Chapter 62
Chapter 62
danake wasa da gefen siririn gyalen kaina. Cikin wata tattausar muryarsa mai cikeda nutsuwa da tarin k'asaita yace, “My Mata”. Kasa d'ago idanu nayi Na kallesa, saida Na amsa a sanyaye. Yad'an murmusa tareda saka hannunsa a ha6ata ya d'ago face d'ina. Kallo d'aya namasa Na risinar da idanuna, murmushi yayi mai sauti, yakuma sanyaya murya tamkar mai rad'a yana fad'in “Kin huce?”. Kamar bazance komaiba dai saina d'aga masa kai siraren hawaye na ziraromin a kumatu. Baice komaiba sai zubamin ido da yayi kusan seconds 30, ya sauke 6oyayyar ajiyar zuciya yana saka hannayensa biyu ya tallafe fuskata a cikin tafin hannun, ya gogemin hawayen da babban d'anyatsansa guda biyu. “A d'an kalleni mana my Queen, a kuma min murmushi ko kad'an na tabbabatar an huce d'in”. Yay maganar yana Raba idanu akan fuskarta. Yanda ya marairaice sai bansan lokacin da murmuahin ya kufceminba ma. Shima murmusawa yayi da d'an jan hancina, “Haba kokefa my heartbeat”. Hannu na saka na kare fuskata saboda naji kunya. Yawani lumshe idanu da sakin murmushin gefen baki, tareda maida kallonsa ga k'aramin agogon dake bisa dirowan gefen gadon. Time yaja Sosa, kallonsa ya maida ga Munaya data kasa kallonsa. “tashi kiyi shirin barci mu kwanta, ga dare na Neman rabawa”. Kallonsa nad'an sata ina janye idona. Nace, “To yaranfa?”. Bai amsaminba saida ya mik'e tsaye, “karki wani damu kanki, tunda kikaga Momma bata bamuba aikinsan ranar ta musamman Ce yau”. Ban sake maganaba danjin ya kamo wata tashar, na mik'e tsaye zuwa wardrobe na d'auka kayan barci. Duk abinda take idonsa a kanta, yana zaune a bakin gado yana binta da kallo. Ina juyowa muka had'a ido, nai azamar janye nawa, shikuma ya jehomin tambaya. “Wad'annan kayanfa?”. Kallon kayan nayi sannan Na kallesa da mamakin tambayar tasa, idonsa a kaina Dan haka Na janye nawa. Nace, “Zan sakane”. Baicemin k'alaba, sai mik'ewa da yay ya tako gareni cikeda izza da k'asaita, saina samu kaina da fad'uwar gaba, jinake tamkar nama zura da gudu. Kayan ya kar6a yana matsowa jikina, nad'anja baya amma saiya taro k'uguna da hannunsa yana kallon fuskata, cikin magana rad'a-rad'a daf da fuskata yace, “basu nake buk'atar ki sakaba yau, ke kad'anki nakeson gani babu wani shamaki a tsakaninmu”. Da mamaki na kallesa saiya d'agamin gira, nai azamar janye idona ina marairaice fuska. “ALLAH nidai bazan iyaba yalla6ai”. Kuma rank'wafowa yay kaina yana fad'in “Zaki iya my Queen, inhar da gaske kina son farin cikin mijinki, ni haka nake buk'atar ganin matata aduk lokacin kwanciya barci, ni kad'aina na isheki riga da bargo OK?”. Yanda ya k'are maganar saida tsigar jikina ta tashi, babu shiri na d'aga masa kai alamar amsawa, dan inhar nabari muka cigaba da kasancewa a haka wlhy za'a iya samun matsala. Harna fara tafiya ya rik'o hannuna, cak na tsaya batareda na juyoba. Yace, “nazo na tayaki wankan?”. Ai babu shiri na juyo ina kallonsa cikin waro idanu, saiya kashemin ido d'aya yana cizon lips. Zare hannuna nayi nai gaba da hanzari, saida naga na rufe k'ofar bayin na jingina sannan na sauke ajiyar zuciya, lallai naga takaina da Galadima, dama haka yake? Sumi-sumi dashi, idan ka gansa saika d'auka bazai iya ko kallon macenba, amma humm. Shima tana shigewa ya murmusa yana shafa sajensa zuwa gemu, takawa yay zuwa gaban gadon ya zauna, zuciyarsa na kuma tsunduma a k'aunar matarsa da ayyukanta, waya ya d'auka yana danne-danne, kusan wasu mintuna sannan ya mik'e yana ajiye wayar, kayan jikinsa ya cire, dagashi sai boxer ya haye gadon tareda jan bargo ya lullu6e jikinsa yana kwanciya, luf yayi tamkar mai barci. Sosai na nutsu na gyara kowane lungu da sak'o na jikina, nasha turarrurukansa dake bathroom d'in, kunyar fita nakeyi da towel wlhy, Dan haka naja rigar wankansa na saka, ahankali na bud'e k'ofar, saida na fara lek'a kaina na hangoshi kwance akan gado da alama ma yayi barci. Ajiyar zuciya na sauke kafin na ida fita cikin sand'a. Duk abinda takeyi Galadima na kallonta, ya had'iye dariyar dake taso masa da k'yar yana kuma yin luf. Cikin tafiyar sand'ar tazo har gaban madubi, bai motsaba harta gama shafe-shafen turarenta da lips gloss, ta tako a hankali gaban gadon zata d'auke wayarsa data kusa fad'owa k'asa, wadda ya ajiye dama matsayin tarko, yasan inhar tagani bazata wuce ta bartaba saitayi yunk'urin d'aukewa. Caraf kuwa ya damk'e hannunta, gabanane ya fad'i, ina k'ok'arin ja da baya ya kamo igiyar rigar wankan danaima d'aurin zarge, aikam lokaci d'aya ta warware, nai saurin rik'ewa Dan karta bud'e, amma ina saiya jawo igiyar ya fisgoni na fad'o jikinsa, bargon ya d'aga ya turani ciki yana murmushi mai sauti. Ya zare wayarsa dake cikin hannuna yana fad'in, “Dukfa wayon amarya.....” Shiru nayi nakasa magana danni tsoronsa ma kuma mamayeni yakeyi, ban ankaraba naji yana zare bathrobo d'in. Cikin marairaicewa nace, “please yalla6ai kayi hak'uri kabarni da rigarnan akwai sanyi fa......” Yatsansa d'aya ya d'ora saman la66ana, yaymin alamar nayi shiru, banida za6in daya wuce bin umarninsa. Yace, “Nifa ba komai zanyiba, bashina da akaci za'a biyani, sanyi kuma nine bargonki ai”. “Ni yaushe naci bashinka?”. Nai maganar a raunane”. “Uhyim, in maye yaci ya manta ai maid'a baya mantawa, kedai kawai ki mik'a wuya, wahalar da aka bani yau duk saina fanshe kayana”. Maganar danayi yunk'urinyi bansami lasisin kammalata ba ai, sai a cikin b.....🤭 (😝ba ruwana nayi nan⛹🏻♀). ******************** Yaudai kam Na tabbatar nashiga hannun manya, babu ga6ata da bata ciwo, nayi ligif saboda jikagata, baiyi k'aryaba kam, ya fanshe haushinsa harda gyara, da asubahi saida taimakon ruwan zafi nasami k'arfin jikina, Dan saida nagasa jikin, ga6o6ina suka d'an mik'e, bai fita masallaci ba, shiya jamu jam'i. Sosai barci ya d'inga cin idanuna, muna idar da sallar Na zame a wajen Na kwanta, baice dani komaiba, saima Qur'an daya d'auka yafara karatu cikeda nutsuwa da kwarewa, tun ina saurarensa sama-sama har barci mai nauyi yay a won gaba dani. Bai dad'e yana karatunba ya ajiye Qur'an d'in, Dan shima barcinne taf idonsa, kallon Munaya dake k'udundune cikin hijjaf yayi, yad'an murmusa yana shafa fuskarta, shikansa yasan jiya ya wahal da ita, amma soyayyartace duk ta jawo hakan, ya duk'a yana sumbatar goshinta da kumatunta, mik'ewa yay ya cire jallabiyar jikinsa sannan ya dawo inda take, itama cikin dabara ya cire mata hijjab d'in sannan ya d'auketa cak zuwa gadon. Tad'an bud'e ido ta kallesa ta maida ta lumshe. Murmushi yay da sake sumbatar la66anta sanan yaja musu bargo, ya rungume yalla6iyarsa suka sake komawa duniyar barci.😘👌🏻 ★★★★★ Tun Momma Na zuba idon sakkowarsu har abin yafara bata mamaki, gasu Abdurrahman sun farka tun d'azun, sai faman banka musu ruwan zam-zam mai had'eda Zuma take dasunyi kuka, da alama yunwa sukeji, amma takula iyayen nasuma sun manta dasu. Aunty Mimi dai nata k'umshe dariya, har sukayi breakfast babu su munaya babu labarinsu, yaranma sun kuma komawa barcin dole. Barcin yaran baiyi wani nisaba suka kuma farkawa da kuka, Dan yunwa ta hanasu barcinma. Momma tace Samha tahau saman taga idan sun tashi. Da to ta amsa tana hawa saman. Amma saita iske ko ina tsitt, babu alamar motsin mutum. Dawowa tayi ta sanarma Momma basu tashiba, ga Abdurraheem harwata shid'ewa yake saboda kuka, shi dama baida jimirin yunwa, sauran y'an uwansa sunfiahi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83