Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 55

Chapter 55

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kayan da take tana kallona da mamaki, “Ban ganeba, bakison komawar ne? Dakikemin wannan banzar tambayar?”. Baki Na zum6ura ina fad'in “Nikam dai bazan koma haka siddan ba, sai inhar yazo ya warwarema iyayena komai gameda tubalin daya k'ulla aurenmu a farko, yakuma basu hak'uri”. Kasa magana Munubiya tayi, saima ta zauna a bakin gadon, ita batasan wajen ubanwa Munaya ta d'akko halin taurin kai ba wlhy, ita tama rasa mizata ce mata. Nima d'auke kaina nayi gefe Dan ina kan bakana, ina tausayinsa Dan koba komai ya k'yautatamin a lokacin da nima banida lafiya, kuma ta silata yake kwance yanzu, to ammafa hakan bazai zama yasha a banzaba, kenan ma anan gaba wasu zasu iya aikata hakan ga kowacce mace?. Laraba dataji komai dake faruwa tana niyyar shigowa saita koma da baya gabanta Na fad'uwa, ita bataga laifin Munaya ba, dan wannan shine martaba da sanin ciwon kai, kuma wannan ya tabbatar mata da ba kwad'ayine yasata zama da shiba, amma bata fatan abinda zai girgid'a wannan Auren komai k'ank'antarsa waya ta d'auka ta kira Mom ta sanar mata komai, hankalin mom ya tashi, danba ta wanann hanyar takeson Munaya ta hora Galadima ba, bakuma taso iyayenta su Sani, suma sunada burin d'aukar mata mataki itada Momma, Dan bazasu bar wannan gangancin Na Galadima ya wuce a banzaba.. Momma ta kira tace Dan ALLAH ta kira Munaya tabata hak'uri akan ta koma, Dan babu mai kula da Galadima d'in, insha ALLAHU daga baya wannan maganar za'ayita. Momma ma duksai ta damu, dan har cikin ranta tana k'aunar Munaya, bazataso wata matsala ta tasoba bayan hankalinta ya kwanta akan zamansu. Munaya suna tare da Munubiya har yanzu a d'aki, ta balbaleta da masifa kamar ta daketa, Munubiya tanada hak'uri, shiyyasa idan tana masifa dolene kasan takai k'arshen 6acin rai, Munaya saita zuba mata ido kawai takasa cewa uffan, ana cikin hakane kira ya shigo wayar Munaya. Harzata share saikuma ta d'au tana dubawa, ganin Momma tai saurin d'agawa tana share hawayen da suka zubo mata. Cikeda girmamawa kamar yanda ta saba ta gaisheta. Daga can Momma ta amsa cikin kulawa itama, face, “Kun dawo lafiya d'iyata?”. “Alhmdllh Momma ya jikin Abie”. “Jiki kan Alhmdllh d'iyata, dama Abbanki ne ya kirani akan zaki koma, saboda Muh'd babu lafiya, da farko dai nayi tunanin cewa a barki harsai yazo yafad'a musu laifin daya aikata agaresu, saikuma nayi wani tunani daga baya, kiyi hak'uri ki koma yaud'in Dan ALLAH, saboda Mura bataima Muh'd da sauk'i, namiki alk'awarin zan d'auki mataki da kaina, zan sanar masa Ku tahoma gobe idan ALLAH ya kaimu kinji”. Bazan iyama Momma musuba har abada, Dan nasan bazata cutar daniba, saidai kuma nayi mamakin dama tasan auren Contract mukayine?....... Katsemin tunani tayi da fad'in “d'iyata idan kinga zaki cutu abari kawai, bazan ta6a bari Muh'd ya cutar dakeba wai danni Na haifesa wlhy”. “A'a Momma Na amince”. Daga can Momma ta sauke ajiyar zuciya tana fad'in, “Alhmdllh, d'iyata nagode sosai, ALLAH yay miki albarka kinji”. Idona cike da kwalla Na amsa da amin. Tace Na gaida mata kowa ta Yanke wayar. Munubiya dukda ta fahimci dawa Munaya tayi waya batace da ita uffanba, tacigaba da had'a musu kaya kawai. Ciwonsa ne yasani Na danne zuciyata Na amince, dakuma Kimar mahaifiyarsa danake gani, Dan sun nunamin dukkan k'aunar da inhar Na bitilcemusu banma kaina adalciba nima. yinin ranar gaba d'aya a hidimar shirin komawa mukayisa, ga gajiyar tafiya Na nuk'urk'usarmu, amma ya muka iya, da yamma dole su mama Rabi'a suka dawo domin mana rakiya. A gurguje please🤨😏. ****************** Abin mamaki sai gamu da rusar kuka ni da Munubiya, saikace wasu sabbin amare, bayan nasiha da Abba da baba k'arami, daddy sukai mana Na ajiye musu keys d'in motocinsu, da farko sunce bazasu kar6aba Na sanya musu kuka. Innaro tahau musu fad'a babu k'yau maida hannun k'yauta baya ai, wannan aikin shaid'anne. Albarka dai munshata kam, yayinda zukatan matan gidanmu yakusa babbakewa saboda bak'ar hassadarsu, kowa son samunshi ace d'ansane yayi. Laraba ma harda hawayen sabo, dan bak'aramar girmamawa aka mata a gidannanba, har abada bazata ta6a mantawa da dattako irinna inna ba. Kaf matan gidanmu dasu aka tafi, innarmu da Innaro kawai aka bari, amma hardasu Siyama. Ni suka fara rakawa, ALLAH ya somu muka iske Muftahu yadawo daga yawonsa zai shiga masarautar, da taimakonsa muka shiga, yayi mamakin dawowata, dan Galadima ya sanar masa muna Niger, shi baisan yadawoba ma, hasalima babu Wanda yasan Galadima ya dawo masarautar, tunda ko salla bai fitaba, sai hadimansa kawai. Ba sashenmu akai kainiba, Muftahu ya sanar musu sai an fara kaini wajen mama Fulani sannan, haka al'adar masarautar take. Aikam dai hakan akayi. Tarba ta mutunci mama Fulani tasa akaima dangina, tana nandai yanda kuka Santa da mulkinnan nata da izza, amma ni a yanzu tunda Na fahimci ita ba muguwa bace sai salon nata yake k'ayatar dani. An min dukkan yanda al'adar masaurat ta tanadar, sannan mama Fulani dakanta tamin rakkiya sashena tareda bayi da dangina, ko ina k'al tamkar muna nan. Bayan fitar mama Fulani y'an gidanmu suka kuma shishshiga suna kallo gida wai, dan ranar suna da suka fara zuwa basu sami wannan damarba saboda idon mutane, nidai batasu nakeba, hankalina nakan mijina, burina naje naga halin da yake ciki. Munubiya takuma min nasiha da bani wasu dabaru, tunda su sinzama tsoffin hannu, muko yanzune zamuyi zaman auren tsaftatacce, takuma nunamin nabi komai a hankali, tasan yayi kuskure amma bata hanyar tonama kanmu asiri zan nuna masa kuskurensa ba, kodan matsalar gidanmu ai saina duba, ni macece inada damar juya komai cikin sauk'i, nama iya zama dashi a lokacinda yake ik'irarin auren yarjejeniya bare kuma yanzu daya furta yana sona da bakinsa. Naji dad'in shawarwarinta, nakuma fahimceta sosai, Naimata godiya kuma, da alk'awarin amfani da shawararta insha ALLAH. Hakama mama Rabi'a tak'aramin nasiha da gargad'i mai yawa akan karsuji karsu gani, Na tsare musu mutuncinsu, Dan kowa da tarbiyyar gidansu yake ado. Itama na amsa mata da insha ALLAH zan kiyaye. A y'an gidanmu kam Maman Fauziyya Ce kawai tamin fad'a, amma sauran babu wadda tace nayi mai k'yau ko mummuna, wannan ba matsalarsu baceba, nima ban damuba, Dan wad'anda suka Isa dani sunmin kuma ya wadatar. yayinda zasu tafi rungume juna mukayi da Siyama da Munubiya, Zarah muna hawaye, jimuke tamkar karmu rabu. Dan wlhy yanzu nikam tausayi suke bani, koma miye dai iyayen su mata da k'addara Ce taja musu. Inaji ina gani suka tafi suka barni da kewa, danma laraba Na nan. Suna wucewa laraba ta kalleni, cikin dabarunsu Na tsoffi tace, “koyaya jikin magajin garin?”. Kaina a k'asa nace, “inaga barci yake iya”. Tayi murmushi, Dan kunyar Munaya da kawaicinta Na burgeta, yanda idon yaran yanzu ke a bud'e da rashin kunya a halinyanzu, da watace tuni tanufi d'akin mijin. tace, “yakamata to kiduba koya tashi, da saiki samu kayan k'amshi ki dafasu, insha ALLAH yasha Na kwana biyu sai murar ta barshi”. Godiya Na mata sannan Na mik'e a kunyace Na fita. A falon dazai sadani da sashensa naci karo da Muftahu, barka da zuwa yakuma yimin muka kuma gaisawa amutunce. Yace, “Boss d'in Na ciki kuwa? Dan sarkin k'ofa yace yayi sallama Dan nemamin iso yaji shiru”. Nace, “Ai bashida lafiyane, maybe

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});