Chapter 64
Chapter 64
falon, saiya samu kansa dak'in yarda su had'a ido. Aunty Mimi Ce kawai tayi k'aramar dariya, amma Momma yitai tamkarma batasan inda ya dosaba, saima ta shiga yaba kwalliyarsa da tambayarsa sai ina kuma?. Ganin Momma ta share shima saiya fuske yay mata tamkar yanda ya saba, yasamu ya fice abinsa. *************** Ni dai kam nakasa sauka kasa, ganin kad'aici da kewar Galadima zata fara addabata saina d'auki waya na kira innarmu, hayaniyar danaji a gidan yasani tambayar mike faruwa?. Innarmu tace, “To sarkin son gulma basai kinjiba, ya kuke?”. Dariya nayi, nace, “Kai innarmu Dan ALLAH kid'an gumtsamin”. “O ni Ai'sha ALLAH ya shiryeki Munaya, wato dai bazaki canjaba kekam?”. Nanma dariyar nayi harda k'yalk'yatawa, “Kai Innarmu na canja mana, kinsan gidan namune sai a slow, nasan dai yanzu duk kin wuce da iskancinsu d'innan?”. Itama dariya tayi daga can. Tace, “Ai tsakanina da kowa yanzu sai girmamawa, ni dariyama suke bani, Safara'u ce wai mijinta zai k'ara aure, shinefa inaga ta tada hankalinta taita zuba masa rashin kunya ya shashshek'a mata mari, to jiya dai a gida ta kwana, kinsansu da gutsiri tsomar tsiya, wai Jamila tashiga gaida Hadiza ta iske suna gulma itada Mero, shine taje tasanarma uwar tasu, wannan yakawo wanan fad'an da kikeji, Maman safara'u babu hak'uri tafito tanata zaginsu da fad'in ai ko auren Safara'u mutuwa yayi ba kanta farauba, tunda ga Siyama da Zarah nan a gida tun kafin ita. Shinefa suka kaure fad'a da cin zarafin juna”. “Tofa, ALLAH ya k'yauta to, tosu su mom indai banda take laifinka ka hango na wani ai baikamata su zauna yida waniba ganasu y'ay'an zaune, anriga an koyama yaran gidanan d'aukar gulma wlhy, yanzu kamar jamila tasan ta d'auki zance takaima mamansu, to su Abba duk basa nan innarmu?”. “Wlhy suna nan, kuma duk sunajinsu, shiyyasama danaje nabad'a hak'uri sau d'aya naga sunk'i saurarena nai dawowata d'aki, Aryaan na kwance yana fama da zazza6i gara Nazo natattali yarona yafimin”. “hhh innarmu kinaji da autaras d'innan nakifa, ALLAH yabashi lafiya, sukuma ALLAH ya dai-daita komai. Hajiya Innaro fa?”. “Tana gidanta mana, bama tajin dad'i kwana biyunnan wlhy, tana fama da ciwon k'afa, ki kirata ki gaisheta, dan jiya gwaggonku Safiyya ma tazo itama”. “To su Innaro kodai gangarawa za'ayine? ALLAH yabata lafiya”. “Ja'ira saidai tsohonki ya gangara, amindai to, ai dama sauk'i”. Dariya nayi kawai. Daganan muka cigaba da hirarmu wadda ta shafemu, nan ma innarmu ke sanarmin Aunty Salamah tazo gidan ansaka aurenta. Cikin tsantsar farin ciki nace, “Innarmu dan ALLAH da gaske?”. “To Munaya ana wasa da maganar aurene? Nasanma zata kiraki ai”. Farin cikine sosai ya mamaye zuciyata, nace, “ALLAH sarki Aunty Salamah komai nada lokaci, anata surutun ta tsufa agida batayi aureba, gashi ALLAH yakawo iyakar, lallai aure da Haihuwa duk lokacine dasu, duk saurin mutum saiya jira ALLAH, ALLAH yabama sauran y'an matanmu mazajen aure nagari masu addini da nagarta, suma mazan haka”. “Amin dai Munaya”. Inna ta amsa itama cikin farin ciki.. Nace, “Innarmu zancen Ayusher fa itama?”. “Itama kwanannan sukace min zasuzo akan maganar, dan kawu Mani ma munyi waya dashi d'azunnan, tsohuwar nan ce tarasu mai ciwon hannun nan, shinema ya dakatar dasu”. “ALLAH sarki Innarmu, badai wadda tabama yara maganin ciwon kai ba?”. “Aiko dai ita, ashe kin ganeta, ALLAH ya d'auke kayansa shekaran jiya wlhy, Abbanku ma zasuje gaisuwa su dukansu harda Baba mai kanwa ”. “Wayyo, to ALLAH ya gafarta mata, amma shi baba mai kanwa ina yaga k'arfin wannan doguwar tafiyar innarmu?”. “Ai ba'anan takeba Munaya, dayake ALLAH yabashi lafiya, yace insha ALLAH saiyaje yaga tushena”. “ALLAH Sarki baba mai kanwa, ALLAH yak'ara lafiya da tsawon kwana”. Inna ta amsa da amin. Munsha hira sannan mukai sallama. Itama Innaro na kirata namata ya jiki, daganan muka gaisa da gwaggo Safiyya da aunty Habiba. Na kuma kira Munubiya, sosai mukasha hira, take kuma bani labarin auren Aunty Salamah dayazo kamar ha6o. Tace, “Alhajinan dai dayayta naci wanda muke cema Cingom Alhaji dai shine mijin”. “Oni rayuwa, Sweetheart kinga hikimar Ubangiji ko, idan yazo muyita masa iskanci har ita aunty salamah d'in Ashe dai shine mijin, gaskiya ya cancanci ta auresa, wajen shekaru biyarfa bawan ALLAH nan baita6a gajiyawaba”. “Wlhy kuwa Sweetheart, son gaskiya kenan ai, ga Ayusher nan anata soyewa itada Hamma Youseeff, duk wannan shan k'amshin nasa ya mace mata, Yaa Fadeel ma in fad'a miki shida Badeerah Ashe sun k'ulle”. “Dan ALLAH da gaske ko wasa?”. Cikin Dariya Munu tace, “Wlhy kuwa, waike bak'ya waya da kowama kenan?”. “Wlhy ba haka bane kemakinsan d'an tsakaninan damuwar data hanani sukuni, amma yau dolene na kirasu nasha kanu, shegiya Ayusher bara itama na kirata, dukda kud'ina sun kusa k'arewa, a gaidamin da Sweetness babies d'ina da Yaa Marwan inya dawo”. “Zasuji insh ALLAH, asha amarci lafiya, aidai kulamin da yara kar soyayya tasa abarminsu su rame”. Kafim nayi magana ta yanke kiran. Dariya kawai nayi ina girgiza kai, alokacinne Samha ta shigo. “Ah lallai aunty gimbiya yau Uncle Sam ya 6oye mana ke, Momma Ce tace yau bazaki sakko bane?”. “Dan ALLAH da gaske?”. Nai maganar cikin waro idanu. Dariya ta sanya, “Wlhy kuwa da gaske nake”. “Ni munaya naga idi, ALLAH kunya nakeji”. “Kam kunyafa aunty gimbiya, to miye najin kunyar? Wlhy ALLAH yabani miji irin Uncle Sam a gabanki zan mak'alk'ale abina”. Duka nakai mata ta kauce tana dariya. ************** Cikeda jin kunyar su Momma na sakko k'asan, amma saisukayi tamkar basusan minike mawaba, tun ina sunne-sunnen kai hardai na warware nasaki jikina kamar yanda nasaba. Momma da Aunty Mimi sunji dad'in haka, a zukatansu suna mana addu'ar d'orewar zaman lafiya nahar Abadan.................✍🏻 _Inaga sai Monday zakujini, kuyi fatan nama kammala gaba d'aya😅🤝🏻👌_ *_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻 [8/22, 8:36 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* *_💡HASKE WRITERS ASSO...._* *_♦RAINA KAMA...!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_BOOK 3_* 👉🏻2⃣9⃣ .................Gaba d'aya sun kasa yin breakfast, suna cikin zaman jigum-jigum suka jiyo bud'e gate da shigowar mota. Samha ta fita da hanzarinta danson ganin wanene, fitowar tata tayi dai-dai da fitowar Galadima daga cikin mota fuskarsa d'auke da wani irin k'ayataccen murmushi daya fidda sirrin k'yawunsa. Da gudu ta taho garesa, yakan mata fad'a akan son rungumarsa ko Sauban amma yau saigashi ya bud'e mata hannu dakansa tazo ta shige jikinsa. Ihun murnartace tasaka su Momma fitowa da hanzari suma Ganin Galadima ai sai duk sukayo kansa itada aunty Mimi, itadai munaya gefe ta tsaya tana sharar hawayen farin ciki. Abie dake kallonsu daga cikin mota ya saki murmushi yana share hawaye, yana k'asa d'aya da iyalansa amma bai ta6a sanin muhallinsu ba sai yau, dukda bai shigaba gidan yamasa k'yau. Galadima ya ture Samha daga jikinsa ya rungume Momma da aunty Mimi yana sakin wani irin kuka daya matuk'ar tada hankalinsu. Da sauri suka d'agosa hankali tashe suna tambayarsa mike faruwa? Kodai ALLAH yayima Abie rasuwane?. Cikin kuka da dariya yace kowa ya rufe idonsa . Babu musu sukabi Umarninsa, har Munaya dake gefe. Yace, “kun tabbatar kowa ya rufe?”. A tare suka amsa masa da eh. Ya murmusa da goge sauran hawayensa sannan ya juya ga motar ya bud'e, hannun Abie ya kama da taimakonsa ya fito rik'eda sandarsa mai k'yau dazata dinga taimaka masa wajen tafiya, Dan har yanzu tafiyar batai kwariba. Saida Abie
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83