Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya kalli Ameer d'in, danya ganesa sarai. Ameer ya d'aga kafad'a yana ta6e baki alamar bashida matsala😂.................✍🏻 🤦🏻‍♀yau dai typing d'in rowa nayi muku, gaba d'aya banajin yin typing d'in, kuyi manage kawai⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀. *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭👏🏻_* *_typing📲_* 💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._* *_♦RAINA KAMA.....!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ~BOOK 3~ 👉🏻5⃣ & 6⃣ ...............Galadima ya shigo murmushi d'auke a fuskarsa, dattijon dake zaune a falon ya d'ago ido yana kallonsa shima fuskarsa d'auke da murmushin, k'arawa Galadima yayi garesa, ya zauna kusa dashi yana fad'in “Baffina kanata jirana ko?”. Kafad'arsa dattijon ya dafa, yace “karka damu d'an baffinsa, nasan aiki mai muhimmanci ne ya tsaidaka. ya k'ok'ari?”. “Alhmdllh baffi, munata fama”. “ALLAH ya dafa mana, yanzu ina shi Darma?”. “Gashi a waje tareda ma'aikata, zamu jira zuwan Sir Isa ne, dan asan miya kamata, bazai yuwu mu had'ashi da su Harun ba”. “Uhm hakan shine dai-dai kam, amma yakamata suma bayanansu kagama tattarasu waje d'aya ka kawomin, kasan abubuwa zasu cud'e mana a tsakaninnan, dan fatana insha ALLAH wannan shine case Na k'arshe dazan fuskanta a rayuwar aikina, shekara 1 kacal ya ragemin cika talatin a matsayin lauya, insha ALLAH kuma zan cikasune bisa alk'awarin gurfanar da dukkan mai hannu akan mai martaba”. Murmushi Galadima yay, idonsa cike da kwalla, ya had'iye Abu mai d'aci yana fad'in “ALLAH ya cika maka wannan buri baffi, lallai ina alfahari dakai amatsayin uba, Kaine ka nunamin hanya alokacin da k'ofa ta rufe min, Kaine ka tsallakar dani a lokacin da gada ta karye ina tsaka da tafiya, ga kuma gagarumin hadad'i mai cike da tarnak'in iska ya taso, badan kaid'in ba da jajircewarka da yanzu ruwan daya zuba ya shafe da tarihina dana ahalina, da ace wani zai saurari labarina saiya d'auka labarin film ne ko novel, ni karan kaina nakanyi zaman yin tunanin anya akwai mai irin rayuwata a k'asarnan? Dan mafi yawa a tatsuniyoyi da hikayoyi akejinsa, saikuma abin mamaki ga nawa a zahiri, a yankin k'asar hausa, yanki mai tsananin ruk'on addini da Al'ada, yanki mai mutunta ahali da zuminci, inhar a shekaru 26 baya za'a iya samun masu irin ayyukan su tanderu lallai akwai abin tsoro kenan a k'arni nagaba da y'ay'anmu zasu mu'amulanta, Baffi da ace d'an Adam Na iya za6ama kansa rayuwa da banzo cikin ahalin jinin sarauta ba, amma Alhmdllh, ina godiya da Ubangiji daya halicceni yakuma San cancantar fitowa daga cikinsu.......”. kukane ya sark'e Galadima, Baffi ya mik'a masa handkerchief yana girgiza masa kai alamar kar yayi. Murmushin takaici Galadima yayi, sannan ya kar6a handkerchief d'in ya tsane k'ananun hawayensa. Baffi yace, “Muhammad Sameer akwai labarai da tarihin mutanen da yafi naka sark'ak'iya da hargitsi wlhy, sometimes abinda mukan gani a films ko hikayoyin marubuta akwaishi azahiri, saidai inhar bai faru akanka ba ko waninka saikaga tamkar k'anzon kuregene, kasan su mutane sunfi amfani da abinda suka gani da ido wato zahiri, ko suka San Wanda ya Sani wato tabbaci, a shekarun da nayi INA aiki nahad'u da cases da dama masu sark'ak'iya da ban tsoro, nakuma halarci kotuna da Dama domin ganin wasu cases d'in, idan ka samu wani case kai kanka saika ringa kokwanton anya kuwa wannan da gaske ya faru d'in? Amma daka tsananta bincikema saikaga abinda yafi Na farko mamaki, lallai a ranar gobe kiyama wasu zasu kasance cikin bayi masu tsananin kunyata agaban Ubangiji, Dan wata shari'a Ubangijine kawai mai iya mata, mu kammu acikin lauyoyi da alk'alai hummmm”. Baffi ya d'an bubbuga kafad'ar Galadima yana murmushi cikin takaici. Bai samu damar k'arasa magana ba akayi sallama, izinin shigowa ya bada, wani matashin dattijo da shekarunsa bazasu gaza 45 ba ya shigo, baikai girman baffi ba, sannan ya girmi Galadima sosai. Mik'ewa Galadima yayi yay salute nashi, dattijo ya murmusa yana kama hannun Galadima ya zaunar da fad'in “ni da kai adai bincika mai sarama wani”. Baffi yay dariya, “kudai kuka Sani da gardamarku wacce kullum bata k'arewa inhar kun had'u”. Bak'o mai amsa Sir Isa yace, “wai Yaya naga alhaji Rabilu zaune a waje suna sa'insa da banzan can?”. Nanma dai baffi ne Yakuma darawa, yace, “duk cikin aikine, dukkan wata magana dazai takalesa ya fad'a ai itama hujjace, kasanfa halin Alhaji Rabilu ai, shiyyasa nace masa da irin aikinku ya dace ba siyasa ba”. Sir Isa da yay dariya shima, yayinda Galadima ke murmushi, “Ai yalla6ai yanzu ma aikin dayake mana bashi da banbanci damu d'in, danya bamu damar sanin abinda tsawon shekaru muketa wahala da kaikawon sani”. “Wannan gaskiyane kam Isa, yanzu Yaya za'ayi da Darma kenan?”. Sir Isa ya gyara zamansa, yana saka d'an yatsa a baki alamar tunani, zuwa can yace, “inaga kam saidai mu nema wajen ajiyesa ko yalla6ai ya Adana mana shi, dan yakamata saimun kammala tattara komai a hannunmu bayan yalla6ai Galadiman mu ya dunk'ule kifaye a ragaya, idan sun mik'a wuya shima sai a sakashi a ayari ko?”. Baffi yace, “shawararka tayi kam, inaga yanzu abinda kasaba za'ayi, dan aiki da ilimi yafi aiki da agogo, kaike 6oyewa, kuma kaine akesa kanemo 6oyayye”. Murmushi Galadima ya sakeyi baice komaiba sai jinjina kai. Duk d'insu basu damuba, dan sunsan halinsa Na rashin son hayaniya tuni, ayanzuma suna d'an ganin canji fiye da shekarun baya, shiyyasa suka fara zargin ko (Hikimar matace take aiki?) Dan kad'an daga aikin mace ta tada gari, kuma kad'an daga aikin ta ta gyarashi. Sund'an tattauna har baba Rabilu shima ya shigo, wayar dayay recoding d'in dukkan musayar yawunsa da SD yabasu, babu Wanda baimasa jinjina ba, Galadima ya d'ora da musu godiyar hidimar da sukeyi a kansa tsawon lokaci. Suka amsa da cewar lallai mahaifinsa ya cancanci sumasa fiyema da hakan, dan yataka rawar gani shima a tasu rayuwar. Lokacin da suka fito abinda yabani mamaki shine su Ameer duk salute nasu sukayi suna k'amewa. Galadima basarwa yay, sai Sir Isa ne yay musu inkiyar su sauke hannayensu, baffi yay murmushi yana kallon Galadima dayak'i kallon kowa ta gefen ido. Sarkin mota dai yasha jinin jikinsa, musamman Basarwar da yaga Galadima yayi. SD dake zaune ya zuba tagumi yana kallonsu kawai ya janye hannunsa, cikin jinjina kai yace, “lallai duniya tana cike da abin tsoro, wai Isa kana nufin kaima wani abune a k'asarnan? Kai kuma babban munafuki Brr Usman Audu Tsanyawa! Ba kaine da kanka kaje kasamemu da albishir d'in ajiye aikiba? Ashe wannan k'aramin kwaron d'an cikinku kukema aiki?........” A tsawace Ameer ya katseshi, tareda d'aga hannu zai makeshi amma sai Galadima ya d'aga masa hannu. Sir Isa ne yay wata y'ar dariya yana matsawa ga Darma, yace, “Idan banda abunga Alhaji shehu kowama irin kune mai tsukakken tunani? Ai abin kallo bai k'are makaba saima nan gaba kad'an, kasan ita mota hanyarta kwaltace, birji ma idan tasamu bitake, balle dagwalon ruwa mai kayan datti, shikam jirgi miye gamisa da wannan? ko d'aga a tashi hanyar babu duk wad'annan, kaga kenan aikwai matuk'ar tazarar banbanci a tsakaninsu, kallon idoma tattancewa yake basai an shiga gasar tabbatarwa ba, kaikuma ai taka ta k'are, sauran shekaru sai a prison d'in dajin SAMBISA zaka idasu”. Dariya SD yayi, ya mik'e tsaye yana fad'in “iyaka dai Ku kaini police station, ina mai muku alwashin kwana d'aya bazanyiba a can, daga can a mik'amu Court, alk'alinma namune masu k'ananun

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});