Chapter 54
Chapter 54
kansa tsaye ya kaimu wani had'ad'd'en wajen cin abinci, saima kayi gaddamar ba'a Niger d'in yakeba, duk fitowa mukayi, amma Galadima yak'i fita, saida su Abba suka shige sannan, Ayusher da feena sukazo kar6ar yaran, Dan can Yaa Fadeel da Laraba sun kar6i Ameen da Meenal. Mik'ama Ayusher Abadurrahman nayi, Na bud'e inda Galadima yake Na rank'wafo ina d'aukar Abadurraheem, shima mik'ama Feena nayi, itama Amaturrahman Na d'akkota Na rik'e, ganin ko motsi baiyiba nace, “yalla6ai yadai?”. 'Dan yatsinamin fuska yay saikace wani mace. Na kuma rank'wafowa ina d'ora hannuna saman goshinsa, tausayinsa ya kamani, dan kan akwai zafi alamar bayajin dad'i. Nace, “Sorry my king”. Idonsa yad'an lumshe yana murmushi. Nakuma cewa “ka daure muje ciki, sai a nemi maganin mura”. Nanma baice komaiba, saida yaja wasu seconds sannan ya ziro k'afa, nad'an matsa baya nabashi hanya ya fito. A raina dai ina jinjina jinin masu mulki, k'asaita da izza tarigada tazama jinin jikinsu, babu yanda za'ayi ka iya rabasu dashi. Da hannu yayma Drivers d'in alamar su shiga suma. Mune k'arshe. Shiga. ALLAH Sarki Yaa Marwan, harya tanadar mana wajen zama, gaskiya babu k'arya wajen yayi tsari, mukam mund'an shiga daga lungu kad'an, su Abba basa ganinmu bama ganinsu, inaga hakanne yasaka Galadima d'an sakewa yaci abincin, dukda bama wani Na kirki yaciba, Dana nuna damuwa saiya kalleni. “Karfa ki damu, inhar ina mura banajin dad'in komai, haka take wahal dani”. Cikeda tausayawa Na masa sannu, nima duk saina kasa cin abincin. Spoon d'in hannuna ya kar6a, da kansa ya koma bani abaki, dukda marairaice masan da nayi akan Na k'oshi bai saurareniba, baikumayi maganaba, saida ya tabbatar Na k'oshi da gaske sannan ya barni. Kowa yaci ya k'oshi yay nak Alhmdllh, muka fito da ledojin kayan mak'ulashen da Yaa Marwan shima ya saima kowa, dan kud'in abincin Galadima ya biya. Dagananfa muka damk'i hanya babu sanya, dan burinmu mu Isa Nigeria a yau, wancan zuwanma dan bamusan inda muka dosa bane. Aikam dai tafiya tayi riba, dan salla kawai muka tsaya mukayi, Azuhur da la'asar muka had'a muka kuma damk'ar Hanya, bayan magrib muka shigo Nigeria, nanma mun tsaya munyi sallar Magrib da isha'i, daganan muka cigaba, abinci ma sai saya akayi kowa yaci a hanya. Yanzunma dai Galadima baici Na kirkiba, dan bayajin dad'in bakinsa, da gaske Mura batai masa da wasa kam, dam duk bashida wani sukuni. Sai wajen 2am muka shiga namu garin, zuwa lokacin kowa yayi ligif, ga gari tsitt, sai motoci jefi-jefi Na matafiya irinmu, saikuma manyan motoci masu d'aukar kaya. Gidanmu aka nufa, saida aka fara saukemu harsu mama Rabi'a anan, Fadeel Yaa Marwan da Abbansu ne kawai aka nufi gida dasu su kam, shima Galadima masarauta aka juya dashi, sama-sama mukayi sallama Na fita, tausayinsa Na cin zuciyata, yana buk'atar kulawar matarshi matuk'a, amma ya zanyi. Duk y'an gidanmu sunyi barci, sai tsirarune suka fito y'anson ganin dami mukazo?. To babuma abinda aka fitar daga mota, kowa dagashi sai handbag d'insa ya fita. Koda muka shiga kowa wajen kwanciya ya nema, dukda sashen namu yad'anyi k'ura, amma bamu damuba, Inda zamu kwanta kawai muka karkad'e. ***************** Galadima yana shiga gida ruwan zafi ya had'a yay wanka, kozai sami sauk'in ciwon da jikinsa ke masa, yad'anji dama-dama kam, ya nema kayan barci masu kauri ya saka, dan muma dai nand'in cikin sanyin ake, gadonsa ya haye, ya shige bargo yana sauke numfashi da k'yar, babu dad'ewa barci yay awon gaba dashi. *Washe gari* Bamu tashiba sai kusan 12, su innarmu ne kawai suka tashi da wuri, y'an gidanmu anata shigowa musu sannu da zuwa, kowacce jikinta saiya fara zanyi, dan yanda muka dawo 6ul-6ul damu kad'ay ya Isa basu amsar muna cikin k'oshin lafiya, kuma inda mukaje wajene mai daraja. Duk wadda ta fita saita nufi gidan Innaro da nufin mata sannu da zuwa, ammafa dason jiyo gulma. Tab hajiya Innaro mai abin mamaki, zama tayi tiryan-turyan tana basu labarin garar arzik'i da wacece Inna. Ta rik'e ha6a tana tafa hannaye da fad'in “Yo Niko koda naji wannan halin dattako Na Ai'sha, Ashe jinin sarautace , shiyyasa duk shirmenkunan bata shigarsa, maganama saitaso ta kula maiyinta, duk shirme ya rufe mana idanu bamu fahimtaba, lallai yau naga tushen arzik'i Na gaskiya ba hayeba, nayarda da masu iya magana dakance duk Wanda yace shine to bashi bane wlhy.....”. Innaro dai taita zuba musu labari babu k'ak'k'autawa, sukam sun kume motsin kirki summa kasa, a yanda su inna suka dawo kawai ya Isa ya tabbatar musu da gaskiyar innaro d'in. Tunaninsu bai kuma birkicewa ba saida aka shiga fiddo tsaraba daga motocin da muka dawo dasu, kowacce saita shige d'aki ta koma lek'e ta window itada y'ay'anta🤣. Zarah da siyama da har yanzu suna gida, a sanyaye suka shigo gaida su inna, duksun rame sunyi duhu, dan kowacce tana son mijinta, amma gidajensu sun gagaresu komawa, dan bayan tafiyar su Munubiya saiga takardun saki daga mazajensu su duka. Duk munyi mamakin yanda sukai laushi da fita hayyacinsu, amma bamuce komaiba, muka tarbesu kamar yanda muka saba a ko yaushe. Nidai wlhy duksai tausayinsa yama kamani. Su Ayusher sukai shirin tafiya gida, iya abinda zasu iya d'auka suka had'a Yaa Marwan yazo ya kwashesu.. Suna tafiya nima sai hankalina ya koma ga mijina, waya Na d'auka Na kirashi dan naji Yaya jikinsa, harta yanke bai d'agaba, nakuma kira dai... Galadima Na kwance zazza6i ya rufeshi, tunda yay sallar Asubahi yakoma yakuma k'udundunewa a bargo, cikin barci yaji wayarsa Na ring, kasama motsawa yay balle ya d'auka harta tsinke kiran yakuma shigowa, hannunsa ya tura k'ark'ashin filon da k'yar ya jawo wayar, yabud'e ido kenan ta katse, harzai ajiye saikuma yaga my mata, kiranta yay yamaida idonsa ya rufe yana saka wayar a kunne batareda yayi maganaba. A sanyaye Munaya tace, “Yalla6ai are you okey?”. “My Queen!”. Ya kira sunana a hankali ba tareda ya amsa tambayar dana masaba. Sautin muryarsa kawai ya tabbatar min da lallai bashida lafiya har yanzu, rikicewa nai nacigaba da jera masa tambayoyi, babu wadda ya iya amsamin saida yaga nak'i inyi shiru yace, “relax dear, zan samu sauk'i karki damu”. Hawayen da suke zubamin Na share, Na tabbata abinda zai kwantar da Galadima ligif haka ba k'arami bane, inhar yazam ba ciwonsaba to lallai abin ya girmama. K'arasowa innarmu tayi da sauri cikin d'akin d'auke da Amaturrahman dake kuka, dukta rikice ta shiga tambayata lafiya?. Dole Na yanke wayar ina duk'ar dakai da saurin goge hawayena. Nace, “Innarmu shine baida lafiya har yanzun”. “Ya salam, murardai?”. Kaina Na d'aga mata. Amaturrahman ta d'oramin a cinya tana mik'ewa. “To ai bakiga ta zamaba kuwa, bara Na sanarma abbanku”. Ban iya cewa komaiba Na fara shayar da Amaturrahman ina share hawaye. Bansan miya faruba kawai naga Munubiya ta shigo tana had'a kaya, da tambayata ya jikin nasa?. Na amsa mata ne kawai cewar da sauk'i amma badan inada tabbacin hakanba. Itace take sanarmin wai Su Abba sunce muma mu shirya kawai mu koma d'akunanmu tunda andawo lafiya, zaman wankan ya Isa kawai...............✍🏻 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻 [8/22, 8:29 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* *_💡HASKE WRITERS ASSO...._* *_♦RAINA KAMA...!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_BOOK 3_* 👉🏻2⃣5⃣ .................Da mamaki Na kalli Munubiya ina kwantar da Amaturrahman. Nace, “Komawafa Munu?”. Tsayawa tayi daga shirya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83