Chapter 45
Chapter 45
bata ta6a tsammani ko tunanin zaisotaba shine yake furta wad'annan dad'ad'an kalamin agareta, shine yake rok'onta ta kasance dashi har k'arshen rayuwarsa?, shine yake kiranta katangarsa?, harskensa, bugun zuciyarsa? Koda a yau tabar duniya ta ribantu da nasarorin masu yawan da wahalar k'ididdiga wajen lissafi. Galadima dake share mata hawaye da hannayensa ya duk'a ya manna mata kiss a goshi da saman la66a. Ta kuma bud'e idonta da suke jajur akansa, murmushi suka kuma sakarma juna, ya girgiza mata kansa alamar tabar kukan, idanunta ta lumshe alamar amsawa. Shikam ya tsura mata idanu ko k'yaftawa bayayi, y'ar ramar da tayi saiya k'ara mata k'yau da k'uruciya, ya shafa k'ananun kitson dake kanta ta kuma bud'e ido tana kallonsa. Cikin d'age gira d'aya yace, “baki tambayi ina yaraba?”. Lallausan murmushi ta kuma sakar masa, ta kwanto hannunsa dake sark'e da nata saitin bakinta ta sumbata, sannan ta d'orasa a saman k'irjinta. Tausayinta ya kamashi sosai, domin jikinta akwai zafi har yanzu, ga abincinsu sunyi matuk'ar cika, Wanda zazza6in nata yanada nasaba da rashinsu gareta, dukda akwai Na zafin ciwo. Hakan da tayi shima saiya fahimci mitake nufi, kuma duk'owa yay ya sumbaci goshinta, zaiyi magana doctor ya shigo. Shiru Galadima yay ya juyo yana kallonsa, itama Munaya daga kwancen take kallon doctor ta k'asan ido. Doctor dake gulma da zuciyarsa yana fad'in lallai ya yarda, duk sarautar Sarki a gaban matarsa bawane, matarce ke zama sarauniya..... (Ga naku Matan kwarai sarakin duniya👍🏻👌🏻😜) Galadima ya katse tunaninsa ta hanyar buga yatsunsa biyu suka bada sautin d'as-d'as. Doctor ya dawo hayyacinsa a kunyace. Yace, “sorry ranka ya dad'e, dama Nurse zata goge mata jikine da kuma gasa mata, Dan tasamu sauk'in nauyin da yay mata”. Murmusawa Galadima yay, ya zare hannunsa daga cikin Na Munaya yana mik'ewa tsaye, hannayensa ya hard'e a k'irji yana kallon doctor da fad'in “Doctor da raina zan bar wasu ganarmin sirrina? Ku kawo kayan buk'ata kawai”. Doctor daya fahimci Inda zancen Galadima ya nufa saiya murmusa yana cewa “Afuwan ranka ya dad'e”. Hannu kawai Galadima ya d'aga masa, ya juyo suka had'a ido da Munaya ya d'aga mata gira da cizar lips d'insa. Baki ta tunzuro masa tana yamutse fuska. Ya d'aga kafad'a da ta6e baki alamar bashida matsala🤷🏿♂🤣. Nurses biyu suka shigo da dukkan abinda ake buk'ata, Galadima Na tsaye ko kallon inda suke baiyiba, idonsa nakan matarsa k'yam, sukam sai satar kallonsa sukeyi, suka ajiye suna fad'in “Gashi Ranka ya dad'e”. hannu kawai ya d'aga musu amma ko tari baiyiba. Fita saukai cikin takaici, dan sunso yayi musu magana koda sau d'aya ne. Takawa yay a hankali jikin k'ofar ya Mirza key, sannan ya dawo yana cire link d'in hannun rigar farar shaddarsa da tattarewa zuwa sama. Suka had'a ido da Munaya tai azamar janyewa cike da kunya. Murmushin gefen baki yayi yana zama bakin gadon kusa da k'ugumta. Bottoms d'in jikin green d'in rigar asibitin yafara cirewa a hankali, itadai kunya ta hanata bud'e ido, gashi ya tsareta da idanu, Dan tanajin yanda idanunsa ke yawo cikin jininta, salon daya koma wajen cire bottoms d'in ya sakata dafe hannunsa da hannun haggunta, ta bud'e ido tana kwa6e fuska. Gira ya d'aga mata, da wani mata salo da kwayar ido. Babu shiri ta maida idonta ta rufe ruf, tsigar jikinta Na tashi. A haka dai aka gama cire rigar, yaja bedsheet d'in da ake lullu6a mata a k'afafu ya rufa mata a jiki, sannan ya kuma gyara hannun rigarsa yana tsoma madaidaicin towel d'in cikin ruwan d'umin dake a boket, ya matsa dukda akwai d'an zafi ruwan haka yafara danna mata jiki dashi. Tanajin zafi, amma kuma tanajin dad'in d'umin ruwan sosai, k'in yarda tayi su had'a ido har aka gama, ya d'auki wani d'an kwalba da mai ke ciki tamkar zaitun, karantawa yay yaga amfaninsa sannan ya zuba a tafin hannunsa yana murzawa, kumajin tattausan hannunsa daya had'u da sul6in mai tayi a k'afafunta, tad'an kuma bud'e ido tana kallonsa. Ganin ba ita yake kalloba saita shagala da kallonsa, babban mutum mai daraja jinin mulki yau shine ke mata hidima irin haka, itako badan kar ace tayi alfahari ba da cika baki da yawa da tace ta more fiye da kowacce mace (🙄nidai fa bandani, reader's Ku kun yarda harda Ku🤷🏻♀)?. Sosai tafara jin dad'in tausar, Dan da salon nutsuwa yake mata, tuni tafara lumshe idanu, hardai barcin yaci galaba a kanta. Sai dai saukar numfashinta yaji a hankali. Ya kalleta yana murmushi da lumshe idanu, bai bartaba saida ya tabbatar barcin yayi nisa, cikin dabara ya canja mata rigar da suka sakko a kayan domin canji. Ya duk'o ya sumbaci goshinta da bakinta yanajan bedsheets d'in sosai ya kuma lullu6a mata. Kayan ya maida gefe, ya koma saman kujerar dake gefem gadon ya zauna ya zuba mata idanu, kai kace yaune ya fara ganinta, ya dad'e a haka kafin ya d'auka wayarsa yana dannawa. A haka Nurses d'in suka masa Knocking, izinin shigowa yabasu, amma sai suka murd'a k'ofar a rufe. K'aramin tsaki yaja yana muk'ewa, shi yama manta ya rufe. Bud'ewa yay yadawo ya zauna yana d'ora k'afa d'aga kan d'aya da kuma d'aure fuska. Tuni Nurses d'in suka shiga hankalinsu, cikin risinawa d'aya tamasa bayanin zasu canjama Munaya bandejin jikinta ne. Batareda ya kallesuba yace, “kuyi a hankali, Dan barci takeyi, idan kuma kunsan zata iya farkawa kubarsa saita tashi ”. Kallon juna suka, kowacce tad'an ta6e baki, d'ayar tace, “insha ALLAHU bazata tashiba ranka ya dad'e”. Nanma Kansa kawai ya jinjina musu yacigaba da latsa wayarsa. Haka sukai wannan aiki a gabansa Dan yak'i fita, data motsa ya zuba musu uwar harara mai rikita hanjin ciki. Dolensu suka bita a sannu har suka samu kammalawa lafiya, kowacce ta fice a tsorace.............✍🏻 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻 [8/22, 8:25 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* *_💡HASKE WRITERS ASSO...._* *_♦RAINA KAMA...!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_BOOK 3_* 👉🏻2⃣1⃣ .................Kusan mintuna 7 da fitar Nurses d'in doctor yay Knocking, Galadima ya amsa ba tare da ya ajiye wayarba, doctor ya shigo abinsa, Nurse d'aya da sukai akin d'azun Na biye dashi. Galadima ya d'ago yana kallonsu fuska babu walwala, Dan shifa yafara gajiya da wannan shigi da ficin, amma baice komaiba. Doctor daya d'an tsargu yace, “Afuwan ranka ya dad'e, dama ina ganin yakamata tafara cin abincine, Dan ruwan da muke saka matane dama yake taimaka mata, to yanzu kuma zata fara shan magunguna insha ALLAH”. Galadima yad'an sauke numfashi yana fad'in “ok, to amma yaranfa? za'a iya kawosu yanzu?”. “eh to, sunkai nawa?”. Yatsu uku Galadima ya d'agama doctor, dukda yayi mamaki saiya danne abinsa, musamman dayaga munayar y'ar k'arama da ita. yace, “Ranka ya dad'e dadai and'an k'ara mana lokaci koda kwana biyune, har yanzu zancen danake maka ba'ason abinda zai cika mata hayaniya a kai”. Jinjina kai Galadima yayi kawai, alamar gamsuwa. Daganan Doctor yay d'an dube-dubensa ya bama Galadima Drugs d'in Munayar akan Nurse zata dinga zuwa tana bata kullum. Doctor Na fita shima ya ajiye wayarsa kusa da ita ya fito, d'akin da Nuren yake ya shiga, yana zaune Aunty Mimi Na bashi abinci a baki, Galadima yad'an hararesa yana fad'in “k'aton banza kacika shagwa6a”. “Uhmyim” Nuren ya fad'a yana ta6e baki da rama Harar da Galadima ya masa. Ita dai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83