Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 41

Chapter 41

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Fulani ta gaje ta gagara badau, wannan ya sakashi shigowa cikin tawagarmu dasu tanderu, Sarki Saifudden Na kwanciya jinya kuwa aka d'ora Jalaludden bisa karaga a matsayin mai ruk'on kwarya, bisa alk'awarin zan cigaba da wazircinsa, sannan kuma sarautar waziri tazama din din din, y'ay'ana ma zasu iya gadona, shiyyasa lokacin da aka sanarmin ga camera a hannun mai dawakai nayi azamar son kar6a, amma yamin gardama, nikuma Na kashesu shida matarsa dan karsu tonamin asiri, nakuma saka yara subimin d'ansa daya gudu da camera, a masarauta kuma nace Badi da kansa ya kashe iyayensa. Maganar gaskiya mama Fulani batasan mahaifinta yayi wannan shirinba, danya ta6a tuntu6arta da batun kashe Sarki Saifudden amma tace Sam bata aminceba, bazata ta6a kisan kaiba, shiyyasa bai ta6a sanar mata yanda akayiba, shikansa Sarki Jalaludden baisan komaiba, dan yana masifar son d'an uwansa, bayason abinda zai ta6ashi, shiyyasa nikuma Na dinga kwantar masa dakai dan karma ya fahimci wani Abu, nasaka d'ana Harun yake bibiyar mana dukkan motsin Sameer. Wannan shine dalilina yamai shari'a”. Alk'ali yace, “toshi mahaifin gimbiya zulfa uwargidan Sarki na yanzu minene ya kawo shi a ciki? tunda dai yanzu bashida k'arfin da zaizo kotu ya bamu amsa saboda girma ya kamashi sosai, nakuma San Kasan komai shima a kansa?”. Waziri ya gyara tsayuwa yana jinjina kai, yace, “shima dai shirinsa bai wuce akan mijin y'arsa yayi sarautar ba, wato Sarki Jalaludden Na yanzu kagadai dolene jikokinsa su gaji sarautar anan gaba, sannan kuma yanajin haushin sarki Saifudden d'in, dan shi yaso ya auri d'iyarsa zulfa amma sai Marigayi Sarki Abubakar ya had'ashi da d'iyar Amininsa gimbiya Zaitun, bayan rasuwarta ma Yakuma masa tayin wata y'ar tashi amma sai aka maye gurbin gimbiya Zaitun da gimbiya Zeenah, shi burinsa dai ya nuna inhar ank'i aurama Sarki mai sarauta y'arsa to jikokinsa koda tsiya saisunyi sarautar gagara badau d'in, lallai wannan dai shine dalilinsa shima”. Babbar magana, wai dukdai akan mulki kayan duniya aketa wannan k'ulla-k'ulla, Wanda gashi yanzu a cikinsu wasuma sunbar duniyar baki d'aya, wannan wace iriyar masiface haka?. Alk'ali ma kasa magana yayi, saida yad'au ruwa yasha tukunna, Galadima kam ai babu mai iya tantance halin dayake ciki, ya kwantar da kansa jikin kujera yasaka handkerchief ya lullu6e fuskarsa gaba d'aya. Alk'ali yace, “Lallai a gaisheku, Ku yanzu dan girman ALLAH bakuji kunyar kankuba? Kamarku manyan mutane da k'asa ke alfahari daku da girmamaku Ashe ru6a66une a bad'ini, maciya amanar k'asa, lallai barin irinku ma ai had'arine wa duniya baki d'aya, dan duk abinda aka nema Na wulak'anta k'asarku zaku iya mik'awa domin cikar burinku, kune masu 6ata shugabanni Na kwarai masu k'yak'yk'yawar zuciya, ALLAH ya cigaba da tona mana asirin irinku a k'asarmu”. Gaba daya Kotu ta amsa da Amin!!!, Alk'ali yay k'asa da kansa yana bincike a k'aton books d'in gabansa kusan hud'u, kotu tayi tsitt kowa ya zuba masa ido, ya d'auki tsawon lokaci yana rubuce-rubuce kusan 30minute's sannan ya d'ago yana cire eyeglasses d'in idonsa, yasaka handkerchief ya goge fuskarsa sanan ya goge eyeglasses d'inma ya maida a idonsa yana kuma gyara zama dayin gyaran murya. Yace, “Bisa ga hujjoji da bayanan da suka fita a bakin wad'anda ake zargi kai tsaye, wannan kotu mai adalci ta yankema wad'annan mutane 20 da sukayi gamayya wajen ciwon Sarki Saifudden hukunci d'aurin rai da rai a gidan kaso, saboda kisa da suka dinga sakawa a nayi bayan laifinda suka aikata”. Kotu ta d'auki sowa gaba d'aya, saida alk'ali ya tsawatar ta hanyar buga gudumarsa, kowa yay tsitt. Alk'ali yacigaba da fad'in “Wazirin Sarki kuwa hukuncinsa shine kisa ta hanyar rataya, sakamakon kisan mai dokuna da matarsa, Hakama Alhaji Shehu darma, d'aurin rai da rai da horo mai tsanani saboda bada had'in kai wajen kisan d'an Uwansa Alhaji Abdul-Hakeem uba, dakuma tsiyatakun da suka dinga sakashi yanayi. Akwai yaransu dake hannu bisa laifi daban-daban da suka sanyasu, suma dai d'aurin rai da rai ne akansu, Irinsu Alhaji Halluru, Timothy da sauran su shekaru 30-30 ne hukuncinsu, da horo mai tsanani, dukansu babu maganar beli, dolene saisun rayu a gidan kaso. Sannan wannan kotu ta wanke Muhammad Sameer Saifudden bisa zargin ta'addancin Garkuwa da yara da yayi, dan bai ta6a kowaba a cikinsu, dagashi har tawagarsa da suka bashi gudunmawa kotu ta wankesu tas. Akwai d'angidan Waziri mai Suna Harun, kotu ta yanke masa zaman kaso Na shekaru goma bisa ga cin dunduniya Muhammad Sameer daya dingayi wajen sato bayanansa, ina fatan kowa yasamu hukunci dai-dai da abinda ya aikata, kuma duniya ta gamsu da hukuncin da muka yanke?”. Kotu ta d'auki sowar gamsuwa da ALLAH wadai da halin irinsu waziri dasu Darma. Kowa tur yakeyi da halin masu. Alk'ali ya buga gudumarsa alamar kotu ta tashi, daganan kowa ya mik'e saida ya shige sannan aka kacame da hayaniya, harda masu kaima su Alhaji Halluru duka, ana musu ihu, saima da aka fidosu mutane sukaita jifansu da duwatsu, sai y'an sanda suka dinga karesu har aka zubasu a mota, wasunsuna kuka sukeyi rurus dan ganin iyalansu ko damuwama basuyiba, wasu a cikin yaransu ai ko'a kwalar rigarsu, k'alilanne a cikinsu suka damu. Galadima har kowa yafita a kotun shi yakasa motsi, saida Abba Hayatudden da baffi da Abban munaya sukazo kansa, baffi ya cire Handkerchief d'in daya lullu6e fuskarsa saisukaga ashema a sume yake?, rikicewa sukayi, aka samo ruwa Abba Hayatudden ya shafa masa a fuska ya kawo numfashi. Zabura yayi, saida Abba Hayatudden ya rungumesa, jinsa a jikin k'anin mahaifinsa saiya saki wani irin kuka maiban tausayi, daga Abba har Baffi suma idonsu yacika da kwalla, Abba Hayatudden yashiga shafa bayan Galadima alamar allashi. Kusan mintuna uku ya d'ago da hanzarinsa yana fad'in “Abba Munaya da Nuren, lallai ban yarda darashin zuwansu kawo camera ba, alamun sarkin mota sun nuna akwai wani abu”. Da sauri baffi ya fita Neman sarkin mota, a waje ya iskeshi tsaye yana jiran fitowar Galadima. Baffi ya tambayesa miya faru, bai 6oye masaba ya sanar dashi komai, hankalin Baffi a tashe yakoma ciki yace su fito suje, hakkanne ya tada hankalin Galadima da tabbatar da lallai akwai matsala. A rikice suka shige mota, ko kallon y'an jarida dakeson jin bayani a bakinsu basuyiba, balle bi takan jama'a dake jiran su fito sumusu jaje....................✍🏻 *_Lallai K'arshen munafuki dama duk inda yake jin kunya, duk yanda kakai ga k'ulla kuttun sharri watan watarana saikaga k'arshenka, a duniya ne kokuwa a lahira, babu abinda ke dawwama sai ALLAH, Idan khairan ka shuka lallai saika girba khairan, idan kuma sharranne shima saika girbe abinka, duk danne Gaskiya da k'arya zatai wlhy watan watarana sai gaskiya tadawo sama k'arya ta koma k'asanta, kwanaki 99 ne suke zama Na masheranci, 1 tak kuma suzama namai gaskiya da k'yak'yk'yawar zuciya, d'ayarnan kuma saikaga yazo maka da nasarorin daka rasa shekaru aru-aru, duk nisan jifa k'asa zai fad'o, gashi dai yau su Harun sunzama a k'asa, k'asanma cikin matuk'ar k'ask'anci, musamman ma iyayensu._* _Ya rabbi ka tsaremu ka tsare mana zukatanmu, ka hanamu cutar da wani koda da fatar bakice, ko'a social media bana fatan kwana da hak'in wani ko hassadar wani, idan nabar duniya wace amsa zanbama ubangiji akan d'aukar zunibin wandama banta6a ganiba a zahiri😭, ya ALLAH ka gafartamana muda iyayenmu da dukkan musulmai baki d'aya, ALLAH ka rabamu

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});