Chapter 17
Chapter 17
mai rad'a yace, “mikika gani?”. Na d'an kuma kwantar da murya ina janye idona daga cikin nasa, “Ba komai, kawai yanayinka ne ya nuna”. Baice komaiba ya matso da fuskarsa gab da tawa ya had'e bakinmu, dukda na tsorata kar wani ya shigo ya gammu haka na barsa, yayi yanda yake so inhar hakan zai kauda damuwar dake ransa, nidai fatana na cika alk'awarin dana d'aukarma Momma a duk sanda na gansa cikin damuwa. Saida ya gaji da kansa sannan ya bari tareda rungumeni yana sauke ajiyar zuciya, muryarsa can k'asan mak'oshi yace, “haka kike son ganina”. Kaina na girgiza masa, ya d'agoni da sauri yana kallona, yace, “to yaya?”. Murmushi nayi nafad'a k'irjinsa ina 6oye fuskata saboda kunya, shima saiya saka hannuwansa ya zagayeni yana murmushin, a hakanla ya furta “Thanks”. Bance komaiba, amma naji dad'i daya godemin. Kiran wayarsa da akayi ya sakani tashi daga jikinsa, zan tashi gaba d'aya ya rik'eni, a haka yay picking call d'in, na fahimci da papi yake waya, dukda kakansa ne yanda yake magana cikeda tsantsar girmamawa saiya birgeni, *_Mai dawakai_* danaji yana ambata da bayanin d'ansa mai suna Badi ne yaja hankali na, tsaf na fahinci zancen dukda bansan mafariba, yakuma yanke maganar bai k'arasaba yana fad'ama papi sai yazo zasu k'arasa zancen. Yanke wayar yayi yana huremin ido saboda kallonsa dana keyi, tunda ya fara wayar. K'asa nayi da kaina dan naji kunya ya kamani ina kallonsa, ya ajiye wayar yana fad'in “Zamukai Abdurrahman asibiti ne?”. Kaina na girgiza masa. nace, “A'a aiya warke bama sai an kaisa ba”. Yace, “Okay”. Idonsa akan yaran, Abdurraheem ya fara motse-motsen tashi, sauka nayi a jikinsa nakoma gaban kujerar na durk'usa ina d'an bubbuga bayansa, dan banason ya tashi, inhar ya tashi saiyasha nono, sauran kuma suma duk tashi zasuyi, bada nono a gaban Galadima shine abinda nake gudu ni kuma. Shikam tsura musu ido yayi cikeda sha'awa daga ita har yaran, ya d'auki wayarsa yamusu hoto batare da ta saniba. Saida naga ya koma barci sannan Na dawo kujerar dana fara zama, shima zamansa yagyara yana kallona, magana yakeson yi amma yanata juyata a zuciya, nidai bance dashi komaiba, saida ya gama k'asaitarsa da basarwa sannan yace, “Abba fa?”. Nace, “yayi tafiya yau kwana biyu”. “zuwa ina kenan?”. “wlhy ban saniba, amma miya faru?”. Kansa ya girgizamin alamar babu komai, yad'an furzar da huci yana kallona agogon hannunsa. “Shikenan ni zan wuce, zan iya dawowa a kowane lokaci inhar Abba ya dawo”. Kaina na jinjina masa, ya mik'e, nima saina mik'e ina fad'in “yaa Sauban fa?”. Bai tankaminba saida ya duk'a yayma yaransa kisses a kumatu sannan ya d'an kalleni ya d'auke kansa, “Tare muka dawo, amma zai wuce masarautar su papi gobe, dan a can zai zauna harya gama”. “ALLAH ya bada nasara”. Nafad'a ina sauke ajiyar zuciya. A kan la66a ya amsa da amin. Harya kusa nufar k'ofa nace, “bakace komai game da maganarmu bafa”. Cak ya tsaya amma bai juyoba, a haka yace “wace magar?”. Wani yawu na had'iye da k'yar ina fad'in, “Maganar rabuwa, nifa gaskiya bazan komaba”. Saida yaja kusan seconds 20 kafin ya juyo yana fuskantata, kallon da yakemin yasani janye idona daga kallonsa, cikeda k'asaitarsa yatako ya dawo inda nake tsaye, hannayensa ya cusa cikin aljihu yay matuk'ar d'aure fuska, cikin izzarsa yace, “wai nikam miyasa kikeda naci?”. Nima fuskar na tamke. Nace, “Neman y'ancina nake, tun farko a wannan tubalin ka gina auren, mizaisa kuma lokacin rugujeshi yayi bazakayi hakanba?”. Lips d'insa ya ciza yana kallona da k'ank'ance idanu, cikin salon Basarwar tasa yace, “So what idan nine na gina a haka d'in? Kinsan dai bazaki ajiyemin yara ba koda abinda kikeson ya kasance, dan yarana bazasu sha madaraba bayan sunada abinci”. “Humm” na fad'a cikin takaici. na gyara tsayuwa idona na cikowa da kwalla, “Yalla6ai karka manta a randa na kwana biyu gidanka da bakiknka ka tabbatar min baka zalunci? daga ni har kai mun amince cikin yarannan ya zone cikin k'addarar dabamu shiryama zuwanta ba, to mizaisa kuma zuwansu duniya yazama salon tauye hak'k'ina? Na amintane da aurenka domin warware k'ullun da akaimin da wanda yake kan mahaifina, bawai dan bansan y'ancin kainaba ko darajata, idan har nice a matsayin Amaturrahman zakaso wani ya aureni a matsayin auren shekara d'aya ko biyu domin cikar wani burinsa ya rabu dani?, addininmu da al'adarmu duk basu koyar damu hakaba, anayin aurene domin ibada, saboda bautar ALLAH ne, sannan ana ginashine bisa tausayi da rahama, inhar zuciyarka bazatayi dad'iba a matsayinka na mahaifin Amaturrahman idan hakan ace akanta ta kasance, to ya kake tunanin randa nawa mahaifin yasan gaskiyar matsayin nawa auren zaiji?, tunda nataso nake d'and'anar zafi da d'aci na zamantakewar rayuwar gidan yawa, taya zanso saka rayuwata a walagigin kila wa kala, na shigo wannan yak'inne domin neman y'ancin kai badan ribantuwa da ganima ba, amma lokacin dana wayi gari da abinda ban shiryamawa ba a cikin jikina haka na hak'ura na kar6a da hannu biyu saboda k'ok'arin cinye jarabawa, miyasa kakeson yin wasa da rayuwatane wai? Duk motsi dai yaranka! Yaranka! Karka manta nimafa y'ar wasuce, kamar yanda kakeji haka suma sukeji akaina, inason nima nayi aure na zauna tamkar kowacce mace a gidan mijinta, na fidda hak'insa da ALLAH ya wajabta min, shima ya fidda min nawa da ALLAH ya wajabta masa......”. Hannu ya d'agamin alamar ya isheshi haka, yakuma matsowa gabana cikeda izza yace, “mikikeso yanzun?”. Nace, “sanin matsayin aurena, inhar yaranka ne zan muku sadakar shayarwa na wata shida na yayesu nayi aurena da mijin dazai soni ya k'aunaceni domin ALLAH”. Bakinsa ya ta6e yana cije lips, jijiyoyin kansa duksun mimmk'e saboda 6acin rai, cikin takaici yace, “Yarinya har abada babu shegen namijin daya Isa na k'etara gona shima ya k'etarata, koda kuwa wannan gonar ta jinginace, ko ayanzu nabar duniya wani yayi hakan ban yafeba, duk gonar dana ra6a tawace ni kad'ai koda banyi noma a cikinta ba, wannan yazama first and last da zaki kuma kawomin irin wannan maganar, kodan kinga ina k'yaleki ne shiyyasa kike d'aukata wani sauna kiringa min zancen wani banza can daban, Munaya karki yarda na nuna miki a salin true color d'ina wlhy, ina kuma gargad'arki a karo na k'arshe”. ‘ya k'are maganar da bugamin yatsunsa biyu saitin fuska ya fice abinsa’. Baki na ta6e ina bin inda yabi da harara, sannan na saka gyalena na goge hawayen dake zarya a kumatuna nai kwafa na fice abina nima nabar yaran. ************************** Tunda ya fito Muftahu ke binsa da kallo, harya bud'e mota ya shiga baiko kalli Muftahun ba shi. Dama shine ya kawoshi, amma yana ajiyeshi ya koma saboda wani aiki daya bashi, dawowarsa kenan yana k'ok'arin kiransa yace zai shigo su gaisa da Munaya shine yafito a fusace. Baice dashi uffanba ya bud'e motar shima ya shiga ya tada suka tafi, saida sukayi nisa da tafiya sannan Muftahu yace, “Ranka ya dad'e wai mike faruwane?”. Shiru yamasa yak'i tankawa, shima Muftahu sai yaja bakinsa ya kulle ya cigaba tuk'insa. Sai jera tagwayen tsaki yakeyi, Muftahu ya kuma kallonsa sannan ya maida hankali ga tuk'insa, ya kuma rik'e sitiyarin yana fad'in “ALLAH ya huci zuciyarka ranka ya dad'e, idan kana ganin bazaka juri zuwanba kace ta dawo mana kawai”. Cikin jan wani
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83