Chapter 36
Chapter 36
wasu shekaru, amma lallai da sanadi, wannan kuma sanadin shine Na d'auki tsawon shekaru tundaga tasowata har zuwa yau ina nema. tun daga lokacin dana mallaki hankalin kaina nasan minene matsalar mahaifina natashi da burin d'aukar fansa, sai dai kuma tayaya? Wannan shine yayta wahalar da Muhammad Sameer a tsawon shekaru”. Galadima ya k'are maganar idonsa Na ciko da hawaye, yay murmushin takaici yana jinjina kansa da had'iye hawayen. Hakanne yasaka jikin wasu fara yin sanyi, musamman wad'anda suka k'ullaceshi da farko. Galadima ya cigaba da fad'in, “Ban taso maraya ba, amma nayi rayuwa irinta marayun, ALLAH shine gatana saikuma mahaifiyata da kakana da suka tsaya tsayin daka wajen tsayamin nazama jarumi wajen sanin wahalhalun rayuwa Na yau da kullum, duk Sana'a mai wahala kad'ance banyitaba a k'asar daba tawaba, gakuma gefe ana gwagwarmayar Neman ilimi, ga burin son sanin suwaye suka durk'usarmin da mahaifi?, ban cutar da kaina wajen nutsuwa Na fahimci rayuwa ba, hakama nabama karatuna muhimmanci saboda k'aunarsa da nakeyi, duk da banida burin yin aiki a k'ark'ashin kowa, Alhamdllh yanzu haka inada Company Na had'aka da duk shekarar duniya yake fidda wayoyin Hannu da computers dakan zagaya cikin duniya, ina alfahar da samun cikar burina sosai, Na dad'e ina bulayin Neman hanyar bincike akan abinda yafaru da Abie na, alokacin mutum d'ayane zuwa biyu ke bani gudun mawa, wato lauyan mahaifina, baffina Barrister Usman Audu, sai kakana Sarki Abdul-fatah. Ganin inata wahala sanan babu wani haske a cikin lamarin sai suka bani shawarar mizai hana a nemamin aiki k'ark'ashin wata hukumar tsaro, da farko ban aminceba, Dan irin wad'annan ayyukan basa wani birgeni, hasalima haushin masu yinsa nakeyi, Dan sun gaza binciko Wanda ya cutarmin da Abie na. A tashin farko dana nuna banaso Papi da Baffi sun k'yaleni, basu sake min magana ba, sai wata rana kwatsam wani Abu yafaru anan Nigeria, wasu y'an ta'adda sukayi mummunar 6arna a sirrin gwamnati, k'ark'ashin hukumar DSS. wannan 6arna ta rikita Nigeria sosai a lokacin, shekaru 10 kenan inhar ban mantaba, a lokacin nagama bautar k'asata anan Nigeria ina shirin komawa india, bansan ya akayi sukasan nasan Computer ba, har masarauta akazo aka rok'i mai martaba akan Na taimakesu. Da farko kam naso bijirewa amma babu abinda iyayena zasuce nayishi banyiba inhar bai sa6a shari'a ba, nasanma bazasu sakani wannanba, bisa umarnin mai martaba Na amince da gwadawa idan zan iya, haka akaje dani headquarters d'insu, tun hawan Computers d'in danai a tashin farko Na gane da had'in kan waaunsu aka kwashi bayanan, sannan masu kula da Computers d'in sunada buk'atar k'arin ilimi ma gaba d'aya. Cikin sauk'i Na d'akko bayanan da aka d'auka Na dawo musu dashi, sannan nasaka musu securitys masu tsaurin gaske daba wani mahaluki dazai kuma musu irin wannan kutsen. Ni ban d'auki abinda nayi matsayin komaiba, amma agaresu sun girmamashi, sunkuma biyoni har gida da rok'on kasancewa a cikinsu amma nak'i Sam, nama tattara Na koma India, Ashe sunata bibiyata ta wajen kakana, to shima dama yana burin nayi aikin, Dan haka yabasu goyon baya, sannan yaje har India ya sameni da batun, ya nunamin ta wannan hanyarne kawai zan iya binciko abinda ya faru da mahaifina cikin sauk'i, hakama Baffi ya fad'amin a lokacin, Na zauna nayi nazari dakuma samun kwarin gwiwa daga Mahaifiyata. Rana d'aya sai nima naji yakamata Na amince, Dan haka Na amince, tundaga lokacin nashiga cikin hukumar CID nima, saidai ina musu aikine cikin sirri, a hukumarma ba kowa yasan daniba, tunda ni komai ta computer nake gudanar dashi. Sir Isa Maharazu shine ya taimaka min wajen binciko file Na binciken case d'in mahaifina, Wanda tun kusan shekaru 8 mai kula da case d'in ya rasu, Wanda kuma suke ta fannin y'an sanda suma sukayi shiru, daganan aka ajiye case d'in gefe kawai. Tun a file d'in nafara cin karo da sunayen wasu daga cikinsu Alhaji Lawan tanderu. Nasha mamaki kwarai da gaske amma sai banyi wani yunk'uriba, ina wata shida da aiki wani yaso min kutse a cikin Computer, ta silarsa nagano uban gidansa, har zuwa Kansu Marigayi Alhaji Labaran kachia. Tundagafa wannan lokacin saina tsananta bincike da kwakwalwa dakuma tannin aiki, bisa taimakon sir Isa, mun baza yara cikinsu Tanderu batare da sunsaniba, kullum kuma cikin bin diddigin motsinsu suke. Kwatsam sai Tanderu ya rasu sanadin had'in mota, babu jimawa shima Alhaji Labaran khacia ALLAH yamasa rasuwa sanadin rashin lafiya. daga nan saina d'an dakatama gaba d'aya da wani bincike Na koma gefa Na zuba musu ido kawai. Saida Na d'auki kusan shekaru biyu ban sake wani yunk'uriba sai kwatsam muka wayi gari mijin Yayata Haneefa yayi had'arin Mota, saidai kuma a ranar ne aka turomin massage daya nuna accident d'in nashi akwai saka hannu a ciki, dayake bai rasuba a lokacin sai a asibiti bayan awanni uku da kaisa, Alhaji shehu Darma abokinsa ne Na kut da k'ut sannan d'an uwansa, Dan haka yana tare damu a wajen, saina matsanta akan tambayarsa kozai fad'amin akan miya faru dashi kafin had'arin? Bai iya cemin komaiba sai murmushin k'arfin hali da yayi yana kallon Alhaji shehu har numfashinsa ya k'are, wannan kallo ya tsayamin a rai sosai, Dan nagaza mantawa dashi, abinda Yakuma k'arfafa min zargin Alhaji shehu shine Aunty Mimi Na fita daga takaba sai Yace yanason aurenta, nine Na hana, nama tattarata gaba d'aya itada y'ay'anta Na maidasu india, dukda dangin mahaifin yaran sunso d'aukarsu suma. Dama can lokaci-lokaci Alhaji shehu yakanbi mijin Aunty Mimi suje duba Abie, dan haka ko bayan rasuwarsa bai daina zuwaba, abinda na fara fahimta shine Samha d'iyar marigayi tana tsoron Alhaji shehu, amma shi yana tsananin nuna mata kulawa dayin kaffa-kaffa da ita a gaban mutane. Wannan ma yasa na kuma saka ido a kansa, abinda Na fara karo dashi shine Alhaji shehu yana tursasa Samha ta hanyar mata barazana akan ta d'akko masa wasu sirrikana”. Galadima ya murmusa cikin takaici yana gyara tsayuwa da goge fuskarsa da handkerchief. Yaciga da fad'in, “Tunda Na fahimci hakan saina jata a jikina, nakuma dinga ajiye mata dukkan abinda yasaka ta d'akko, itako data gani saita tura masa saboda tsoron barazanar da yake mata. Suma sauran Na cigaba da bibiyarsu suda ayyukansu, so banida matsala da sauran mugayen halayyarsu, nidai kawai wadda ta had'amu nakeson Sani, Dan Na gano sun gana da mahaifina ana gobe abinda ya sameshi zai sameshi, kuma yafito daga d'akin tattaunawar ransa a 6ace. Batanci da akaimin a shekara d'aya data wuce cikin jaridar manuniya shine mafarin yalwatur haske a matsalolina, dukda Na fahimci ankai tsawon shekaru ana bibiyar dukkan al'amurana, kuma inhar Nazo k'asarnan kullum cikin bibiyata ake, domin rufe bakin mak'iyana Na auri wadda sukaso sakawa a matsalar dabatajiba bata ganiba, wadda a yanzu Alhmdllh itace uwar y'ay'ana, nasan hakan ya girgizasu a lokacin kwarai da gaske, adalilin zama da ita nama fahimci abinda ban fahimtaba da farko, Dan da Duk zargina ko da itane aka had'a kai wajen Neman 6atamin suna, amma sainaga dukba haka baneba, ya mai shari'a Alhaji Auwal Fharuk sai shine surikina mahaifin matata, kuma anyi yink'urin kasheshi watanni kusan 7 da suka shige, saidai ALLAH ya k'addara yanada sauran kwanaki a gaba, bisa dalilin yun k'urin kisansa ne kuma Na fara karo da alak'ar case d'in mahaifina dashi, hakan kuma tafaru
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83