Chapter 68
Chapter 68
A take Momma ta juya gareta, dan ko a mafarki bazata manta mai wannan muryarba, batareda tunanin komaiba ta rungumeta. Yayinda shima takawa ya rungume Abie daga can. Tun a wannan daren labari yafara karad'e masarautar, wasu kan basu aminceba kwata-kwata, burin kowa gari ya waye yayi kallon zahiri ba jita-jita ba. Dole matar mai martaba ta koma sashenta, dan mai martaba yace Abie a sashensa zai kwana, jiyake idan ya barsa zuwa wani sashe tamkar da safe zai wayi gari yaga ba hakaba. Itama Momma a sashen mama Fulani ta kwana tilas, yayi da mukuma muka nufi namu da yasha gyara ko ina yake need tamkar muna k'asar. Yau dai kam na murzu wajen Galadima, acewarsa murnar sallah ce, dukda gajiyar tafiya darashin samun isashen barcin da muka tara a Saudia bai d'agan k'afaba, a cewarsa yamayi k'ok'ari, kwana nawa. *_WASHE GARI_* A Washe gari antashi da farin ciki guda biyu a masarautar gagara badau, Murnar Salla da dawowar Abie. Dan zuwa safiya kam tabbataccen labari daga bakin sank'ira ya isa kunnen kowa, harma da k'yak'yk'yawan albishir na halattar sallar idi tareda Abie. Kafin kace mi labari yafara fita wajen masarautar, su papi ma tun a Daren Galadima ya kirasu da wayar Sauban dake hannunsa. Batareda sanin ya akayiba saiga magana tafara shiga kunnuwan jama'ar gari da y'an jarida, wasu gidajen TV Dana redio suka fara sanar da wannan zance dawasu ke k'arya tawa kansu tsaye................✍🏻 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏼 [8/22, 8:36 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* *_💡HASKE WRITERS ASSO...._* *_♦RAINA KAMA...!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_BOOK 3_* 👉🏻2⃣8⃣ .................Har yamma Galadima bai dawo gidanba, abincin ranama da aka ajiye masa sai d'aukeshi akayi, sainaji inajin tausayinsa, dan nasan yanacan ba zaune waje d'ayaba, yawan harkoki dayakeyi kansa kullum yake yawo tamkar wata motar haya, shidai kullum burinsa ya iya d'aukar nauyin ahalinsa, bai yarda zama rago ko jira daga waniba koda ace papi ne, ya yarda yasha wahalar nema amma ta gumin halak, sa6anin matasanmu da kullum burinsu nakan gwamnati ko alhajin anguwarsu ko d'an siyasa, ko alhajin da yafi kowa arzik'i a danginsu. Akwai wata kalma da Galadima yata6a fad'ama sauban Wanda akulum Na tunata tana k'ayatar dani. Lokacin inada tsohon cikinsu Amaturrahman, da yawan cin abincinnan Na masifa, aranar jikin Abie yad'an motsa, sai yakasance nikad'ai aka bari a gida sai hadiman gidan, cikin barci yunwa ta addabeni, hakan yasani farkawar dole Na sakko k'asa da k'yar, kitchen Na shiga nasami madara Na d'umama kafin kuku yad'an girkamin wani Abu, fitowata daga kitchen d'in keda wuya sai Galadima da Sauban suka shigo, da alama ya tuk'osane, dan idan yana cikin damuwar tashin ciwon Abie Momma hanashi driving takeyi. Da mamaki Sauban ya kalleni da cup a hannu yana fad'in “Yanzu nan Aunty duk hadiman gidannan saikin shiga kitchen da kanki a wannan halin? Aiko yau saisun gane kuransu”. Ya tafi fuuuu cikin fushi saina dakatar dashi ina murmushi. Nace, “A'a Yaa Sauban, kabarsu please, nice ban sasunba nayi da kaina, amma aiga shican nasaka kuku wani aikin”. Galadima dake zaune saman kujera ya d'aura k'afa d'aya kan d'aya idonsa a lumshe tamkar baisan mi mukeyibama ya bud'e baki cikeda k'asaitar nan tasa yana fad'in, “Ai duk Wanda ya dogara da k'arfin wani to lallai nasa na cikin jerin k'arewa a sahun marasa amfani, dan zai dawwama cikin bibiyar samu daga waninsa shikuma bai amfanu datasa fik'irarba, kazama mai k'arfin zuciyar gina kai ba zaman jingina da bangon waniba”. Yana gama fad'ar haka ya tashi ya haye sama, dagani har Sauban da kallo kawai muka bishi, kowa na fassara zancensa dalla-dalla, ni abinda na fahimta kai tsaye bada Sauban d'in yakeba, akwai abinda yafaru daga can inda suka fito, amma saiya za6i mu yamana sharhi bisa dalilin dashi yabarma kansa Sani. (ALLAH dai ya ganar da matasanmu domin tashi su nemi na Kansu ta hanya mai k'yau basu cigaba da dogaro a bangon wasuba.👏🏻😢). Tun d'azun yake tsaye akanta amma bata saniba, ta Lula duniyar tunani mai zurfi, ga Abdurrahman dake gefenta yanata mutsu-mutsu da k'ananun kuka amma batama jishiba. Agabanta yay wani durk'uso mai birgewa, yakai fuskarsa daf da tata yana hura mata iska a saman ido zuwa hanci. Wata sassanyar ajiyar zuciya na sauke tareda dawowa hayyacina cikin zabura, yay azamar damk'e hannuna da fad'in “My Mata!?”. Ajiyar zuciya na sauke tareda dai-daita dan fahimtar shine, na zuba masa idanu cikin mamaki nace, “Yaushe ka shigo?”. Murmusawa yayi sannan yamik'e daga durk'uson dayay agabana, batareda ya bani amsaba ya fara k'ok'arin cire farar rigar suit d'insa. Mik'ewa nayi na taimaka masa, sannan nadawo gabansa na warware tia.. 'Din da bottoms d'in pink d'in rigarsa ta ciki. Sai wani faman lumshe idanu yake da bud'esu akaina, bansan miyake tunaniba. Ina cire bottom d'in k'arshe na rigar ya rik'e hannuna, idanu na d'ago na kallesa, ya sakarmin wani k'asaitaccen murmushi yana matsoni jikinsa sosai, a saman la66a ya furta “Kinyi k'yau sosai, amma mikike tunani haka?”. Da mamaki na kalli kaina, sanye nake doguwar rigar shadda milk color, anmata simple aiki da brown d'in zare, an k'awatashi da stones, Wanda sune suka fidda ainahin k'yawun d'inkin, sai siririyar sark'a data kwanta a wuyana d'as, nayi d'aurin Maryam babangida daya kuma fidda ainahin suffata ta bahaushiyar asali mai rik'o da al'ada. Yanda nake bin jikina da kallo haka Galadima kebi shima da idanunsa, na maida kallona ga face d'inshi dake kadaran kadahan, bai d'aureba kuma babu walwala sosai tare dashi. Gira d'aya ya d'agemin sai kuma yad'an ta6e baki yanajan hancina da had'e yatsunsa biyu na k'arshe👌🏻alamar komai yaji. Nad'an murmusa ina k'ok'arin barin wajen dan naga alamar miskilawan suna kusa. Ruwa naje na had'a masa, na fito ina goge hannuna da towel. Durk'ushe na iskeshi gaban Abdurraheem da cup d'in ruwan dana ajiye danshi a hannunsa. Ya d'ago yana kallona dad'an murmushi a face d'insa, “kinsan minake gani a jikin Abdurraheem kuwa?”. Kaina na girgiza masa alamar a'a. Kallonsa ya maida ga yaran yana cigaba da murmushinsa. Yace, “Kamannin Abie”. Takowa nayi Inda suke Nima Ina murmushi mai sauti da fad'in, “Nadad'e da wannan tunanin a raina, saidai nabarma zuciyatane har sai randa zan gansu a waje d'aya, Ashe kaima kana lura?”. Wata y'ar dariya yayi, wadda tafi kud'i tsada awajensa. Yace, “My Heartbeat ALLAH kin iya haihuwa”. Ba k'aramar dariya maganarsa tabaniba, aiko nashiga k'yalk'yalawa. Shiko ya shagala da kallonta saboda birgeshi da dariyar tata tayi, burinsa dama yaganta cikin farinciki. Bayan na tsagaita da dariyar na kallesa Ina d'aga kai da kashe masa ido alamar kallonfa?. Mik'ewa yay tsaye ya dawo inda nake tareda rank'wafowa kaina yana dafa hannayensa biyu asaman gadon gefe da gefena. Kusancin namu yasakani d'anyin baya kad'an ina kallon cikin idonsa, yakuma matsowa, na matsa, yakuma again, Nina still na matsa, saida na haye gadon sosai shima yay balance yanda yake buk'ata sannan ya kwanto gefena kusan Rabin jikinsa a nawa, har lokacin idonsa na sark'e da nawa. Galadima yay bala'in Sanin sirrin kallo, inhar ya sark'e idanunsa da nawa duk wani hope d'ina nemansa nakeyi na rasa, yatsansa kawai naji saman la66ana yana zagayawa ahankali, santsin hannunsa Dana lips gloss d'in Dana sanya sunayin kamar susa, kasa jurewa nayi na lumshe idanuna a hankali. Galadima ya murmusa da bud'e baki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83