Chapter 80
Chapter 80
wannan sadaukarwar ga iyayenka da al'ummarka, domin samun damar k'ar6ar sakamakonka wajen adalin Sarki mai tarin rahma da jin k'ai. Zuciya da tunani duk mallakar gangar jikice, haka gudanar jini da motsin ga6o6i, su papi sune sukasan tayaya ka cancanta kaida d'an uwanka, har suka d'auki wannan nauyin suka d'ora muku, Ku kar6i yau d'unku da hannu biyu, domin jiyanku tazama labari, Ku hidimtawa gobenku domin Ku ribantu da jibinku, wannan shine kawai masalaha mai k'ayatarwa ga mu ahalinku, masu ganin baka kaiba saisu ajiye makamansu su tabbatar da ka kai d'in, kazama RAINA KAMA mijina, kosu amince, ko karsu amince kaine RAINA KAMA”. Tsam ya rungumeni yana fad'in “kece RAINA KAMA munaya, domin a dalilinki ne suke ganin nayi feeling, har ake ambaton ni da sarauta har Abadan, su ganin auren talaka shine k'ask'anci, shine ke nufin ka koma k'asa, a yak'ininsu saika auri y'ar wani mashahurin Sarki ne darajarka ke a idonsu, sun manta ba talaucine ya rarrabe tsakaninmu ba, Wanda yafi wani bautar ALLAH shine mafifici a cikin bayi, su Papi sun tabbatar min kina d'aya daga cikin manufofinsu na bani Sarauta, sunason tabbatarma duniya da mai sarauta zai iya auren d'iyar talakawa, basai y'ar mai mulki irinsaba, sunason duniya tasan shima talaka akwai baiwa da darajar da ALLAH yamasa fiye da mai mulki, sunason duniya tasan ba mai mulki bane mafi k'ololuwar daraja a cikin bayi, kowanne Bawa da tarin daraja da baiwar da ALLAH ya masa, kinga kuwa kece RAINA KAMA my heartbeat, ko ni kin zamemin RAINA KAMA balle su da suke tunani ba daidaiba”. Kasa magana nayi, muka rungume juna tsam cikeda so da k'auna. An cigaba da gudanar da gagarumin biki na wannan nad'in sarauta, kwanaki 5 cif akayi anayi, danma mutuwar gimbiya zulfah ya rage armashin bikin. bayan lafawar komai da sati biyu mukaje India Galadima ya maida dukkan harkokinsa nacan ga Sauban daya zama tilas ya d'auki matarsa su koma can, dole kuma ya ajiye aikinsa duk da sonsa da yake, su Vijay zasu cigaba da kulawa da komai, idanma suna buk'atarsa zai cigaba da kawo shawarwari. Mun dawo da kwanaki biyu aka gama kammala aikin Company d'insu na nan Nigeria, Wanda dole su Vijay sukazo suka aiwatar da komai, zuba masa kaya da d'aukar ma'aikata da dukkan abinda yakamata ayi. Wata d'aya cif a tsakani aka basa umarnin shirya fara gudanar da mulki, Shiga fada da nad'e-nad'en sarautu da zaiyi, dakuma Neman matar aure dazai k'ara.🤦🏻♀ Wannanfa Abu ya tayarmin da hankali sosai, ga cikina ya tsufa, aiko na birkice masa naita kuka, kai wlhy kishiya da ciwo, duk dauriyarka saikaji babu dad'i, musamman idan kana son mijinka kuma. ALLAH Sarki Momma Uwa ta gari, itace taita kwantarmin da hankali da kalamai masu sanyaya zuciya, hakama Galadima yayta lallashina da nunamin muhimmancin lafiyata kodan tsohon cikin dake jikina, itama Munubiya da Innarmu haka, nima da naga mijina da kowa na son ganin kwanciyar hankalina saina kwantar d'in, na kar6a k'addarata da hannu biyu. Da farko d'iyar Mom akace ya aura, bankuma San yanda akayi ya zameba yace yabani wuk'a da nama na za6o masa dukkan wadda tamin, koya take wlhy zai aura shikuma. Kusan sati biyu daya bani sainaita nazari da hasashen wazan za6a masan, haka kawai matashiyar budurwa Hafsat da muka ta6a had'uwa a jirgi ta fad'omin a rai, lokacin inada cikinsu Amaturrahman, tamin wani taimako da Galadima ya yaba mata sosai, Wanda harna kamashi yana satar kallonta, amma a time d'in saiya basar kamar yanda halayyar tasa take, Nima sai banja maganarba, mukan gaisa da Hafsat miss xoxo time to time, amma mun dad'e bamu had'uba, inagama tun taron sunan su Abdurrahman da tazo. Muna zaune dashi na lalubo hotonta da mukayi ranar suna tare na nuna masa. “My king wannan ta makane?”. Kar6ar Hoton yay yana kallo, yay wata irin zabura yana ajiye hoton gefe da hararata, “Kina zargin ina sontane komi?”. Murmushi nayi ina d'auke hoton, nace, “yanayinka da amsarka kawai ta wadatar dani ranka ya dad'e, danason ma kanason miss xoxo da tuni na had'a wannan alak'ar wlhy, ALLAH yabamu zaman lafiya”. Duk yanda yaso bijirewa da nuna ba haka bane ban sauraresaba, na nunama Momma photo aka shiga binciken miss xoxo. A cikin sati biyu aka gama komai, duk da itama ta nunamin bata aminceba. Duk da kishi na cina haka na jajirce tsakanin borensu, babu 6ata lokaci akasha biki. Da kaina namata rakkiya d'akin mijinta a maimakon rakkiyar jakadiya da har yau bai za6aba., nai k'ok'arin danne kishina nai mana addu'ar zaman lafiya. Na dawo d'aki ina kuka da rungume y'ay'ana, akuma asubahin farko na farka da nak'uda. Wadda har aka wuce dani asibiti Sarki Muhammad Sameer bai fitoba, yanacan yana lallashin amaryarsa daya maida cikakkiyar mace a daren jiya. Na sauka lafiya na haifi d'a namiji mai kama dani sak, sai daga baya labari ke kaiwa kunnen Sarki Muhammad Sameer, ya rikice da murna, gashi babu damar binmu a asibiti, dole ya hak'ura har muka dawo. Fad'an farin cikin samun wannan haihuwa ga Sarki 6ata lokacine, hakama su Abie da tsohon Sarki da a yanzu suka koma daga gefe suna koyama yaransu dabarun mulki. Washe garin suna kuma Sarki Muhammad Sameer ya zauna a fada, tare da yin wasu nad'e-nad'e, hardasu Badi a ciki, sarkin mota da Sarki k'ofa sunce iya wuya suna tare dashi. Haihuwar danayi Ce ta d'auke hankalina daga damuwar kishin mijina da wata, duk da bana nuna kishin dama a fuska balle Hafsat ta fahimta, dan Alhmdllh tarbiyyarta tasa muke zaune lafiya, saima k'ok'arin jan yarana da take a jikinta, yarona yaci suna Abdul-fatah, papi kenan, daga Hafsat kuma Sarki Muhammad Sameer yace ya tsaya, mata biyu sun ishesa, ALLAH yamusu zaman lafiya. Rayuwa ta cigaba da gudana cikin nasarori, wajen saloon d'ina nata ha6aka, da kud'in shigarsa na d'auke kaso mafi tsoka na nauyin gidanmu, mahaifina ma yasamu sarauta da Sarki Muhammad Sameer ya nad'ashi, hakan yamin dad'i sosai. Munubiya itace mai kula da ladies mirror, office d'inma ita ke zamansa time to time, danni banida wannan damar a yanzu, fitarma sai wadda ta zama tilas nakeyi. Sarki Muhammad Sameer nada watanni takwas akan mulki ALLAH yayma mama Fulani rasuwa, tsakaninta da papi wata 1, wannan rasuwa biyu ta matuk'ar girgizamu, dan Sarki Muhammad Sameer kusan zarewa yayi akan mutuwar papi, yabasa gudunmawa mai yawa a rayuwarsa, wadda mantata abune mai matuk'ar wahala a garesa, mai makon babansu Nuren ya hau mulkin, sai yasa aka nad'a Nuren d'in. Sarki Nureddin ALLAH ya tayaku ruk'o baki d'aya. Babu dad'e da nad'im Sarki Nureddin akasha shagalin bikin Saleem da Feena, bikin dayay armashi sosai, dan itace last mace dasu innarmu zasu aurar, saura y'an k'ananun y'ay'ansu Aryaan, Aiyaan da Ahmad, Wanda a yanzu sun zama samari masha ALLAH, dan duk suna sa2 a secondary school, jirama Sarki Muhammad Sameer yake su kammala ya had'asu da Khaleel su wuce karatu. A yau kuma Munubiya ta kawo mana ciyara da y'ay'anta Meenal, Ameen da k'aramar Ai'sha muna ce mata Islam. Munsha hira sosai, taita mamakin yanda nake zuba mulkina, yo matar Sarki uwar gida wasace😂👍🏻🤸🏻♀🤸🏻♀. *_BAYAN WASU SHEKARU_* Rayuwa ta shud'a ababen dariya Dana kuka sun faru iri-iri, an haifi wasu wasu sun rasu, hak'urin zama Na yau da kullum,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83