Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 32

Chapter 32

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,210 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sallar La'asar, kafin a dawo a cigaba da gashi😜. ....................................★ Bayan sun idar da salla C.P ya kira Galadima, suka shaida masa su Alhaji Bana suna hannunsu yanzu haka. Galadima dake tsaye yace, “Alhmdllh, zuwa safiyar gobe kuma sai a kai case d'inmu Court, Dan inason komai yafarune cikin gaggawa ya k'are, bana son jan jiki a aiki”. C.P ya kalli IG Dan jiran amsa. Kai IG ya jinjina masa alamar za'ayi hakan. C.P ya shaidama Galadima amsar IG. Galadima yace, shikenan, shi yatashi daga aiki, saikuma safiyar gobe. C.P zaiyi magana I.G ya dakatar dashi alamar ya barsa kawai. Ta6e baki Galadima yayi yana yanke wayar, ya maida kallonsa gasu Muftahu da duk suna maidashi television, gira d'aya ya d'age musu, sukuma sukai masa jinjina👍🏻. Kauda idonsa yayi ya maida ga yaran, yace, “yaya akwai mai buk'atar wanka ko barci?”. Gaba d'aya suka amsa da duk suna buk'ata. Kallon Ameer da Saleem yayi yabada Umarni da ido. ..............................★ 'D'aya bayan d'aya suka dinga kaisu suna wanka, duk Wanda yagama sai abashi lemo, batare daya San miye acikiba saiya shanye, daga sha ko mintuna 3 basa k'arawa suke 6ingirewa barci🤣. 🤣🤣ho Galadiman mu kasan takan tsiya, Zuma kenan, ga zak'i ga harbi🤸🏻‍♀, kaga Na Munaya baban triplets, bada kanka a sare kaje gida kacema su mama Fulani an k'illesa👌🏻😜😂. Da akazo kan Harun k'in tankawa yayi, Dan haka Galadima yace su barshi kawai, amma harsu Malam Saminu da Alhaji Darma su Farhat duk sunma Kansu gyad'ar dogo sunje sun mik'e zasu huta. Nuren ya kalli Galadima cike da tausayi yace, “Brother kaima kad'anje ka huta mana”. Murmushin gefen baki Galadima yayi, yajawo lap-top gabansa yana girgizama Nuren kai alamar a'a.................✍🏻 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu_*😭👏🏻 [8/3, 4:45 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* *_💡HASKE WRITERS ASSO...._* *_♦RAINA KAMA...!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ___________________ *_Na gaisheku, gaisuwa irinta musamman d'innan. Makaranta buk d'in RAINA KAMA dake JAMI'AR KUST dake WUDIL, alkairin ALLAH yakai agareku, ALLAH ya yalwataku da ilimi mai tarin albarka damu baki d'aya._* Ina inyinku irin Trillion's d'innan my guys🤸🏻‍♀😘😘😘😘❤❤. ____________________ *_BOOK 3_* 👉🏻1⃣7⃣ ...................Abin surutu lallai ya samu, mak'iyan Galadima kuwa duk sun kasance a tsorace, Dan ba kowane ya fahimci inda shirinsa ya dosaba, hakama a cikin masoyan nasa, wasu suna ganin daidainsa wasu kuskurensa, kowa da irin fahimtar dai da yayma lamarin. Yauma dai haka suka kwana zagaye da police. Amma su IG duk sun tafi, d.p.o ne kawai tare da tawagarsa, kamar kuma yanda ya buk'ata sunakan tattara case d'in zuwa Court. 6angaren su Baffi kuwa lauyan Abie dukkan shirye-shiryen shiga Court suma suna akanyi. Dan dukkan shirin Galadima yasan dashi tsaf, hakan yasa koda yagani baiyi mamakiba, kisan Ahmad daine da akace yayi yabashi mamaki, dukda zuciyarsa bata aminta Galadima zai iya kashe yaro ko d'ayaba. Amma lallai hakan ya sakashi a rud'ani, harma ya kira sir Isa sukayi maganar. Sir Isa yace shima yagani a labarai amma gaskiya bai yardaba, akwai dai abinda duk basu saniba, Dan Galadima bazai aikata hakanba. Da wannan maganar ne Baffi yad'an samu Nutsuwa yacigaba da tattara bayannsa daduk abinda zasu kafa hujja dashi a court. Duk abinda ke faruwa Momma tasan komai. Dan Galadima ya sanar mata, baya kuma 6oye mata dukkan shirinsa akan wannan case d'in dama, amma sai tayi lup tamkar batasan anaiba, koda labari yazo musu saita taya su Aunty Mimi rud'ewar itama, harda pretending d'in kukanta tana Neman number Galadima, amma sai tak'i wucewa. Daga Baffi har mai martaba babu Wanda ya kirata akan batun, duk a nufinsu Na 6oyemata kar hankalinta ya tashi balle Na mahaifinsa dake kwance yana fama da kansa. Amma saiga kira daga mama Fulani, tafad'ama Momma maganar daduk yazo bakinta ta 6atanci akan Galadima, itadai momma cikanki batace da itaba, har tayi ta gama ta yanke wayar. Saiga gimbiya Zulfah ma ta kira Momma, itakam ai harda kukan makirci irinna y'an duniya. Itama dai tayi kid'anta tayi rawarta Momma Na saurarenta. Koda ta Yanke wayar saita kira munaya. Taita kwantar mata da hankali da lallashinta akan ta kwantar da hankalinta. Insha ALLAH komai zaizo k'arshe, kowace rayuwa takan tafine da jarabawa. Babu wani rai dazai rayu cikin farinciki da samun yanda yakeso 100%, dolene kowacce rayuwa akwai NATA k'alubale, nakowa kuma akwai ta hanyar dayake fuskantar nashi. Sosai Munaya ta gamsu da nasihar momma hakannema yad'an samu mata nutsuwa tad'an rintsa a wannan dare. .................................★ *_WASHE GARI_* Nasara ta farko da aka wayi GARI da ita shine farfad'owar Abba cikin hankalinsa, saidai har lokacin baya sanin Wanda yake a tare dashi, hakanne yasaka likitocin fad'in a k'ara masa lokaci yasamu isashen hutu. Ahalinsa sunsamu Kansu a farinciki ainun, hakama masoyansa, shikansa Galadima Yakuma samun kwarin gwiwa da karsashi akan aikinsa. An kuma shigar da case d'in Court kamar yanda Galadima ya buk'ata, abinka da lamarin manya har antsaida washe gari a matsayin ranar da za'a zauna Court d'in. Yinin ranar zubur Galadima baiyi magana da police ko d'ayaba, koda sun buk'aci magana dashi saiya had'asu da Muftahu ko Nuren. Daga k'arshe dai dolensu suna k'yaleshi. ★★★★★★★★ *_⚖RANAR SHIGA COURT_*⚖ Yau ta kasance ranar zaman court, shari'ar su Galadima Ce kuma farko da za'a fara saurara a court d'in, lallai wannan shari'a ta manyace, Dan court d'in ta cika da manyan k'asa wad'anda sunfi kud'i wahalar gani, amma yau gasu available, y'an jaridar ma manya-manya aka bari, k'ananun suna awaje sunyi tururuwa domin rajin nemawa d'an uwansu hak'insa wato Alhaji Auwal fharuk dayake a asibiti har yanzu cikin halin ni y'asu. Mukuwa talakawan gari y'an jiran jin yazata kaya mu sai dai gani a tv☹. Yo Wayaba asibi laya ubanta ba malam ba😬, ai ko babama da babansa aradu🤕. *_Court_* d'in tayi tsit babu abinda kakeji sai gudun fankoki da tarin manya jefi-jefi, dan babu alamun fara'a a fuskar kowa. Daga masarauta dai k'anin mai martaba ne yazo wato Garkuwa Hayatudden Abubakar, sai wasu daga tawagar y'an majalissar Sarki, harda waziri dayazo bisa tirsasawar mai martaba. Daga masarautar su Papi kuwa yarima mai jiran gado mahaifin su Nuren wato Wambai Abubakar Abdul-fatah Wanda yagaji sunan kakansu Galadima marigayi Abubakar kenan. Saikuma wasu daga jiga-jigan masarautar suma. Fitowar alk'alin alk'alai Othman Ibraheem gwannu tasaka dukkan jama'ar Court d'in mik'ewa domin girmamawa a garesa, (dan shima Alk'ali baba uban su babane shima🤭😝). Saida ya zauna sannan yabada izinin kowa ya zauna, Court d'in tayi tsit kowa ya Zubama alk'ali dake karanta takardar k'arar hankali kwance ido, kusan mintuna 3 ya d'ago yanabin Court d'in da jama'ar cikinta da kallo ta cikin eyeglasses nashi daya jawo k'asan ido, d'auke idonsa ya ya maida ga Lauyoyi dake zaune suna jiran kule, suce cas. Gyaran murya yayi yana maida idonsa ga takardar da fad'in “Ina wad'anda suke k'arar da kuma wad'anda akai k'ara? Idan kuma Lauyoyine to na masu k'ara da wad'anda ake k'ara suna inane?”. A tare Baffi suka mik'e shida abokan aikinsa su uku, cikin girmamawa ga alk'ali ya risinar dakai yana mik'a gaisuwa da fad'in “yamai girma mai shari'a sunana Barrister Usman Audu Tsanyawa, nine lauya mai kare Wanda yake k'ara, tare dani akwai Yohan Emanuel, da Bilkisa Ibraheem Musa (kutu melesi su bilyn Abdul anzama lauyoyin novel🤸🏻‍♀😎🤣😜). Bilkisu da yohan suka risina alamar girmamawa. Alk'ali ya jinjina kai alamar gamsuwa, su Baffi

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});