Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 43

Chapter 43

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,195 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

zuciyar galadima tayi ta ragu sai yay gyaran murya, cikin tausasa harshe yace, “Muhammad Sameer mike faruwane? Kokuwa kukan farin cikin cikar burine?”. Da k'yar Galadima ya iya bud'e baki yace, “papi yanzunan duk abinda suka aikata a gareni tsawon shekaru bai ishesuba? Saisunyi yunk'urin kashemin d'an uwana da matata? Papi minayi musu da zaifi haka? Miye laifin mahaifina danyak'i goyama k'arya da cin amana baya? Miye laifinsa danya zama shugaba? Bayan hakan ba shirinsa bane tsarin ALLAH ne? Miyasa suka manta babu abinda ke dawwama sai ALLAH, papi inhar matata ko d'an uwana suka rasa ransu wlhy bazan hak'uraba, saina kashesu da hannuna nima s........” Dakatar dashi papi yay ta hanyar kiran sunansa. Galadima ya amsa masa da k'yar. “Kayi hak'uri Muhammad kaji, ALLAH yana tare da masu hak'uri, Hayatudden ya sanarmin komai, ALLAH yabasu lafiya, ba shari'ar duniya bace kawai shari'a, akwai babba wadda babban alk'ali zaima kowa, koba komai ALLAH ya kunyatasu tun a duniya, kowa yasan misuka aikata, kuma ka dak'ilesu suda masu burin aikata irin nasu, ka ringa tunawa akwai tonon asirin dayafi wannan, harma abinda yafi wannan da suka aikata akwai babbar kotu mai cikeda d'unbin jama'a da babban alk'ali a gaba, banason kabar wannan abin yayma zuciyarka tasiri haryakai ga kadaka k'asa, sannan karna kumajin kayi kuka, ka kwantar da hankalinka muci gaba da musu addu'a, insha ALLAH gobe zan shigo garin”. Gyad'a kai Galadima yayi tamkar yana gabansa, papi yakuma kwantar masa da hankali da nasiha mai ratsa jiki, saida ya tabbatar hankalinsa ya kwanta sannan ya barsa.... Ya jingina da kujerar yanamai lumshe idanu, wata nutsuwa ta musamman Na ratsa jinin jikinsa da zuciyarsa, knocking glass d'in da akayi ya sakashi bud'e idanu a hankali, ganin sarkin motane saiya sauke glass d'in k'asa, cikin girmamawa sarkin mota ya mik'o masa gorar ruwa. Bai musaba ya kar6a yana gyad'a masa kai alamar ya gode. Sosai yasha ruwan kuwa, wata nutsuwa takuma saukar masa, ya kuma d'aukar kamar 5minutes ya fito daga motar, ya koma cikin asibitin, yanson ganawa da doctor d'in, idan yaji bai gamsu da aikinsaba dolene yasan mai yuwuwa. Yana shigowa su Ahmad suka k'araso gareshi suna gaidashi da jajanta masa. Cikin k'arfin hali yace, “baku tafi gida bane?”. Sarkin mota dake tsaye kusa dasu yace, “Ranka ya dad'e ai Ahmad shine ya taimakeni nakawo camera d'in kotu d'azun”. Da mamaki Galadima ya kalli Ahmad yana nunashi da d'an yatsa alamar kaid'in?. Murmushi Ahmad yayi yana gyara tsayuwa. yace, “Uncle bayan fitowa daga kotune za'a hutunnan sai naji wani yaron su Abbana yana waya akan atare su Aunty a kar6a Camera d'in, dan basa buk'atar ta k'araso Court d'in, to hakan danaji shine Na k'arasa garesa Na bigi cikinsa akan zancen”. “nake cemasa zamuje ni da su Ahakam muma a kwato Camera d'in damu, so hakan dayaji saiya d'auka da gaske tare nake dasu, shine yabani key d'in mashin. Ina ajiye driver d'inka, sai mukazo asibiti ni da Yassar muka sanarma da Uncle d'ina, shine ya bimu da Ambulance har wajen da abun ya faru muka d'akkosu”. Galadima ya kamo hannun Ahmad ya rungumesa, yayma su Yassar dake kallonsu alamar suma suzo, cike da farin ciki suma duk sukazo jikinsa. __________________________ Hankalin mai martaba a matuk'ar tashe yake, jin wai dan kawai yayi mulki wasu suka bada gudunmawa domin durk'usar da d'an uwansa, “hazbinallahu wa ni'imal wakil” wannan wace iriyar masiface hakan?. Sai safa da marwa yakeyi a bedroom d'insa, idanunsa Na kwarar da hawayen tausayin d'an uwansa da Galadima, ALLAH Sarki mahaifiyarsa, yadad'e yana zarginta akan ciwon d'an uwansa, Ashe babu hannunta a ciki, son zuciyar mahaifinta ne, Wanda a yanzu haka tsufa ya kamashi sosai. Waya ya d'auka ya kira Abba hayatuddeen danyaji wane hali d'an d'an uwansa yake cikine? Dan yayi tsumayen shigowarsu masarautar amma yaji shiru. Bugu biyu Abba Hayatudden ya d'aga. Mai martaba ya tambayeshi suna inane?. Abba hayatudden ya amsa masa da vewar gasu a cikin asibiti, Dan mutanen su Alhaji Mansur sun saka an tare matar galadima a hanya itada Nuridden yayin kawo Camera Court. Kasa magana mai martaba yayi, saboda jin kuma wani sabon zaluncin, Wanda suka aikata baya baima ishesuba kenan. Abba Hayatudden ma bai kuma cewa komaiba saboda yasan ran yayan nasa ya 6aci. Mama Fulani kanta yau cikin damuwa take, bata ta6a tunanin mahaifinta zai iya aikata hakanba, dukda tsantsar son datake da burin y'ay'anta suyi mulki bazataso duk'usar da Saifudden akan hakanba, shekaru 26 bawan ALLAH Na kwance yana jiyya tamkar gawa, banbancinsa da gawar fitar numfashi, wannan wane irin son zuciyane su jinin sarauta sukeyi? Shikenan saboda sarauta sai aita halaka juna? “Ni Marawuyya wannan wane irin burine mai cutar da imani.......” Lallai zato zunubine koda ya zama gaskiya😢, kiyi hak'uri mama Fulani munata zarginki Ashe ba haka bane🤔🤦🏻‍♀. .............................★ A gidansu Munaya ma hankalinsu a matuk'ar tashe yake, gasu Abdurraheem nata kuka, dan tunda Munaya tabar gidan suke kuka, kukansu ya tada hankalin Munubiya dasu Inna sosai, lokacin da aka harbi Munaya bak'aramar fad'uwa gaban Munubiya tayiba, ta mik'e a zabure tana dafe k'irji, number Munaya tashiga nema, dan taji a jikinta wani mummunan abu ya faru da y'ar uwarta. Lokacin da labarin abinda ya faru da Munayar ya iso garesu mafi yawan jama'ar gidan saida suka koka, Dady kuma ya hana kowa zuwa asibitin, saisu mazan kawai sukai shirin zuwa, gashi basusan wane asibitin bane. __________________________ Iyalan su waziri hankalinsu a matuk'ar tashe yake, hakama su Alhaji Sageer, ga duniya tanata ALLAH wadai dasu, gaba d'aya yau kowacce kafar yad'a labarai da social media maganar kenan, su kansu sauran manyan kowa ya shiga hankalinsa, dan lamarin yayi matuk'ar girgozasu, suna yabama basirar Galadima matuk'a, gashi yabi ta hanyar da babu Wanda yata6a zaton zata 6ille masa yayi nasara, inhar za'a iya samun irinsa a yau, to lallai wataran za'a samo Wanda ya fisa ma. ....................★ Yanda masarautar su Galadima take a harmutse gameda wannan lamari haka tasu papi ma ta gama harmutsewa, dan lamarin ba'a cewa komai, cin amanar da waziransu sukayi yayi matuk'ar girgiza masarautun, bakajin komai sai gutsiri tsomar bayi da dogarai, harma da manyan gidan ba'a barsu a bayaba. Tashin hankalin da papi da inno suke ciki ba'a magana, ga Sauban ya tasasu gaba yanata kukan son zuwa yaga halin da Munaya da Nuren suke ciki, harma da yayansa. Dukda an hana fad'ama Su Momma amma saida labarin yakai musu, aranar aka nemama Aunty Mimi ticket d'in tahowa Nigeria, Samha nata kuka itada Khaleel zasu biyota, amma bata sauraresuba, dan hankalinta a matuk'ar tashe yake. ............................★ Doctor da kansa ya fito yayma Galadima iso cikin office nashi, bayan sun zauna doctor ya kalli Galadima cikin alamun damuwa, yace, “ranka ya dad'e da farko dai ina mai baka hak'uri akan zaluncinsu mijin y'ar uwata, ALLAH yay maka babban samako da sayya agaresu”. Murmuahi kawai Galadima yayi amma baice komaiba. Doctor ya kuma gyara zama yana fad'in “Alhmdllh jikin namijin babu wata babbar matsala, yanzuma mun saka masa alurar barcine cikin ruwan danya huta sosai yasamu nutsuwa, daya farka Normal zaku gansa. Ita kuma akwai harbi da akai mata a hannu, amma Alhadullh mun samu nasarar cire harsashin, tafin hannunta kuma shima anji mata ciwo, dan yatsunta Na tsakkiyama duk sun samu karaya, amma

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});