Chapter 1
Chapter 1
[7/21, 7:47 PM] Aysha Galadima: *_typing📲_* 💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._* *_♦RAINA KAMA.....!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* __________________________ *_Kai jama'a yau dai kun Sani typing dole saboda munafurcin y'an bani Na iya, wannan karon kuma kurasa k'ullin da zakuyi sai akan Uwa da 'Diya?, nikam yau koda mamana (mamu gee) kwaikwayar RAINA KAMA tayi to wlhy birgeni zatayi, ai baiwace ma wani yayi Abu kabishi daki-daki kana kwaikwayo. Irin wannan shirmen naku baya cikin kan Bily, ba mamu gee ba koda watace aka jingina da hakan bazanji komaiba wlhy, sannanma nifa abinda yabani mamaki a writeup d'in da mamana tayi bata ambaci sunan RAINA KAMA ba aciki ko wani littafi daban, to tayaya y'an bani Na iya da tsugunne-tsugunne su anasu writeup d'in suka saka sunan RAINA KAMA? (Wlhy halin wasu daga cikin writers namu ko kad'an bashida k'yau, neman sunane kokuwa son asanine niban saniba🤦🏻♀)._* _Reader's kuma da naku, sometimes bakunanku basuda linzami, irin wannan abubuwan kune ke fara tsirarsu saisuzo kuma su buwayeku, Ku ke karanta RAINA KAMA DA TARAYYA Ku kusan banbancin abinda ke cikin kowanne, amma dayake Ku irin wannan dama shine farin cikinku saikuyita k'irk'irar abinda dolene daga k'arshe saiya zama rikici, to nikam zan sanar muku, awanan karon sai had'in naku baiyiba, Dan MAMU GEE DA BILYN ABDUL duk Abu d'ayane, daga tarayya har Raina kama buks d'inmu ne, mu muke rubuta abunmu, babu wata munafukar writer ko reader da mukayi shawara da ita kafin mu d'aura alk'alaminmu a takarda, masu had'a husuma kuma sai kusha fetur Ku had'iyi ashana kuyi bombing d'in kanku, ina dai shikenan ko?🙅🏻_. *Daga k'arshe inamai muku nasiha da kuji tsoron ALLAH, wlhy bashin naira 10 kacal yana hana bawa kwanciyar kabari, karo tsakanin rago da rago kawai akwai hisabi tsakaninsu, aranar kiyama bayan an tsaya hisabi duk Wanda kasani koya sanka saika Ganshi kakuma ganeshi, bawai kaitsaye za tantanceka akaika wuta ko aljanna ba, wlhy sai an tsidaka, ancire hak'in mutane a kanka, ka zagi wane babu hak'k'insa, ka harari wane, kama wane zind'e, ka cinye kud'in wane, ka had'a fad'a tsakanin wane, ka 6ata sunan wane, ka cuci makwafcin, ka...ka...ka...da yawan gaske, duk wani cin amana ko zalunci dakama wani inhar bai yafe makaba a wannan ranar sai an cire masa hak'insa a cikin ayyukanka, (Dan sune kad'ai guzirinka) komai tarin aikin alkairin daka tara inhar kanada irin wad'annan bashishshikan d'aya bayan d'aya sai an zaresu daga gareka, koda dabba da kafiri ka zalunta kuwa, idan dama bakada komai, sai ayita kwashe nasu zunubai ana lafta maka, sai angama tas, kabiya an biyaka saikuma a gwada ayyukanka a kan mizani, miyarage kuma? Saika koma gefe jiran sakamako. Wlhy y'an uwa babu babban tashin hankali irin kar6ar sakamako, a wannan lokacin uba baya gane d'ansa, y'a bata gane uwarta, miji baya gane matarsa saboda tsantsar tashin hankalin da ake ciki, da wane hannu xaka amsa, ina ne zaizama mazauni Na dindindin, duk baka saniba, haba y'ar uwata, kinada wannan babban aiki a gabanki amma kika shagala wajen had'a husuma irin ta social media wadda bansanki ba, baki sanniba, maybe ma har Abadan bazamu ta6a sanin junanmu ba, muji tsoron ALLAH wlhy, yakamata irin wannan abubuwan su tsaya hakanan, daga ni har mamana badan Neman suna mukeba, domin Isar da sak'o mukeyi a cikin tarayya da raina kama, burinmu kuma ko mutum d'aya ya amfanu da manufarmu ya wadatar, bawai tarin masu karantawa ba, ni miyasa babu Wanda yata6a tarata yacemin tarayya copy d'in raina kama ne? to Ku kama kanku please, kodan tsoron ALLAH.* _My Sweet mah-mah mamu gee wannan page d'in sadaukarwane a gareki, kiyi yadda kikeso dashi nabaki, ALLAH yabarmu tare, I love you irin trillions d'innan, kisamun albarka nakuma zama gagara badau😁😘._ Bilyn Abdull & Mamu gee RAINA KAMA ne mu, sannan munyi TARAYYA NE akan Isar da sak'o mai muhimmanci, mabiyanmu Na gaskiya a KAFTA kawai⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀😂👍🏻. HARUN da GALADIMA kuma Ku KAFTA naku wasan🤣🤣🤣🤸🏻♀🤸🏻♀✍🏻😜. __________________________ ~Book 3~ 👉🏻1⃣➖2⃣ ...............Saida suka fara tafiya sai Harun yafara jin tamkar k'amshin turaren Galadima yakeji, mamaki ya kamasa, ya kalli gaban motar yana fad'in “lawwali nikam kaji minakeji kuwa? k'amshin Sameer fa”. Murmushi Galadima yayi, baice komaiba sai “Uhmm”. Hakan yakuma d'aure kan Harun, kamar zai sake magana saiya fasa, ya d'auki wayarsa domin son kira yaji ina Galadima, yasan Abu dolene ke fiddashi da daddare daga masarauta, amma sai kira ya shigo a wayarsa, k'aramin tsaki yayi Dan ba'a ko'ina yake d'aga wayaba, ya yarda da lawwali drivern babansa waziri amma bakomai yake barin ya saniba, ganinfa an damesa da kiran saiya d'aga. Da sauri ya janye wayar a kunnensa yana lek'o kansa gaban motar danya tabbatar. shin ina tunaninsa ya tafi dahar ya iya gaza banbance lawwali da Sameer?. yace “Sameer!”. Galadima dake tuk'insa hankali kwance yana kuma sauraren wayar Harun ta abinda yasa akunne, saboda ya saita duk wayar dazata shiga ta Fita a war Harun saiya shigo wayarsa shima kota fita yace, “Uhmyim”. A tsorace Harun yakoma baya ya bigi seat da k'arfi, babu abinda zuciyarsa keyi sai dukan 100-100, wayarsa ya jawo jiki Na rawa yafara k'ok'arin kiran wani. Galadima yay murmushi, cike da izzar k'asaita yace, “bar wahal da kanka my dear friend, duk wata waya dazaka kira a yanzu wayata zata shiga”. Harun yay jifa da wayarsa a kujera jiki yana rawa, batare da wani tunaniba ya mik'e kawai ya shak'e Galadima, da hannu d'aya Galadima yake driving, hannu d'aya kuma yana k'ok'arin kare kansa daga shak'ar da Harun ya masa. Da k'yar yasamu ya gangara gefen titi, yasaka hannunsa d'aya ya bigi gefen cikin Harun daya samu damar shak'esa da k'yau, Dan numfashin sa harya fara fita afisge. Dukan cikinsa da Galadima yayi yasakashi sakinsa da sauri, Galadima ya juya yakuma naushin bakin Harun saiga jini, dama bai gama dawowa hayyacinsa ba daga dukan cikinsa da yayi. Harun ya fad'a saman kujera yana rik'e ciki da shafar hancinsa dayaji yana yoyo, kallon hannunsa yayi saiyaga jini, ya zaro ido cikin matuk'ar mamakin shi Sameer ya fasama baki, yo ko danbe zasuyi ai babu abin zai d'auka a jikinsa, (Dan shima Harun d'infa ba bayaba). Galadima daketa huci ya dafe sitiyari da kife kansa ya kuma tada motar a harzuk'e ya fara tafiya cikin tsananin gudu. Cikin hakki da fidda numfashi a wahalce Harun yace “Sameer n..n..ni ka daka? harda fidda jini?”. Banza Galadima yamasa yacigaba da tuk'insa, Harun ya kuma yunk'urawa zai tashi amma saiya kasa, saboda ba k'aramin duka Galadima ya masa a gefen cikiba, wajen ya k'ulle, dole ya koma ya kwanta yana cije baki da matse ido, hannunsa rik'e da wajen har yanzu. Suna isa inda ya nufa yay horn, saiga Nuren da kansa yazo ya bud'e masa k'ofa, a fusace ya shiga gidan, shi Nuren ma har yana tsorata. Yana tsaida motar ko kashewa baiyiba yabud'e ya fito a harzuk'e, inda Harun yake ya bud'e ya jawoshi, yakuma kai masa naushi, shima ya kai masa dukda azabarda cikinsa ke masa. Nuren da Muftahu sun iso wajen a hanzarce, Dan ganin danbe Na Neman hark'ewa tsakanin aminai guda biyu, Nuren yaja Harun, shikuma Muftahu Galadima. “Waishin mikukeyi ne haka brother? Da girmanku da ajinku kuke danbe? danbe fa? Wannan wane irin kuma abin kunyane? Lallai da y'an
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83