Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 71

Chapter 71

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya zagaye fuskarsa. Wata zabura Galadima yay mai kama da firgita, Dr Erfan Fahad yay saurin tarosa, Dan kad'an yarage ya zube a k'asa. Cikin rawar baki data jiki yake kallon dattijon, dak'yar ya iya fusgo numfashi da magana mai cike da in'ina daga bakinsa “A..b..ie k..ai.ne?”. Abie ya share hawayen da shima suke ziraro masa, cikin tsantsar so da k'aunar d'an nasa yabashi amsa da fad'in “Tabbas nine Muhammad Sameer sanyin idaniya, Abie d'inka ne zaune yau agabanka, Wanda ya tashi cike da hukuncin Ubangiji gagara misali”. Galadima ya maida kallonsa ga Dr Erfan Fahad. Murmushi Dr Erfan Fahad yayi, “Karkayi kokwanto da ikon ALLAH Sameer, shike kwantar da Wanda yaso, Yakuma tasheshi a lokacin da yaso, dama ba'a yankema rayuwa hukunci, mai jiyya saiyayi rayuwa mai tsayi amma mai lafiya a wayi gari yazama gawa, ciwo bashi bane mutuwa, kwanaki 10 kacal Na d'auka ina treatment d'in Abie ga66ansa suka fara aiki, a sauran sati uku danayi tare dashi muna koya masa yanda zaiyi tafiyane, da zama, d'aukar Abu, da sauransu, Dan duk ga66ansa sun manta, kamar yanda ka sanarmin addu'ar da kukaita masa lallai itace babban magani daya zama mai tasiri a garesa, domin nikam abinda ba'a rasaba Na k'arasa, duk Wanda yabar addu'a lallai dole matsala tazama ma'abociyar rayuwarsa, a yanzu haka ina mai tabbatar maka Abie zai iya tafiya dayima kansa wasu abubuwa, amma bamasu yawaba, tafiyarma bamai tsaho ba, Dan yawanyin ne zai bama ga66ansa kwari da sabo, shekara 26 mutun Na kwance sai na'urori ke sarrafashi ba k'aramin Abu bane Sameer, Dan dolene akira Abie d'an baiwa, masu irin nasarorinsa kad'anne a cikin al'umma wlhy, kaje ga Abie, domin kuna buk'atar juna”. Tamkar Dr Erfan Fahad yama Galadima allura ne, cikeda sasaarfa ya k'arasa ga Abie, a gabansa ya zube yana sakin wani kuka maiban tausayi tamkar mace”. Abie ya sakko daga kujerar ya rungume jarumin d'ansa shima yana hawaye, sun dad'e a haka, jisuke tamkar karsu saki juna, a tunaninsu Kodai mafarki sukeyi, suna tsoron rabuwa su farka suga ba haka baneba. Shi kansa Dr Erfan Fahad hawayen tausayinsu yake sharewa. Ni kaina masu karatu wannan lamari yasani hawaye Na gaske😭, da zaka k'iyasta hakan a kanka wane farinciki kake hangowa yayinda waraka ta riskeka?.😭 Wad'annan bayin ALLAH yau lallai suna cikin tsantsar farin ciki, ko kad'an Galadima ya kasa gusawa daga jikin Abie, Yakuma k'i kiran kowa, burinsa shima yabasu mamaki tamkar yanda Dr Erfan Fahad yabashi. A yau yay niyyar su juya amma Dr Erfan Fahad ya hana hakan saidai gobe, Dan dare yayi kam a yau. A gado d'aya Galadima da Abie suka kwana, dukda sunma cinye rabin daren da fira😁. ********** Hankalin Munaya duk a tashe yake, saboda tanata kiran Galadima yak'iyin picking, tun tana daurewa harta gaza tafara kuka da shiga tsantsar tashin hankali. Momma Ce ta lura da canjawarta, ta tambayeta lafiya?. Kasa magana tayi saboda kunya, saida Momma ta kuma maimaitawa sannan tace, “Momma inata kiran Number Abbansu ne yak'i yin picking tun d'azun”. Ita kanta Momma ta kirashi baiyi picking ba, amma ta d'auka ko wani uzirine yasha kansa, sai yanzumefa hankalinta ya fara tashi itama, waya ta d'auka tashiga kiransa amma babu amsa, kusan kira 10. Cikin firgici ta kalli Munaya da aunty Mimi da itama take kan gwada kiran nasa, amma itama ba'ayi picking. “Kinga Munaya tura masa massage mu gani”. Jiki a sanyaye Munaya ta tura massege, amma kusan 30minutes babu reply. Hankalinsu fa yakai k'ololuwar tashi, amma sun rasa mafita. ********* Shikam Galadima baima San sunaiba, wayarma kanta baisan inane ya jefar da itaba, gabaki d'aya hankalinsa ya tattarane ga Abie, harkuma suka kwanta barci bai nemi wayarba. *********** Yau kam inhar wani yay barci a cikinsu to bana kwanciyar hankali baneba, dan kowa damuwa tamasa katutu, dai-dai da Hadiman gidan suma duk a damuwa suke, sai dai tamkar yanda suka saba yauma sun mik'a lamarinsu ga Ubangijin talikai. *_Washe gari_* Tunda safe Momma ta nemi Number Dr Akash da Dr Ajey akan rashin jin Galadima, duk sun amsa mata da zasu bincika. Can kuma su Galadima sun wayi garine da shirin dawowa New Dhalhi, cikin tsantsar farin ciki irin Wanda misaltashi ma 6ata lokacine.................✍🏻 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻 [8/22, 8:36 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* *_💡HASKE WRITERS ASSO...._* *_♦RAINA KAMA...!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* _____________________ *_Tawan miss xoxo tawa ni kad'ai, wannan gaisuwar takice ke kad'ai da babbar murya my dear, ALLAH ya bar mana zuminci mai d'orewa har Abadan, ke ta dabance a zuciyar bilyn Abdull, ina yinki irin Trillion's d'innan wlhy, na gaisheki da gaba d'ayan ahalinki da tawagar y'an Group d'inki na HOME OF NOVELS baki d'ayansu, alkairin ALLAH yakai gareku har gadon barci My Hafsy🤸🏻‍♀😘👍🏻._* _______________________ *_BOOK 3_* 👉🏻3⃣0⃣ ...............Da asubahi na tashi jikina cike da gajiyar tafiya da wadda boss ya k'aramin, daga sallar asubahi bai samu dawoba, Dan ana fitowa salla dukan ahalin gidan mai ruwa da tsaki sun hallara ne ga yima Abie barka da zuwa dakuma tabbatar da gaskiyar zancen, domin tabbatar musu da kokwantonsu mai martaba yabasu damar ganin Abie d'in tareda shelar Sank'ira. Wannane dalilin yad'uwar zancen dawowar ta Abie har a wajen masarauta. Dukda gajiyar dake tare dani bansamu komawa barciba, nashiga k'imtsa gidan iya bedrooms d'inmu zuwa nashi sashen da babu wata baiwa dakeda lasisin shiga. Sauran guraren zuwa kitchen kuma bayina dasukayo asubancin zuwa sashen saboda jin nadawo ne keta k'ok'arin gyarawa. Na fito da nufin komawa d'akina na tashi yara na musu wanka cikin bayina d'aya ta zube Guywoyinta a k'asa tana fad'in “Ranki ya dad'e ga sak'on kayan abincin salla nan daga sashen mama fulani”. Cikin d'an mamaki Na kalleta tareda kayan abincin dake jibge, sai naman kaji cikeda k'atuwar roba irin wadda ake tarama mai jego ruwan wanka. Katsemin tunani tayi da kuma fad'in, “Ki gafarceni ranki ya dad'e, wannan al'adar mama Fulani Ce, a duk daren salla takan aikama kowanne sashe Na y'ay'anta da manyan gidannan irin wannan kayan, yanzu zama a k'araso da sauran, kowane sashe dasu yake abincin salla”. Kaina Na jinjina tareda zama bisa kujera ina d'ora k'afa d'aya kan d'aya da kallon baiwar dani nama mance sunanta a yanzu. Nace, “Oh, yama sunanki?”. “Ranki ya dad'e Umimi”. “To Umimi wace shugabar hadiman sashen nan?”. “Nice rankai ya dad'e”. “Ok, ya zamuyi kenan? gashi mun kasance lokacj a k'ure, Dan yanzun kinga kusan 6:23am, bamuda isashen lokacin abincin salla kenan”. “Ranki yadad'e ki gafarceni, zamu iyayi insha ALLAH, tunda kinga ai munada yawa”. Shiru nayi inad'an nazari, saikuma Na sauke numfashi ina mik'ewa damata nuni muje kitchen d'in. Alhmdllh inada kaso mafi yawa Na buk'ata, saidai abinda ba'a rasaba, Umimi nasaka ta tattaro sauran suka shigo da kayan, Dan danan suka fara rage aikin, ni kuma Na fito nad'an rubuta sauran abinda nake buk'ata nabama baiwa d'aya da kud'i takaima Sarkin Mota yabama wani ya sayomin. Badansu Abdurrahman sun tashiba Na tadasu duknai musu wanka, shirin sune yad'an jani lokaci abinka daba d'ayaba, gashi sunfara wayo, sauk'i nama d'aya Umimi babbar macece kuma Na yaba da tsaftarta. Duk da dai namusu gargad'in jira nazo Na had'a komai da kaina. A gurguje nayi wanka nasaka simple gown dabazata takurani wajen aikiba, nasaka k'aramin hijjab Na fito nabarsu Abdurraheem a d'akin,

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});