Chapter 35
Chapter 35
zuciya ta sauke tabashi hak'uri kawai, dan bata buk'atar jan maganar. Yace, “kunje asibitin?”. Munaya tace, “An cire mata ai, babu wata matsala tunda bai ta6a cikiba”. Ca yay ta d'auka hoton wajen ta turo masa yagani, kamar tace bazatayiba sai kawai ta cire wayar ta katse kiran, hoton wajen ta d'auka ta tura masa”. Tausayin yarinya ya kamashi ganin yanda wajen yay cinye sosai, Yakuma kiran Munaya yana jaddada mata karta sake akuma sakamata wani d'an kunne. To kawai ta amsa masa dashi dan a zauna lafiya. ..............................★ Tun daga ranar Munaya bata sake jin Galadima ba, saboda yayi busy da yawa akan shirye-shiryen shari'ar dake gabansu, dan fatanshi wannan zaman yazama zama Na k'arshe insha ALLAH. Alhmdllh jikin Abba anata samun haske sosai, dan sauk'i yana samuwa iya gwargwadon iko. *_RANAR DA ZA'A KOMA KOTU_*................✍🏻 Hummm😬 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭👏🏻_* [8/3, 4:45 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* *_💡HASKE WRITERS ASSO...._* *_♦RAINA KAMA...!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_BOOK 3_* 👉🏻1⃣8⃣ .................Yauma dai kotun ba'a cewa komai, wad'anda ma basuzo zaman farkoba yau sunzo, Dan su sir Isa duk suna wajen da muk'arabansa, hakama tawagarsu Tanderu, Dan suma lauyansu a cewarsa yau yazo da sabon shiri, ranarma an mamesa ne kawai. Galadima yagama shirinsa tsaf cikin wani lallausan yadi sky blue dayasha d'inkin boda, Dan rigar iyakarta Rabin cinyarsa, kayan sunmasa k'yau matuk'a, danya fito ainahinsa Na jinin Hausa Fulani, ya Mirza hularsa sky blue itama, fuskarnan tayi fayau Dan hardasu gyaran fuska yayi abinsa, danma ya tabbatarma mak'iya yana cikin farinciki fiye da zatonsu, yana cikin saka sock's Nuren ya lek'o yana fad'in “Brother ka hanzartafa mun makara”. “umhum” kawai yace masa yacigaba da saka kayansa a tsanake kamar yanda yafara, danshi komai saurin dazaiyi akan Abu to anutse zaiyi abinnan, ganin haka sai kawai Nuren ya ida shigowa, ya durk'usa gabansa yana kama k'afar daya sakama sock's d'in ya saka masa takalmi. Baki Galadima ya tsa6e yana cewa, “kaifa shegen gaggawane dakai wlhy, ni bansan INA kuka kwaso halinnanba, haka Momma da Aunty Mimi suke, komai kunfison mutum yanayi kamar wani mazari”. Nuren ya sanya dariya yana saka masa d'aya takalmin, yace, “to sokake muke Abu kamar marasa laka a jiki? Munaya dai kam tana fama...” Hararsa yayi, hakanne ya hana Nuren k'arasawa, Galadima daya wani tsaresa da ido yace, “Tana fama da k'aniyarka”. Nuren ya mik'e yana fad'in “oho maka dai, mu ka fito su sarkin mota tuni sukazo”. Mik'ewa yay ya d'auki turarensa Na kullum a bag d'in daya had'o kaya ya fesa, k'amshin ya gauraye ko ina, waya d'aya ya zura a aljihu ya fito. Su Ahakam duk shagala sukayi da kallonsa, a ransu suna matuk'ar yaba tsarinsa, komai nasa abin birgewane, kamar yanda ya saba haka yabasu hannu da kansa sukayi musabaha dukda suna nok'ewa alamar jin kunya da girmamawa a gareshi, shikam babu ruwansa, inhar bakasan halinsa bane dolene tashin farko ka jefeshi da kalmar girman kai. Su Farhat ma suka gaisheshi cikin risinawa, wani miskilin murmushi yamusu yana d'aga musu hannu kawai, ya kalli Saleem tare da masa nuni yabama kowa kayansa. Saleem ya amsa da cewar “ok boss”. Bag d'in da wayoyinsu ke ciki ya d'akko, amma sai sukace sukam ya barsu, Dan inhar ba'a yanke hukunci ba zasu dawo su cigaba da zama dasu, Dan zama da Galadima akwai dad'i, kuma ko an yanke hukuncima masarauta zasu bishi. Shi dariyama abin ya bashi, hakanne yasakashi bubbuga kafad'ar Yassar dake kusa dashi yana sakin murmushin da har hakwaransa ke bayyana, ya wucesu yana sauka daga benen cikin takunsa Na birgewa. Suma duk binsa sukayi a baya, komai nasa Saleem ya tattaroshi, dan bazai sake dawowa gidanba koda ba'a yanke hukunci ba kuwa. Harun dai anyi laushi matuk'a, dan maganarma yanzu ba iyayin mai k'arfi yakeba, saboda saiya gadama yakecin abinci, babu kuma mai sakashi dole yaci. Cikar k'ofar gidan tabama Galadima mamaki matuk'a, yakuma d'aure fuska tamkar bai ta6a dariya ba, musamman yanda duk aka zubo masa ido, a Bayama an kallesa balle yanzu da yayi abun kallon, y'an sanda da dogaransa da suka zo d'aukarsa tun d'azun sai k'ok'arin hana y'an jarida dakeson zuwa ga Galadima sukeyi, amma suna k'ok'arin kutsowa. Tsaye Galadima yayi ya zuba dukkan hannayensa a aljihu, saida yaga shigarsu Rahma mota dasu alhaji darma sannan yanufi inda sarkin mota ya bud'e masa, y'an jaridar daketa masa tambaya ko kallo basu isheshiba ya shige mota abinsa, yayinda Muftahu ya zauna gefensa, Nuren Na a gaba. Mortar y'an sanda Na a gabansu da Bayansu, a haka akayi tafiyar. Sauran y'an sandan da aka bari suka shiga gidan domin d'akko gawar Ahmad, amma sun bincika lungu da sak'o babuma alamar an cutar da wani, sai harbi guda d'aya daya shiga jikin bango, (shima Wanda Galadima yayine sanda ya tsoratasu da cewar ya kashe Ahmad), basu samu komaiba dazai nuna Galadima d'an ta'addane, sai suka fito suna kulle gidan, amma basu tafiba harsai kotu tabada damar hakan. ............................★ Sun Isa Court d'in, inda Galadima da Nuren da Muftahu ne kawai suka Shiga, yaran dasu Alhaji Darma an kaisu wani d'akine kusada wajen. Takun takalman Galadima dake tafiya cikin tsantsar izza da nuna jinin mulki ya saka dukkan jama'ar kotun zuba masa idanu, shikam ya had'e fuska tamkar hadarin gabas Na tsakkiyar ogusta dabaya d'aga k'afar zubar ruwa, kallon kowa bayayi, gashi ya toshe idanu da Google eyeglasses d'insa da babu mai kallon kwayar idonsa. A kujerar farko irin wadda su Alhaji Mamman ke zaune shima aka nuna masa shida Nuren da Muftahu. Wani zama yayi dake tabbatarma da mak'iya shid'infa sarakine, gaba da baya kuma. Hakan ya k'ona zuciyar su Alhaji balala matuk'a, amma babu yanda zasuyi. Zaman Galadima babu jimawa saiga alk'ali ya fito, kowa ya mik'e domin girmamawa, saida ya zauna sannan duk aka zauna. Kotun tayi shiru kowa ya zubama alk'ali idanu, yagama dube-duben ta kardun gabansa sannan ya d'ago ido yana kallon jama'a, yace, “Yau shari'ar zata tafine kai tsaye batare da shigar lauyoyi Na kowanne 6angare a tsakiyaba, Dan haka muna buk'atar Wanda yay k'ara, da wad'anda ake k'ara a gaban kotu”. A hargitse su alhaji Sageer suke kallon kallo, hakama lauyansu dukya shiga rud'ani, saboda mugun shirin dayayo yau akumace ba haka za'ayiba. Shikam Galadima wani mugun murmushi yayi yana kallonsu Alhaji mansur d'in damusu wata inkiya da yatsu biyu alamar a kafta, sannan ya mik'e. Dole suma duk suka mik'e inda aka buk'aci ganinsu, dukda wajen yamusu kad'anma. Alk'ali ya kalli galadima. Yace, “kaine Wanda kai k'ara, Dan haka munason jin shin minene mafarin wannan takun sak'a kai tsaye?”. Murmushi galadima yayi, ya cire eyeglasses d'in idonsa ya saka cikin aljihu, tareda zaro handkerchief ya goge fuskarsa, yasa hannayensa biyu ya dafe katakon gabansa yana jifan waziri mahaifin Harun dawani mugun kallon daya hargitsa y'an cikinsa da tunaninsa, hakanne yasaka mutane kallon waziri suma, duk sai yaji ya muzanta. Galadima ya ta6e baki yana janye idonsa dad'an cije lips, cikin k'asaitacciyar muryarsa yace, “ya mai shari'a labarina mai tsawone kwarai da gaske, sannan cike yake da abubuwan ban mamaki da takaici masu tarin hargitsi, duk da nasan kowa yasan sunana amma zan sake maimaitawa, sunana Muhammad Sameer Saifuddin Abubakar, gidan sarauta Na fito, mahaifina shine tsohon Sarki da k'addarar ciwo ta kwantar tsawon
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83