Chapter 53
Chapter 53
daya hana kowa sukuni, sai a waya muka gaisa dashi, bayan Azhur aka kaimasa yaransa dai, sunsha gayu cikin kayan sanyi. Bayan sallar la'asar mukad'an fito ni da sauran y'an uwana domin mud'ansha iska dai, saidai kowa a cikin kayan sanyi yake, ina goye da Meenal, yayinda suma sauran yaran su Badeera duk suka goyasu. Mun shiga sashen matan sarki mun gaishesu mun fito muka had'u da su Galadima sun fito daga masaukinsu zasu shiga mota, da alama dai fita zasuyi. Ido muka had'a dashi ya sakarmin Murmushi da d'agemin gira d'aya. Nima murmushin namasa ina juya idanu. Da yake d'an nesa damu suke, basu zoba muma bamu k'arasaba, suka shiga motar da aka bud'e musu. Har suka fice inabin motar da kallo. ******** Tarbar da Galadima ya samu ta girma da mutuntawa tamasa dad'i ainun, Dan shima har wata sarauta suka bashi, sun Nuna farincikinsu Na had'a jini da babbar masarauta irintasu Galadima, shima kuma yayi farincikin kasancewarsu cikin yankin ahalin matarsa, shikam bashida abun fad'a sai godiya. Washe gari Sarki da Kansa yasa aka kirani, naje har turakarsa Na samesa, nasiha yaymin mai ratsa jiki, ya k'ara nunamin Girman daraja da Kimar masarautar su Galadima dayake gani, dukda basu had'a k'asa d'ayaba, inhar Na aikata k'yak'yk'yawa martabarsu da darajarsu Na kare, domin su ahalinane, kuma dole ace daga tsatsonsu Na fito, Na kare musu mutuncinsu, shima bada dad'ewaba zai shigo Nigeria insha ALLAH. Cikin girmamawa da share hawaye nace, “Insha ALLAH bazan baku kunyaba, zan zama d'iya tagari mai ado da tarbiyyar ahalinta Na kowanne 6angare,, da izinin ALLAH saikunyi alfahari dani”. “ALLAH yayi miki albarka, Yakuma tsareku da dukkannin sharri keda y'an uwanki, yabaku zaman lafiya Na har abadan a gidajen aurenku”. Nace, “Amin Abba mun gode sosai, ALLAH ya k'ara girma”. A gurguje please🤗 ******************* Kwanakin Galadima uku a masarautar muka fara shirin tafiya, dan mura ta kama shi ram, gashi bata masa da sauk'i, a lokacin mu kwanakinmu 10, kowa yana cike da kewar tafiyarmu, jisuke kamar karmu tafi, mu kanmu a kewar rabuwa dasu muke ji sosai, dan Sabone maiban mamaki da shak'uwa ta shiga tsakaninmu, ba k'aramar hidima suka manaba, lamarin harma yayi yawa, sukace suma insha ALLAH suna tafe garemu nan kusa. Mussamman da kowa ya fahimci alak'a mai k'arfi dake tsakanin Yareema Issifu da Ayusher, wadda kowa yake cikin tsantsar farinciki da fatan ALLAH ya tabbatar da wannan had'i. Yanzu kam tafiyar ta canja salo, dan Munubiya da Yaa Marwan, ni da Galadima. Innarmu da Abba, mama Rabi'a da abbansu Ayusher, Feena da Ayusher, innaro, laraba, Yaa Fadeel dasu Aryaan aka had'asu a babbar mota guda d'aya (gwauraye kenan🤭🤣). Tunda Na shigo motar k'amshin turarensa ya faramin sallama, sanye yake cikin milk d'in shadda datasha ainahin aikin masu sarauta harda hula, yayi k'yau, Dan yau a sarakinsa ya fito, muka kalli juna kowa yay murmushi, saida Na zauna sosai su Deejama dake rik'e da yaran suka mik'ominsu, ganin zasumin yawa yad'an matso ya d'auki Abdurraheem da Abadurrahman, idona dukya cika da k'walla, haka suma su Maryamu hawaye sukeyi, haka suka rufemu suna d'aga mana hannu. Saida motar ta fara tafiya sannan hawayena suka sami damar zubowa. Galadima da tun shigowata idonsa Na kaina yay murmushin gefen baki, tissue ya Ciro a bayanmu ya matso jikina sosai da d'ago fuskata. Kallonsa nayi, idanunmu suka sark'e cikin Na juna, ya lumshe nasa dake cike da barci da mura wadda ta k'ara musu girma da canja kalarsu jaa kad'an yana girgizamin kai alamar nabar kuka. Bance komaiba, sai kuma matso hawayen da nayi, yasaka tissue d'in ya gogemin, sannan ya sumbaci saman la66ana kad'an yana jingina kaina da kafad'arsa. Shiru nayi ina sauke ajiyar zuciya kad'an-kad'an, yayinda shikuma yake d'an shafa gefen kafad'ata daya d'oro hannunsa wajen, saida nasami nutsuwa sannan Na d'ago, kallona yayi muka had'a ido, cikin salon rashin son yayi magana ya kad'a kwayar idonsa alamar yadai?. Da hannu Na nuna masa yaran nima, dukda bai fahimci minake nufiba baice komaiba. Hulunan su Amaturrahman Na fiddo a handbag zan saka musu, dan sauri bai barni nayi hakanba dazamu fito, anafa fitowa daga sallar Asubahi akaita mufito-mufito, kuma duk Yaa marwan ne da wannan azalzalar. Amaturrahman dake jikina Na sakamawa, shima gogan da mura taima murus ya kar6a yasakama mazan yana magana tamkar an masa tilas, “kai garinnan da dad'in zama da wahala, wannan sanyin nikam shiya hanani sukuni”. Dariyar data tahomin Na had'iye da k'yar ina fad'in “Ai sanyin kam babu sauk'i, sunce idan zafima yazo yashin yaji rana haka suke azabtuwa, garama sanyin, kaji kuwa muryarka fa ta canja gaba d'aya”. Murmushi yayi ya jingina kansa dake masa ciwo jikin seat batareda ya amsaminba. Nima sai ban sake magana ba, Na nad'e yaran sosai a showal dukda glasses d'in duk a rufema suke, driver dai nata tuk'insa, ni idan son samunema Na kwanta, Dan barci nakeji sosai, jiya bamuyi wani barcin kirkiba anata hirar bankwana, muna kwanciya babu dad'ewa innaro tafara tashinmu mu shirya. Seat d'in gaba Na kalla, tunanin maida yaran can yazomin, nakuwa d'aukesu d'ai-d'ai ina maidawa, tunda suna cikin kayan sanyi, kuma barcinsu sukesha, nima ai saina huta ko. Zamewa nayi Na kwanta tareda d'ora kaina a cinyarsa, ido kad'an ya bud'e ya kalleni da mamaki, “Ina yaran?” ya fad'a yana kallona. Da hannu Na nuna masa gaban motar, “Amma ai zasu takura a can?”. A shagwa6e nace, “ALLAH bazasu takuraba, barci nakeji har kaina yafara ciwo”. Kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru, Dan bayason yawan maganar saboda kansa ciwo yake sosai. Nima ban sake cewa komaiba Na gyara kwanciyata ina lumshe ido, hannunsa ya d'ora a jikina daganan motar ta d'auki shiru, Dan barci tuni yayi awon gaba dani, shima a hakan barcin ya kwasheshi. Bamu kuma sanin halin da ake cikiba saida tafiya tai nisa sosai, yara suka farka suna k'ananun kuka, shine ya fara farkawa, ya bud'e ido a hankali bakinsa d'auke da addu'a, agogon hannunsa yafara kallo, sannan ya maida kaina danabi dukna kanainayeshi, yad'an murmusa yana janye gyalen jallabiyar jikina daya rufe rabin fuskata, barcina nake hankali kwance, shi saima yaga Na k'ara k'yau a hakan. Kukan yaran daya fara k'arfine ya sakashi dawowa hayyacinsa, ya shafa fuskarta a hankali yana kiran sunanta. Munaya batada nauyin barci dama, idanma aka cika surutu a kusa da ita takan farka, tad'anyi mik'a tana bud'e ido, hannunsa nakan fuskata ya zubamin idanu, ni saima kunya ta kamani, naja gyalen Na rufe ina tashi zaune. Murmushi yad'anyi yana fad'in “Duk kin samin ciwon jiki”. Fuskata Na bud'e ina tura baki kad'an da kallon kaina, ina naga nauyin dazan saka masa ciwon jikin?. Fahimtar abinda nakeyi dayayne ya sashi cewa, “kina kokwanto ne?”. Nace, “sosaima”. Nai maganar ina d'akko yaran. Yanzuma kar6ar biyu yayi, Na dungure kan Abadurrahman ina fad'in, “kun ishi mutane da k'ananun kuka, nima yunwar nakeji ai”. Galadima dake kallonmu cikeda sha'awa yay murmushi mai sauti dahar ya bayyana hak'oransa a waje, amma baice komaiba. A nutse Na shayar dasu su duka d'aya bayan d'aya. Munzo cikin babban wani gari Galadima ya Umarci driver da cewar yasama mana wajen abinci mai k'yau, Dan karsu Aiyaan suji yunwa. Cikeda girmamawa driver ya amsa masa. Abinka da driver manya, dukkan wani wajen girma sun sanshi,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83