Chapter 70
Chapter 70
abinci takuramin yakeyi, shiyyasa ko sau d'aya nacisa a rana ya watar dani”. Nace, “Nikam dai ban wadatuba, bud'e baki wannan bashida nauyi, nasandai gudun k'aton ciki kake kawai”. Dariya ya sanya kawai. Nima nad'an dara ina kai abincin bakinsa. ALLAH yanzu saikaga mutun nata hora kansa da yunwa wai karyayi k'iba, shikuma ALLAH ba ruwansa, idan haka yayoka ko ruwane kawai abincinka sai kayita”. Abincin ya shiga taunawa da murmushi saman fuskarsa hankalinsa nakan system d'in. Haka nacigaba da bashi abincin da janye hankalinsa da hira, yayinda yake aikinsa da saurarena, idan na murmushine ya murmusa, Wanda zaiyi magana ya amsamin a tak'aice, Wanda tuni na fahimci al'adarsace tak'aita magana yabaka a dunk'ule kawai ka fassara sauran. 'Dagowa yay fuska a marairaice, “My mata ki tausayamin hakanan cikina karya fashe”. Dariya nayi da nuna masa plate d'in daya koma empty. Ya waro idonsa waje yana shafa ciki, “Dan ALLAH da gaske kike dukni na cinye?”. Nakuma tuntsurewa da dariyar danake dannewa, “Yo dawa kukaci? Wlhy duk kai kacinye harma d'an k'arawa nayi”. “Chiii yarinyarnan kin gama dani, amma gama dariyar muguntar ai kanki zata k'are wlhy, ke zakiji nak'ara miki nauyi”. Dukda na fahimci inda ya dosa saina shareshi ina cigaba da dariyata, nama mik'e daga kusa dashi. “Humyim zaki gane kuranki ne”. Yay maganar yana cije lips. Da lokacin isha'i ma yayi shine ya jamana jam'i, ya kuma komawa kan aikinsa, ganin aikin ya d'auke dukkan hankalinsa saina d'auka wayarsa Na kira su Zuhuriyya y'an Niger, muka gaisa dad'an ta6a hirar zuminci cikeda nishad'i. Sannan Na kira aunty Salamah itama nasha labari. Ganin harna gama wayoyina yana aikin still saina d'auka Novel d'insa d'aya nai zaman karatu. Sai wajen 10 ya dafe kai yana sauke ajiyar zuciya. Kallonsa nayi da tausayawa. Nace, “Ka huta haka nan mana my king”. Huci yakuma furzarwa yana k'aramin tsaki, ya taso daga gaban tebir d'in ya dawo bakin gadon ya zauna. Hannunsa Na kamo, Na kwanto kansa bisa cinyata inad'an shata goshinsa, idonsa a lumshe yace, “wlhy sonake naga na had'a kud'in jirgi da abubuwan buk'atar mu idan zamu wuce Nigeria, Dan Dr Erfan Fahad yamin albishir da k'arshen watannan insha ALLAH zai sallami Abie, gashi ina cikin matsalar kud'i Munaya, narasa yanda zanyi, bazai yuwu Na kwashe kud'in kasuwa Na narkarba kuma”. Ajiyar zuciya Nima nayi cikin damuwa, ganin ya bud'e idonsa saina murmusa ina d'an matsa masa kafad'unsa. Nace “ga shawara to”. “Ina saurarenki”. Yafad'a cikin maida hankali gareni tareda hard'e hannayensa a k'irji. Yatsana d'aya Na d'ora saman girarsa ina kwantar da gashin a hankali, “My King mizai hana gifts d'in dana samu Na aure da haihuwar yarannan kayi amfani da kud'ad'en ciki, abinda ya kasance Na kud'i a siyar dashi Dan banga amfanin ajiyesuba ai”. 'Dan Murmushin gefen baki yayi yana lumshe ido, sannan ya bud'e a kaina, “Munaya duk abinda aka baki ko yarana halalinkine, idan Na kar6a nazama mai handama kenan, ta wani faninma zaluncine, nine yakamata Na baki domin sauke wasu nauye-nauyenki Na y'an uwa da makamantansu, saikuma Na amsa Dan nine baba rodo sarkin babakere”. Na 6ata fuska ina janye hannuna daga saman girarsa dukda dariyar da furucinsa Na k'arshe ya bani, “Shikenan tunda baka d'aukeni yanda Na d'aukeka ba, yanzu tsakani da ALLAH idan kabarni dasu mizanyi dasud'in? Ashe abuna ba naka baneba?”. Nai maganar cikin matso hawaye. Da Sauri ya tashai zaune yana rik'oni amma saina kwace ina niyyar sauka ma gaba d'aya daga gadon. Gaba d'aya yasani a jikinsa yana fad'in, “Sorry tsaya muyi magana to kinji my sweetness, ya kikeso ayi yanzun?”. Hawayen nakuma sharewa nace, “Ka kar6a kawai”. Shiru yay yana kallona da nazarin maganar, saikuma yad'an numfasa yana gyara zama. Yace, “to ai naga suna Nigeria? ”. “A'a suna nan, Dan dukna had'osu Na taho dasu wannan karon”. “Ok babu damuwa, da safe zamuyi magana, shirya yara nakaisu wajen Momma dare nayi nafara jin barci”. Naji dad'i daya amince zai kar6a, Dan haka Na rungumeshi ina dariya. Bayana yad'an bubbuga kawai yana cewa “jeki shiryasu”. 'Dagowa nayi ina kallonsa, “Amma my King zamuke takura mata itama ai, ka barsu kawai”. “Babu wani takurawa, bazaki gane bane y'ammatana”. Babu yanda Na iya, dan babu jayayya a tsakaninmu, shiryasu nayi Na shayar dasu kowanne yay d'if, ya d'auka biyu yakai yadawo ya d'auki d'ayan shima. Nikamdai wannan Abu ya girmeni, amma babu damar magana. Ya dawo yana dariya da bani labarin gargad'in da momma tamasa akan wlhy mu tashi da wuri, kokuma da anyi sallar asuba yazo ya d'aukesu, Dan bazai yuwu ake barinsu da yunwaba. Sai Na k'arajin duk kunya ta lullu6eni, amma shi ko'a kwalar rigarsa, saima wata tashar daya kamo. A gurguje please😊. ************************ Washe gari ya koma Kashmir, yaso mu tafi tare amma Na nuna masa Momma yakamata ta fara zuwa, Dan tunda aka kai Abie babu Wanda yaje saishi kad'ai. Daga baya dai sai muka tsaida shawara akan zaije yafara ganin halin da ake ciki a yanzu, da wannan shawarar yatafi. Ba k'aramin abin mamaki Dr Erfan ya shiryama Galadima ba, shiyyasa gaba d'aya ya hanashi ganin Abie. Da yamma lik'is Galadima ya isa Kashmir, saboda bai tafi da wuriba, kai tsaye asibiti ya nufa dukda yana tunanin mawuyacine ya samu Dr Erfan Fahad a can, saboda lokacin tashinsa aiki yayi, saidai idan wani muhimmin aiki ya tsaidashi ko Emergency ya riskeshi. Ilai kuwa a harabar asibitin Galadima yaci karo da Dr Erfan Fahad ya fito zai wuce gida, sosai Dr Erfan Fahad yay mamakin ganin Galadima, Dan basuyi waya yana hanyaba. Ya bashi hannu sukayi musabaha da rungume juna, “wai my friend dama kana hanya?”. Galadima ya murmusa da shafa kansa, “Kabari kawai, ya aikin?”. “Alhmdllh”. “To inaga kawai muwuce gida. Dan wlhy nagaji sosai, yau nayi aikin daya wuce kima”. Galadima yay d'an jim alamar tunani. Murmushi Dr Erfan Fahad yayi yana dafa kafad'ar Galadima, “Sameer nasan kana tsananin buk'atar son ganin Abie ko? Karka damu, kaidai muje gida kawai abokina”. Galadima baice komaiba ya bisa suka wuce, Dr Erfan Fahad nata jansa da hira, amma shi iyakarsa murmushi ko eh da a'a. Ko kad'an Dr Erfan Fahad bai damuba, danya fahimci halin Galadima Na rashin son hayaniya tsaf, dama tun a baya bashida yawan magana, Ashe halin Na nan bai canjaba, saima k'aruwa dayay. Shikam Dr Erfan Fahad mutum ne faran-faran, ko jama'ar dake jiyya namasa wannan shaidar ta yawan tsokana. Ahaka dai suka isa gida, shidai Dr Erfan Fahad yanata murmushinsa. A k'ofar falo ya tsaida Galadima, tareda fidda handkerchief a aljihunsa yace Galadima ya rufe idonsa. Da mamaki Galadima ke kallonsa, amma yagaza furta komai. Dr Erfan Fahad ya jinjina masa kai da had'e hannayensa alamar rok'o. Ruf Galadima ya rife idonsa, Dr Erfan Fahad ya saka handkerchief d'insa ya d'aure masa ido, sannan ya kama hannunsa suka shiga ciki. A tsakkiyar falon ya tsaidashi, ahankali yace, “my friend are you ready?”. Cikin sauke numfashi Galadima ya d'aga masa kai. Dr Erfan Fahad ya murmusa yana kwance masa handkerchief d'in sannan yace, “Bud'e idonka”. A hankali Galadima ya shiga bud'e idanu, harya bud'esu gaba d'aya akan k'yak'yk'yawan dattijo zaune bisa kujera, fuskarsa ta k'awatu da murmushi, yasha gyaran fuska mai k'ayatarwa, sai gashi kad'an mai adon furfura da aka bari
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83