Chapter 72
Chapter 72
insha ALLAH bazasuyi kukaba, Dan saida cikinsu yay taf sannan Na fito. Naji dad'in iskesu sunci rabin aikin, to kusan su 15 kowa da abinda yakeyi. Dannan nasaka hannu nima wajenyin abinda yakamata ace ni nayi d'in, Dan Sarkin Mota yakawomin sak'ona tuni. Sannan ankawo sauran kayan daga sashen mama Fulani. 8:00am dai-dai Galadima ya shigo sashen, saboda yazo yay shirin massalaci, mamaki ya kamashi jin k'amshi ya baje ko'ina, shidai yasan bai tanadi komai d'aya danganci abincin salla ba. Yana cikin tunanin Sauban ya shigo d'auke da k'atuwar ledar kayanda zai saka, Wanda tun muna India yabada umarnin a dink'a masa su. Tare suka shiga sashensa da tunanin ko inacan, dukda yasan bazanbar y'an aiki akan girkiba, Dan yakula inada son komai naima kaina musamman girki. Babu abinda ke tashi sai k'amshi mai dad'i anan d'inma, ga ko ina yayi k'al gwanin sha'awa da birgewa, saidai kuma tsit alamun babu kowa. Sauban ya Shiga bedroom d'insa da kayan shima yana biye dashi. Cikin sigar tambaya Galadima yace, “to ina take itada yaran?”. K'aramar dariya Sauban yayi, yace, “Yaa Sam kasan halin auntyn tamu dai, Na tabbatar k'amshin girkinnan daga sirrin iyawartane, kaga kenan tana kitchen ”. Hararsa Galadima yayi, Sauban ya rufe baki Dan tuna ta6argazar da yayi. Ina cikin aikin Sauban ya shigo, bayin duk suka zube suna gaisheshi, da farko nama zata ko Galadima ne, saida Na waigo naga Sauban. Bayan ya d'aga musu hannu dabasu izinin tashi ya kalleni yana fad'in “Aunty gimbiya kinsani jin yunwa mai yawa da wannan k'amshin girkin naki”. Murmushi nayi kawai ina wanke hannayena, nace “ALLAH Yaa Sauban akwaika da tsokana, ya gajiya”. “Ai tabi gado wlhy, tare muka shigo da Yaa Sam fa”. Nace, “Ok". Coffee Na had'a masa a k'aramin filas Na d'ora a tire mai k'yau da mug daduk abinda zai iya buk'ata. Kar6a Yaa Sauban zaiyi nace, “A'a kabarsa Na hutar dake nikam”. Yay murmushi, “shikenan Aunty, inagafa nima zuwa zanyi Na shirya yau idin Na musamman ne ga jama'ar masarautar gagara badau”. “Gaskiyane Yaa Sauban, ALLAH yasa yau asamo mana amaryarmu”. Dariya yayi yana yunk'urin fita, “lallaima Aunty d'an k'araminnan dani wazai ban y'arsa?”. Ban samu bashi amsaba ya fice, Nima sashen Galadima Na Shiga INA murmushi. Babu kowa a falon, Dan haka Na wuce bedroom d'insa. Sallama nayi kawai Na shige. A bakin gado Na iskeshi zaune d'aure da towel, da alama wanka zai Shiga. Murmushi mukaima juna. nace, “Afuwan my King, aiki ya d'auke hankalina bansan ka shigoba”. Murmushi ya kumayi yana wani lumshe ido, Na ajiye tiren saman k'arim copy table d'in gabansa sannan Na zauna kusa dashi Na kwantar da kaina gefen kafad'arsa bayan Na sumbaci damtsen hannunsa”. Shima saiya karkato fuskarsa gareni ya shafa tawa fuskar da tattausan hannunsa, cikin magana rad'a-rad'a yace, “miya kaiki aiki keda ke tare da gajiya?”. Idanuna na d'ago na kallesa ina murmushi, nace, “my king ai yakamata ace anyi abincin salla a sashen Galadima, wannanfa shine karon farko da zakayi bikin salla da matarka a masarautar nan, bai kamata ace anyishi babu wasu alamuba ai OK?”. Yanda nai maganar da kashe ido d'aya saida tsigar jikinsa ta tashi, yad'an lumshe ido da sumbatar goshina, sannan ya rad'amin “ALLAH yay miki albarka” acikin kunne. A saman la66a na amsa da “Amin”. Ya tambayeni yara nace, “suna d'akina, maybe ma sunyi barci. Bamu tsaya 6ata lokaciba muka Shiga na taimaka masa da wanka, sannan muka fito nahau shiryashi, dukda lokaci yaja a nutse nake masa komai, danshi ma'abocin son komai a nutsene, bayason gaggawa ko yawan sauri koda a magana ne kuwa. Inamasa shiri yana shan coffee, kaga d'an gatan Munaya.😂 Tsaf na shiryashi cikin farar shadda daduk salla yakanyi amfani da ita wajen idi, nakawo babbar riga na saka masa sannan na fesheshi da turare, ajiye mug d'in hannunsa yayi yana d'aukar hularsa zanna bukar daketa maik'o yay mata kari ya kafa bisa kansa yana dai-dai tawa. Alk'yabbar dazai sa nagama feshewa da turare sannan na matsa ina kwantar masa da sajensa dayasha gyara da cumb, shikuma yana saka link d'in hannunsa. Kusan tare muka gama, na kama hannunsa na d'aura masa agogon dabai San da shiba. Da mamaki ya kalleni amma saina janye idona ina murmushi da fad'in “Happy salla nane nida triplets d'inka”. Rasama mi zaice yayi, sai kallon agogon da koshi da kansa iya mak'urar za6ensa kenan. Yakai hannu zai rik'oni nai baya kad'an ina girgiza masa kai, Dan nasan makomar rik'onin. Cikin marairaice face nace, “please kabari saika dawo kawai”. Wani miskilin murmushi yayi yana cije lips. Nima na murmusa da nuna masa Alk'yabbar. Kansa ya girgizamin a hankali yana mai shafa agogon Dana d'aura masa da d'ayan hannunsa. “kibarta zasumin nauyi da yawa, idan zamu fita gaida Governor zan saka”. Ido d'aya na kashe masa da had'e yatsuna👌🏻alamar yayi. Ya murmusa shima yanamin jinjina👍🏻. Ban barsa ya fitaba saida namasa photo biyu, sannan na rakoshi har falon k'arshe, inda Muftahu da Matawalle ke jiransa, suma sunsha wanka mai birgewa, tamkar ka sacesu ko anguna ranar aurensu. Galadima ya kareni da bayansa tareda min alamar na koma. Baya buk'atar su ganni kenan. Nima saina juya ciki kawai. Yayinda nake jiyosu suna masa Sheri da kod'a wankan nashi. Na lek'a yara naga barci sukeyi, Dan haka na koma kitchen muka cigaba da aikin da fatan mu kammala akan lokaci. Tunda matasan samarin masu d'anyen jini suka fito sai kallo ya koma sama, bayi sai zubewa suke suna gaishesu, sukam sai d'aga hannu dad'an murmushi. Haka kawai sai Galadima yaji kewar Harun, aduk irin wannan ranar shike zuwa ya fiddoshi daga sashensa, amma yau gashi bak'in halinsa yasa a gidan yari zaiyi tasa bikin sallar dagashi har ubansa. Ya k'aunacesa saboda ALLAH ashe shid'in ba haka bane a tashi zuciyar. Motocin da aka tanada domin su suka shiga. Wambai da talba haushi ya kamasu, ganin wai yau d'an uwansu matawalle ne zai tafi salla tareda Galadima. Oho, daga matawallen har Galadima basusan sunayiba. A 6angaren Abie da mai martaba shiga sukayi iri d'aya, Abie ya fito a ainahin sarakinsa na asali, sai rama wadda kayan jikinsa suka 6oye, idan ka gansu bazaka ta6a banbanta wanene sarkin ba. Mai martaba ya fito rik'eda hannun d'an uwansa Abie, nanfa aka fara ruwan cameras dukda dogarai na karewa ma, cikin lullu6esu da manyan riguna da musu kirari da busar algaita suka shiga mota d'aya. Masallaci yacika mak'il da al'ummar manzon ALLAH (s.a.w), isowar Sarki da tawagarsa kawai ake jira. A dai-dai k'ofar baya ta musamman motarda ke d'auke dasu Abie ta tsaya, mai martaba ya taimaka masa ya fita suka shige cikin massalaci. Nan take aka d'auki kabbara bisa umarnin liman domin nuna godiya da al'ajabin hikimar ubangiji na dawowar tsohon Sarki cikin k'oshin lafiya, bayan tsahon shekaru daya d'auka baya k'asar. Duk matashin dake k'asa da shekara talatinma bai sanshiba. Mak'iyan 6oyefa da sukaga tabbas sai tsoro ya kamasu, ashedai zancen daya karad'e gari gaskiyane, yau ga Sarki Saifudden Abubakar a gabansu ko sunaso ko basaso kuwa. An gabatar da Kud'uba tamkar yanda addini ya tanada, mai ratsa jiki da 6argo, mai k'arama muminin kwarai imani da tsoron ALLAH. Su Galadima suna jerin sahun farko, saidai na kusada su Abie ba. Alhmdullah, sallar idi ta gudana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83