Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 60

Chapter 60

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Munaya tayi ganin yana Neman maketa, idonta cike da kwalla tace, “Ai kaima kasani”. Hannu ya d'aga tamkar zai maketa saikuma ya fasa, ya dunk'ule hannun, “ke wai wace irin mutumce birkitacciya?, ba'a ta6a zama dake lafiyar ALLAH?, kinsan ALLAH wannan karan Abban zan kira Na sanarmawa idanni kin rainani.......” Cikin kuka munaya ta katseshi, “Dama kasanar masa ai shine ya kamata, kaga shima zaisan tayaya ka aurar masa yarinya, Papi da mai martaba zasusan Neman auren shekara biyu sukaje suka nema kuma suka d'aura.....” Kansa ya dafe cikin tsantsar takaici, miye kuma nadawo da wannan maganar bayan ta wuce? Kai yarinyarnan y'ar matsalace. Duk a zuciyarsa yake zancen. Momma da dama duk cikin shirinsune ta fita tai saurin shigowa tana fad'in “Minakeji haka? Waye yayi auren shekara biyu?”. Duk kasa magana sukayi, munaya Na kuka shiko kunya da nadama dukta rufeshi. “Waishin bakujini baneba?!”. Momma tayi maganar a tsawace. “Momma please cool down”. “Nayi cool down a ina Muh'd, dama abinda ka aikata kenan bamu saniba? Yanzu nan da hankalinka da iliminka Na addini da tarbiyyar da muka baka zakaje kayi auren yarjejeniya da d'iyar mutane? Shekara biyu ta cika kasaketa saboda son zuciya? Wannan d'abi'ar daga ina kuma ka samota? Danba koyarwar addininmu bace balle al'adarmu”. Jiki a sanyaye Galadima ya zauna a bakin gadon kansa a dafe, itama Momma saita zauna tana kiran Munaya data mak'ure jikin bango tana kuka maiban tausayi. Takowa tayi tazo inda take, saita zauna a k'asa kusada ita. Momma ta kallesu dukansu, saima suka bata tausayi, Dan takula kowannensu yakamu dason d'an uwansa Na gaskiya, tad'anyi gyaran murya tana fad'in “Muh'd!”. Kallonta yayi idonsa ya kad'a zuwa jaa kad'an, jijiyoyin kansa da gashin jikinsa duksun mik'e saboda damuwa, sai faman cizar lips yakeyi. Momma datasan bazaiyi magana ba tunda yahau sama saita cigaba da maganarta, “Muh'd ka fad'amin gaskiya ya akayi ka auri Munaya?”. Kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru yana kallon Munayar da kanta ke a duk'e tana kuka har yanzu..... “Ba kallonta nace kayiba, amsar tambayata nake buk'ata”. Zamansa ya gyara a sanyaye yace, “Momma ku gafarceni, dama nasan duk daren dad'ewa wannan ranar saitazo, nasan nayi kuskuren aikata abinda Addinina bai koyar daniba, hakama al'adata idan taji zata k'yamaci hakan, saidai wlhy a wancan lokacin banida za6in daya wuce hakan, ban ta6a tunanin son wataba, damuwar mahaifina da ciwonsane kawai agabana, banta6a kallon mace dawata siga ta soyyayaba balle tunanin aure, dukda fad'a da kukemin akan nayi aure a kullum. Bayan jaridar nan ta fita saina shiga rud'ani da zargin an aikotane dama gareni, wannan daliline yasani tunani sakawa a satomin ita Na ajiyeta harsai ta sanarmin wanene ya sata, amma sai Muftahu ya nunamin Sam hakan ba mafita baneba, dama kawai Na aureta, maganarsa ta sakani d'aukarsa mahaukaci, Dan haka namasa gargad'in karma ya kuma yinta, nidai kawai a d'akkomin ita Na tuhumeta. Shikuma yace Sam bazai bani goyon baya bisaga wannan gangancinba, k'yalesa nayi da nufin zan nemo Wanda zaimin aikin. Saidai kuma Nureddin kawai gareni, shikuma a time d'in yana Italy. Kwatsam sai wani tunani yazomin a zuciya da gamsuwa da shawarar Muftahu, Dan gaskiya yafad'amin, inhar wani yasan tana hannuna duniya zata d'auka abinda yafaru a jaridar nan gaskiyane Na aikata d'in, amma idan aurenta nayi bakin kowa zai mutu, inada kuma ikon sata tayi komai takuma sanarmin Wanda ya sata. Wannan ne dalilin dayasani bincike akanta, har nasamu aka d'akkomin ita Na sanar mata buk'atata. Da farko k'in abincewa tayi, amma daga baya bansan dalilinta Na amincewarba. Wlhy Momma kinji Na rantse ban aureta dannaci zarafinta ba, kuma harga ALLAH banso kutse cikin mutuncintaba, wlhy Muftahu ne ya zuba mana pills a hollandia muka sha, ALLAH kuma ya k'addara zuwan yarannan ta wannan silar, tundaga randa Na aikata mata abinda babushi acikin yarjejeniyarmu nayi nadama, nakuma gane kuskurena, tunkuma a lokacin nafara tausayinta, tsakanina da ALLAH badan Na amfanu da itaba Na aureta, saidai nasan koda fad'a mata nayi bazata aminceba, zata d'auka bisa wancan dalilinne nace ina sonta, amma nasha nuna mata inason nata, saita dunga sharewa, bansaniba ta fahimcenine kokuwa bata fahimtaba, wlhy Momma tsakanina da ALLAH nakeso Munaya, kuma nayi nadamar aikata abinda Na aikata, na tabbatar bazanma ALLAH wayoba, ikonsane ya aikata yanda yaso a lokacin dayaso d'in”. Momma tayi murmushinsu na manya tana kallon Munaya, “Na fahimceka Muh'd, amma adalci d'aya zan maka bisaga wannan gangancin naka, adalcin kuwa shine ka saki Munaya a warware auren Contract, saika koma ka kuma Neman aurenta na gaskiya ga iyayenta, ka kuma sanar musu mika aikata musu a farko, kanemi afuwarsu, shima takawa da mai martaba kaje ka sanar musu abinda ka aikata, nikuma namaka alk'awarin zan tsaya maka wajen ganin dawowar Munaya gareka”. Kasak'e yay yana kallon Momma da wannan tsarin nata, toshi mahaukacine dazaiyi wannan gangancin? Ai kowane irin hukunci zai d'auka amma banda na saki wlhy. “wai kobaka jini bane?”. Momma ta katse masa tunani. Narke mata fuska yayi tamkar zaiyi kuka, “Haba Momma Dan ALLAH, yanzunan dakanki kike fad'ar haka? Nidai kimin dukkan hukunci dakikeso amma wlhy banda na saki, bazan iya aikata wannan gangancinba, nayi kuskuren farko amma na biyu kam yana dai-dai daku rasani baki d'aya, wlhy inason matata ina k'aunarta har cikin raina, ni na amince zanje nasami su Abba da papi na sanar musu, nakuma nemi afuwarsu amma banda maganar saki please ”. Shiru Momma tayi tak'i tanka masa, saikuma yabama Munaya tausayi, ita dama burinta ya amince yayi kuskurenne. Haka yaytama Momma magiya amma tak'i tanka masa, shikuma ya nace. Saida Momma ta tabbatar yayi ligif sannan tace, “To ga adalci na biyu tunda ka nace, idan Munaya ta amince ni banida matsala ai, nabaka minti goma kacal zanje na dawo”. Tashi Momma tayi ta fita tana gumtse dariya, saida ta fita tayita sosai, dama akwai randa Muh'd d'inta zai risina irin haka akan mace, Muh'd dazai aikata laifi bada hak'uri ya gagaresa koma yafi Wanda yayma laifin zuciya da fusata, itakam babu abinda zatace da ALLAH sai godiya, Munaya tagama mata komai data zama sanadin canjawar yaronta mai masifar tauri da tsauri. A d'aki kam Momma na fita Galadima ya sakko k'asa wajen Munaya, matsawa tayi baya, ya bita, takuma matsawa, yasake binta, sai kawai ta saka masa sabon kuka. Kansa ya dafe yana fad'in “O ALLAH, Munaya please and Please kiyi hak'uri, nasan nimai laifine amma ki gafarceni, wlhy tun kwananki biyar kacal dakikayi a gidana nayi nadamar aurenki ta sigar yarjejeniya”. Cikin kuka Munaya tace, “saboda kashiga mutuncina ba”. Huci Galadima ya furzar, “Haba Munaya yakike fad'ar haka? Ke shaidace dagani har ke babu mai nutsuwar banbance wani Abu a waccan ranar, sai wahaltuwa da mukayi muduka, wlhy kinji namiki rantsuwa badan na lashi zumarkiba nafara sonki, a lokacin nadamar auren contract da mukayi nayi, amma soyayyarki tafara tsiro da yad'one a zuciyata tamar yanda tushiyar bishiya keyi, wasu k'yawawan halayyarkine suka jani a k'aunarki, rashin tsoronki da d'aukar raini, dukda kasantuwata a gidan dana fito baki amince na takaki yanda nasoba, hakan ya tabbatar min bak'ya cikin mata masu kwad'ayi dason wani Dan d'aukakarsa ko dukiyarsa, yawan ibadarki ya tabbatar min da tarbiyyarki, babbar mallakata da kikayi shine damuwa da ciwon mahaifina, wannan Ce babbar hanyar dakika cusan

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});