kwanana sun k'arene, koma basu nayi saisun kasheni, ballema bazan ta6a basu d'inba, ALLAH yabama mai martaba lafiya da tsawon kwana mai amfani, yakuma baku ikon hukunta wad'annan tsinannun masu jinin Fir'auna a jiki, wad'anda mulkine da tara duniya kawai a gabansu ba al'ummar k'asarsuba, duk yanda zakuyi karkubar la'anannnun nan yin mulkin al'umma, subasu cancanci zama shuwagabanniba._ *_Bisalam_*. Kotufa tayi tsitt, ko tarin wani bakaji sai k'arar fanka, yayinda zufa tagama jik'e su Alhaji balala sharkaf, kallo d'aya zakai musu ka fahimci ruwafa ya k'arema d'an kada. Alk'ali baice komaiba, jira kawai yake camera ta daidaita ajikin TV kowa yagani, matsalar camera Ce irin ta da, shiyyasa take bada wahala, da k'yar dai cikin amincin ALLAH ta kawo, tofa, saidai kalar da take nunawa White and black, ga wani rawa-rawa da takeyi saboda ba nutse aka d'aukaba, kuma da alama ana yayyafine. Dagani wajen wani ke6antaccen wajene daba kowa ya isa shigaba, shikansa d'an jarida habu kota Yaya yayi hakan? ALLAH kad'ai ya Sani saishi, gashi bashida rai balle mu Sani. Mutanene da ak'alla sunkai 20 a wajen. Alhaji balala, Alhaji Mansur, Alhaji Lawan tanferu, Alhaji Bana, Alhaji Abdul-Naseer, Alhaji Labaran khacia, Timothy, Hajia A'i, Victoria, Miracle, Alhaji Sageer, William, Josaya bamma, Kabiru Ibarheem, Alhaji Mamman, Waziri, Sai wani Sarki daba wani k'arfin ikone dashiba, yama rasu tuni, tun ciwon Abie babu dad'ewa, sai Mahaifin Gimbiya Zulfah uwargidan Sarki, shima sarkine mai fad'a aji, Sai mahaifin Mama Fulani😱, sauran Biyun turawane. Duk suna zaune kowanne da kwalbar coca-cola a gabansa (sannan shinsa sai manya🤣). Alhaji Lawan tanderune ya mik'e yafara jawabi kamar haka. _Masu girma saraki dake wannan waje, da bak'inmu (turawa) sai abokaina shak'ik'ai ina muku sallama gaba d'aya_ Duk suka amsa a tare. yaci gaba da fad'in, _Muduka nan mun tarune akan mak'iyinmu guda d'aya, Wanda ya tare mana gabas ya tare mana yamma, hakama kudu da arewa, mun bishi ta lallami akan yabamu goyon bayan cikar burinmu amma yak'i, yana wulak'antamu saboda yaga ALLAH yabashi k'arfin iko da izzar mulki a hannu, a daren jiya mun yanke shawarar kasheshine kowa ya huta, amma yanzu mun fasa hakan, zamuyi masa abinda saiya gwammaci yazama gawa, dan zai rayune shiba mutumba Shiba butun butumiba, ahaka naman jikinsa zai ringa ru6ewa sashe-sashe, mukuma zuwa sannan mulkinnan dai dayake ganin bazai dafa mana muyiba ya dawo hannunmu, dan mungaji da mulkin soja hakannan, gashin kanmu muke buk'atar ci koya kukace?”_ Hannu suka d'aga suna fad'in eh hakane hakane. Alhaji Lawan tanderu yayi dariya yana gyara babbar rigarsa, ya d'akko wani ruwa a kwalba yana nuna musu, _“kunga wannan itace gubar ruwan allurar da za'ai masa, ita cikin mintuna biyu zuwa biyar take fara tasiri koba haka kaceba Mike?”._ Cikin turawa biyu dake tare dasu d'aya ya gyad'a kai yana murmushin mugunta. Gaba d'aya suka sanya tafi, raf! Raf! Raf!, saikuma suka koma tafawa da musabaha a junansu (irin sun samu cikar burinsu d'innan). Tanderu yacigaba da magana bakinsa a washe. _“Wannan aiki ba kowane zai mana shiba sai wazirinsa, Munaso da asubahin yau kamasa wannan allura dakagani, inamai tabbatar maka inhar ya Idar da sallar to bazai shiga gida da kansaba”_. Waziri mahaifin Harun ya kar6a yana washe baki tamkar gonar auduga, da fad'in “lallai nafi kowa farin ciki da samun wannan dama, domin kobabu komai zanyi maganin mak'iyina da kaina, daga yanzu sainaga da bakin dazai kuma cin zarafina da jifana da kalaman banida hali, toshi mai halin saiya cigaba da shukashi muda bamu dashi muyita girba munakaiwa gidanmu munaci....”. Gaba d'aya suka kwashe da dariya suna tafawa, a Na wannan dariyane Alhaji Bana idonsa yakai ga camera, alamun yaga habu kenan, ajiye k'aramin kofin silver dake hannunsa ya zuba coc yayi yana mik'ewa zumbur. Sauran suka fara tambayarsa mike faruwa?, tuni habu daya farga dasu ya shek'a da gudu. Daga nan ba'a sake nuno kowaba, sai gudu da habu yakeyi da hakkinsa, Camera d'in Na wani shuw-shuw harma aka bar ganin komai. Kwakwkwaran Motsi kowa ya kasayi acikin Court d'in, Galadima ya duk'ar dakai yana kallon k'asa hawaye Na zirara suna d'iga, hakama Abba Hayatuddin kuka yake saboda tausayin d'an uwansa da takaicin waziri daya kasa zama kusa dashi yanzun, ga takaicin wai harda kakansu Wanda ya haifi mahaifiyarsu, shin shikuma miye matsalarsa da d'an uwansa ne? Kenanma mama Fulani mahaifiyarsu itama tasan komai? Innalillahi wa inna'ilaihiraji'un, wannan wace iriyar masifacene hakan?. Alk'ali daya buga gudumarsa a sanyaye ya katse tunanin mutane da yawa dake cikin kotun, cikin sauke nannauyan numfashi yace, “yanzu babu tanderu a duniya, shin ko akwai mai wakiltar wannan group a yanzu?”. Su Alhaji balala da duk jikinsu yay lak'war kunya da nadama duk sun lullu6esu sukayi tsitt. A fusace cikin daka tsawa Alk'ali yace, “waishin! Ba'a jini bane?!!”. Jiki Na rawa Josaya bamma ya mik'e, tsufa sosai ya kamashi, danma akwai jin dad'i tattare dashi, ko a wancan lokacin dagani ya girmi tanderun ma gaba d'aya. Wani cikin ma'aikatan kotun yaje inda alk'ali yake suna magana k'us-k'us, komi yake fad'a masa oho, nagadai alk'ali yayi alamar a kawosu, wancan ya sakko, shikuma alk'ali ya maida hankalinsa ga Josaya bamma dake k'ok'arin shiga inda ake buk'atar ganinsa. Josaya Yaje inda ake tsayawa ya tsaya, Alk'ali ya kallesa cike da tsantsar tsana yace, “kotu tanason jin shin minene kuka nema ga adalin Sarki mai gaskiya da son ayi gaskiya irin Sarki Saifudden yak'i baku goyon baya har kuka nakasashi?”. Josaya bamma ya gyara tsayuwa kansa a duk'e saboda kunya. Yace, “Ya mai Shari'a, mu mun kasance y'an k'ungiya d'aya masu burin kafa gwamnatin farar hula a wacan lokacin, mafi yawa acikinmu tare mukayi karatu a landan, tunkuma munacan wannan shine babban burinmu, dan haka koda muka dawo najeriya muna kan wannan buri, duk da mulkin soja shike gudana a k'asar tamu, kuma babu wani mahaluki daya Isa yin koda kwakwkwaran tarine, da farko mun fara janyo wasu mutane da yawa suka shigo jikinmu, sannan muka farabin sarakunan gargajiya Na kudanci da arewaci dan samun had'inkai, wasu sun amince mana, wasu kuma sun nuna babu ruwansu, Sarki Saifudden yana sahun farko Na manya-manyan sarakunan gargajiya da akeji dasu da girmama maganarsu a arewaci, munada yak'inin inhar ya bamu goyon baya mun gama samun abinda mukeso, wannan yasa muka fara binsa ta k'ark'ashin k'asa, wato su Mike sukaje ga wazirinsa suka gana da samun manya-manyan sirrika a wajensa, sunje da kwanaki biyu muma sai muka tunkari Sarki Saifudden bisa jagirancin Waziri. Cikin lalama da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83