Chapter 26
Chapter 26
k'arama kamarta zata iya tasirantuwa da abinda ta fad'a, mizai hana shima ya samu jarumta cikin tagomashin fik'irarta. Mik'ewa yay tsaye yana tattara kayansa da fad'in “Bara Na wuce, sai kunji yadda zata kaya kawai”. Basu barshi yatafi shikad'aiba, saida sukai masa rakkiya har masarauta, koda ya shige sashensa saiya kulle kansa, domin yin shiri. Hummm,🤸🏻♀shirya da k'yau Galadiman mu. ★★★★★★★★★★★ Abinda ya faru da Abba shine, bayan yagama kammala shirinsa domin baro inda sukaje shida S... halluru daya jashi domin masa rakkiyar tafiyar kwanaki biyu kacal. Lafiya lau suka shiga mota zasu taho, amma sai shi S... Halluru ya dakata da cewar Abba yayo gaba, shi anmasa kiran gaggawa, bai kuma kamata ace ya tsaidashiba shi, tunda ya sanarma iyalansa yau zai dawo. Da farko Abba kamar zaice suzauna kawai harya gama, saikuma tunanin yariga da ya sanarma su innaro zai dawo ya fad'o masa, shiyyasa kawai yataho, basuyi wani nisa da tafiya ba driver ya tsaya wai motar Na d'aukar zafi, ALLAH Sarki Abba, sai shima ya fita domin taimaka masa, suna tsaka da duba motarne garadan samari hud'u suka fito daga ma6oyarsu sukai ma Abba d'aukar amarya. Duk yanda yaso kare kansa ya gaza. Driver da dama duk cikin shiri yayi haka saiya hau tsallen k'arya cikin pretending yana ihun azo a taimakesu, (🤦🏻♀bayan yasan baza'a samu kowaba a wajen tunda jejine☹). Abba mutumne mai dagiya akan ra'ayinsa, hakan yasa duk yanda sukaso yabasu had'inkai akan zancen Camera yak'i, yama dage shi baisan Cameran da ake magana a kaiba, kuma dayaso basun tun lokacin da ake bibiyarsa da dukiya mai tsoka daya bada, amma basuda kud'in dayakai darajar camera d'in, sannan inda zai bada kodan barazana da rayuwarsa da sukasa aikaitayi tunba yanzuba daya bada, amma yasan ruhinsa Na hannun Wanda ya halicceshi, shine kuma mai kar6a aduk lokacin da yaso, inma sun kasheshi dama kwanansa ya k'arene, Dan haka subar wahalar da Kansu kawaima. Wannan maganar Ce ta fusatasu, wani ya daki Abba a baki harya fashe, dukda yaji zafi saiyayi murmuahi kawai yana kauda kai gefe. Wanda sukasa yamusu aikin lalata documents d'in Galadima Na cikin Computers ne ya ankarar dasu zoben hannun Abba akwai wata kimiya a cikinsa, wannan ne ya sakasu cire zoben daga yatsansa, shi Abba saima yanzune yasan manufar zoben, yay murmushi, Dan hakan ya tabbatar masa cewar Galadima yasan wani Abu game dashi. Duk yanda suka ringa k'ok'arin yima Galadima mugunta a sirrinsa Na Computer Abba Na kallonsu, hankalinsa kuma a tashe yake, amma jarumin namijineshi mai iya sarrafa kai aduk yanayin daya kasance, ko'a fuska bai nuna musu yana tare da damuwar abinda sukeyinba, saida Galadima ya kashe komai nasune Abba ya sauke 6oyayyar ajiyar zuciya, dukda yasan hakan ba shine nasaraba. Wanda suka saka aiki mai suna William yashiga rud'anin abinda Galadima yayi, Dan da farko yanata cika baki babu wani d'an African daya isa ja dashi a fannin ilimin Computer, bak'ak'en fatar ai a wajen su suke koyan komai, ta Yaya kuma zasu fisu Sani?. wad'annan kalamai nasa sun Sosa zuciyar Abba da sakashi cikin takaici, shiyyasa yayta jerama Galadima addu'ar samun nasara a zuciya. Yayinda sukuma wad'anda akema aiki suke kuma hurama William kai da kwanzartashi (ko kishin Kansu basayi😏, a zageku da kuma k'ask'antar daku kuna yabon mai ganinku marasa daraja🤦🏻♀, wata dai bahaguwar rayuwa sai bak'in fata😏🙄. Dak'ilesu da Galadima yayi ta hanyar kashe komai ya fusatasu suda William d'in, suna kuma kunna Computers d'in komai naciki ya goge, wannan Abu ya rikita William matuk'a, gashidai yagama proud d'in shi kwarone kuma bak'in fata d'an Africa ya masa kwaf d'aya, dukkan fushinsu saiya dawo kan Abba. Ana cikin haka saiga Alhaji halluru da sauran tawagar y'an group d'in, wad'anda sai yanzune suka samu k'arasowa, da farko Abba ya zata Alhaji Halluru taimakonsa yazoyi, saida yaji suna masa izgilanci sannan ya fahimci komai, cikin tsantsar mamaki yace, “Alhaji Halliru da kanka?”. Ta6e baki Alhaji Halluru yayi, yace, “zaka bani takarar Governor ne?”. Abba yay murmushin takaici yana fad'in “Tir da kai Halluru, wannan ai jahilcine, ALLAH shikad'aine ke bada mulki ga Wanda yaso, akuma lokacin dayaso,, yanzu kana nufin duk shekarun daka d'auka a jikina kai dama da manufa kake tare dani?”. Alhaji Halluru ya kuma ta6e baki yana murmushin mugunta, yace, “Alhaji Auwal kenan, ai bama zaka tabbatar da hakanba sai y'ay'anka da kansu sun d'akko min camera sun kawo, sannan mukuma kasheka a gabansu babu yanda zasuyi, yanzu haka suna gida, zuwa anjima kad'an kuma camera zatazo garemu”. Zufa ta fara karyoma Abba a dukkan sassan jikinsa, danjin za'ayi amfani da gudan jininsa wajen tarwatsa abinda yad'au shekaru yana rik'ewa amana, k'ala baice da Alhaji Halluru ba, su kuma sai kiraye-kirayen waya suke Na had'ama Galadima tarko.🤦🏻♀ Abba ba tausayin kansa yakejiba, tausayin Galadima yakeji matuk'ar tik'ewa, Dan ganin rai kusan 15 kowa k'iyayyarsa akansa take da muguntarsa... ★★★★★★★★★★ Tunda Galadima ya shigo bai zaunaba, saida yagama had'a komai dazai buk'ata, yabama sarkin mota yakai cikin motar dazaiyi amfani da ita, alwala yay yafita salla massalacin masarautar, bai yarda sun had'u da Sarki ba, yay fitowarsa, koda ya dawo saiyasha magani ya kwanta, kaikace bashida wata matsalane, babu dad'ewa kuwa barci yay gaba dashi. Bai tashiba saida aka kira sallar la'asar, nanma massalacin yaje, bayan ya dawo yay kiran Momma ta video call, duk suna asibitin hardasu Samha, d'aya bayan d'aya ya gaisa da kowa, Samha harda kukanta tanason zuwa Nigeria, ita missing nasu takeyi sosai. Galadima yace a'a ba yanzu ba, tashi tai tabar gaban lap-top d'in tana kuka, Galadima ya girgiza kai kawai. Yasha hirarsa da Abie sosai, saboda Alhamdullah jikinsa saidai godiyar ALLAH, dama ciwo keshiga farat d'aya, sauk'i kam sai a hankaki. Addu'a kuma takobin muminice ako yaushe. Bayan ya gama waya dasu Momma Sir Isa ya kirashi, ya tabbatar masa da komaifa is done, Dan ansami kowanne acikinsu, yanzu haka wasu sunma iso. Galadima yay murmushi yana shafa fuskarsa. Yace, “Nama canja shawara, zamu canja gidan da zamu ajiyesu da, yanzu akwai wani gida annan kusada plaza d'ina, nagama magana da Saleem komai yayi ready, Ameer duk yakaisu can, insha ALLAH ana idar da sallar Isha'i zan fito”. Sir Isa yace, hakan yayi, dan acikin yaran nasuma za'a iya samun munafukai, tunda duk sunsan gidan daza'a ajiyesun, yanzu kuwa shi Ameer kad'ai zaisan da wannan. Galadima ya kira Munaya, dama tun d'azun kiran nashi take jira, ta d'aga tana shigewa cikin bayin d'akinsu Dan kar wani yaji. Galadima yace, “haryanzu kukan?”. “a'a” ta fad'a cikin share hawaye. Yad'an murmusa kawai yana fad'in, “Akwai bak'in da sukazo gidanku?”. “A'a babu Wanda yazo, sai Siyama da Zarah”. Galadima yay murmushin gefen baki yana cigaba da danna lap-top, hasashensa yazama gaskiya kenan, gyaran murya yad'anyi kad'an yana fad'in, “kina jina?”. Munaya tace, “eh”. “Ki saka ido akan d'akin Abba, motsin kowa yazama akan idonki koda cikin matansane, ko yayyenki maza, Dan za'a iya yin amfani da kowa, inda da dama ma key d'in d'akin yazama a hannunki”. Munaya tayi d'an jimm alamar tunani, zuwa can tace, “babu damuwa, zan gwada hakan insha ALLAH, amma kunji labarin Abban?”. “Karki damu, insha ALLAH Abba zai dawo gida, addu'a muke buk'ata”. Munaya ta jinjina masa kai tamkar tana ganinsa, ta share hawayenta dake zubowa.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83