Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 7

Chapter 7

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

basira, yanzu haka nasan sak'ona ya Isa ga y'an uwana, kafinma Ku kaini station d'in reshe ya juye da mujiya, dan dolene a kamaku da alhakin kamani kunga martabar wasu saita zube, mulkin da akema mutane homa da buri babushi kenan”. Murmushi Galadima yayi, dan yasan dashi yake, yad'an ta6e bakinsa yana cigaba da latsa waya hankalinsa kwance, Sir Isa da baffi da baba Rabilu, su Ameer duk kallon Galadima sukayi, don suji amsar dazai bada, amma saiya basar tamkarma baijiba. Saida ya kammala abinda yakeyi yay kiran Nuren suka kammala magana sannan ya kalli SD yana murmushi, “Wannan lissafin naka fa ya birgeni Alhaji shehu, saidai albishir d'in dazan maka nima shine, duk wani kira dazakayi ko ayi maka to zai shigo wayatane, yanzu haka driver d'inka yayi had'ari, rashin ganinka a motar kuma zantuka sun baje kowacce kafar yad'a labarai, Na tabbata dukkan labaran rana kaine shafin farko, hakama jaridun gobe masu fita, labarin nemanka da ta Yaya ka 6ata? Shine babban labari, sukuma abokan naka hakan zai tada hankalinsu, saisu fara zargin ko dai d'an tsohon Sarkine Galadima Sameer da wannan aiki?, dole kuma sufara bincike, bayan sun haukata y'an sanda wajen nemanka, daga haka kaga nikuma saina cigaba da samun hujjoji........🤦🏻 kai zaka samin ciwon kai wlhy”. Galadima ya karashe maganar da bud'e mota ya shige abinsa. Su Ameer duk suka shiga k'yark'yala dariya, saboda yanda Darma ya mugun shiga rud'ani da sakin baki yana bin Galadima da kallo harya shige mota. basu tsagaitaba saida Sir Isa ya tsaidasu ta hanyar d'aga musu hannu, yace, “Alahaji Shehu yadai? Kaji irin aikin masu basira ko? Kai! Kai! Harna tausaya muku lallai. Ameer! Kubi yalla6ai Galadima dashi, shikeda masaukinsa”. Angama ranka ya dad'e. Suka fad'a suna salute nashi. 🤦🏻‍♀lallai nimafa yau nashiga ciwonkan Galadima, shin wane laujene cikin nad'i kuma dabamu saniba haka? Nadai fahimci Su Ameer ba y'an iskan matasa bane, kamarma jami'an tsarone?🙆🏽. To Aunty Salama fa? Data kawosu a cakwakiyar. Masu karatu, kumuje zuwa dai, nasan komai yana gab da bayyana lallai kam.☹⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀. __________________________ Galadima dai kam plaza suka koma, yayinda Nuren ya tari su Ameer a hanya suka bashi SD. Acikin Plaza Galadima yad'anyi zagaye-zagaye, saida ya tabbatar da komai dai-dai a wajen ma'aikatan sannan ya fito suka d'auki hanyar masarauta. ***************** Bayan fitar Galadima Aunty Mimi sashen su Munaya ta nufa, ta isketa har yanzu tana juya kalaman Galadima dabata fahimtaba. Bayan sun gaisa tabata Umarnin ta shirya dan za'a kaita sashen manyan gidan ta gaishesu da bangajiya sannan suga yara, inhar zaki tafi wanka bayan kwana d'aya da suna haka akeyi a masarautar, to amma su nasu Munaya yazo da Matsala, tunda gashi sai bayan kwanaki hud'u da suna zasu tafi, matan Sarkine kawai basa zuwa gida wanka. Kuyangi biyu sukaima Munaya shiri, itadai wannan lamari Na d'aure kanta, haka kawai da girmanka ace komai sai anmaka, dolene mai mulki yake kallon talaka ba komaiba, sauk'inta ma bakomaine Galadima ke bada fuskar ayi mataba, yama hana hadiman masarautar sakewa a sashensa gaba d'aya, sai iya wad'anda ya aminta dasu kawai. Yaukam tasha kallon kanta a mirror, hakan yakuma tabbatar mata da tuna mata agidanfa SARAUTA take, a kuma matsayin matar mutum mai girman rawani da matsayi a Masarautan. (Kusan dai mutuniyar taku da jan aji😉, ai saita kuma tsumewa tana basarwa🤣). Suma yaran an musu shirin dake nuna lallai Ubansu waninine a wannan masarauta, sannan suma ababen tattaline ga wannan kujera kwara 1 tal dakowa ke mutuwa da rayuwa a kanta a masarautar gagara badau☹. Sun sami rakkiyar kuyangi da Aunty Mimi, kowane sashe saida suka zagayashi amma a mota, an farane da fada. Yau itace ranar farko da Munaya ta shiga Fadar sarkin ta, yaukam taga abin mamaki, musalta yanda wannan fada ta k'awatu ai 6ata lokacine kawai, ammafa lallai komai yaji, ga Sarki hakimce bisa garagarsa cikin kwarjini irinna mutuntakar mulki, sarkinmu kenan kuma sirikinna ta wani fannini, daga ni sai aunty Mimi da kuyangi ukune muka shiga, kowanne d'auke da yaro d'aya a hannu. Fada cike take mak'il anata fadanci, Su Wanbai da talba duk ana ciki, hakimai da masu manyan muk'amai Na masarauta da wajen masarauta duk an hallara, kasancewar shine zaman farko Na wannan makon, kuma ana saka ran zuwan Governor ne da zaizoma mai martaba jajen abinda ya faru Na 6atan y'an uku, dan labarine daya zagaye kowacce kafa ta yad'a labarai da socia media Na k'asar nan, (kunsan dai abin manya duk k'ank'antarsa saiya fita, balle wannan da yazamo mai girma). Bayan Munaya da aunty Mimi sun zauna a k'asan lallausar darduma can gefe suka kwashi gaisuwa, dogarai suka amsa da yawun Sarki, sannan suka kuma gaisheda fadawa. Daga nanan aka amshi su Abdurrahman, y'an majalissar Sarki sukaita d'auka d'ai-d'ai suna saka musu albarka, da addu'ar fatan alkairi. Bayan fitowarsu sai sashin iyalan mai martaba, yau ma dai gimbiya zulfa bata fasa nunama Munaya da yaranta soyayyaba, daga Munaya har aunty Mimi basu San komaiba, dan haka sukaji dad'i da sakin jikinsu fiye da sauran matan sarki. Daga nanan sai sashen Mama Fulani, (kaga manya, Sarautar gagara badau a hannunku take, mama fulaninmu ta mutunci🤸🏻‍♀😂, ga irin naku manyan mata👍🏻) To kunsan dai mutuniyar taku, yauma dai cikin izzar mulkinta suka isketa, ita dama Aunty Mimi babu ruwanta, tana mata yanda takeso, shiyyasa babu y'ar habaici ko bak'ar magana tsakaninsu kamar Galadima, hakanne yasaka munaya samun tsira daga samun nata rabon, amma mama Fulani bata d'auki yaro ko d'aya ba, a hannun kuyangin ta gansu tana ta6e baki. Daga Munaya dai har aunty Mimi babu Wanda yay ko tari, to balle kuyangi dasuka zama takalmin takawarta, basu jimaba suka fito, haka sukaita zuwa sashe-sashe, basu sami Kansu ba saida suka Shiga ko ina . Sun dawo kusanda awanni biyu aka gama loda kayansu a mota Samha da Sauban suka shige gaba aka kai gidansu Munaya. Ita kuma sai zuwa yamma za'a mata rakiya. ************ Gidansu Munaya dai tunda kaya suka isa aka tsaya kallon-kallo, daga Sauban kam har Samha babu Wanda yamusu kallon arzik'i, yo sunaji da hayak'in girma dana mulki, innarsu Munaya da Munubiya da tuni tana gida kawai suka kula, harda sakin jiki dasu sukaita hira, sunmayi zamansu anan sai ankawo Munaya zasu koma. Nanfa matan gidan suka fara k'ananun magana, saidai babu mai yunk'urin d'aga murya saboda tsaro🤣. Oho innarsu Munu ma batasan sunayiba, balle Munubiya da yanzu saita ma gadama suke ganinta, ko yaushe tana d'akinsu, da anyi magana tace jego, dukda gasu Fiddausi a gidan duk suna wankan suma, Fauziyyace kan shigo susha hirarsu ta zuminci, amma sauran saidai idan an had'u a gaisa, kowa uwarsa Na kitsa masa munafurci a d'aki (🤦🏻‍♀gaskiya iyaye mata munada gyara babba ta wannan fannin, inhar zaka rayu gidan yawa sai kayi gamo da irin wad'annan matsalolin kuwa, ALLAH ya ganar damu baki d'aya dai). ****************** Su gadima Na shigowa masarauta ana kiran salla, hakanne ya sakasu yada zango a massalaci, saida aka idar sannan suka k'arasa sashensa, Duk agajiye yake, d'akinsa daret ya nufa, yashiga zame kayansa tun a falonsa, yana shiga ciki k'arasawa kawai yayi yashige bayi. Ya dad'e aciki kafin ya fito, baiko cire rigar wankanba yasha wani Magani ya kwanta, dan kansa ciwo yake masa. Cikin mintuna k'alilan barci yay

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});