Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 61

Chapter 61

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

k'aunarki cikin sauk'i, Munaya kin bada gudunmawa a arayuwata wadda bazan ta6a mantawa da itaba, aduk lokacin da raina ya 6aci kafin shigowarki rayuwata nakan azabtu da motsawar ciwona, na fita hayyacina, bana sauraren kowa sai damuwata, amma kece kika canja wannan matsalar tawa ta k'yak'yk'yawar siga, cikin hikimarki da ilimin da ALLAH yabaki, da kasancewarki mai tarbiya, Dan kowanne tsuntsu da gaske kukan gidansu yakeyi, nasha gwadaki akan abubuwa daban-daban amma kina cinye wannan gwajin nawa saboda zuciyarki a tsarkake take, please ina rok'onki a karon farko ki yafemin, kiyi hak'uri kiyi hak'uri kiyi hak'uri, nimai laifine amma mai nadama, tabbas zanji ciwon wani ya k'ulla alak'ar aure da Samha ma ba Amaturrahman ba ta sigar dana k'ulla dake, amma wlhy inhar kince naje gabansu Abba na sanar dasu komai zanje, nidai karki bari aurenmu ya girgiza koda da igiya d'ayane, namiki alk'awarin samuna fiyema da yanda kike tsammani matata”. Idanu Munaya ta d'ago tana kallonsa, ya jinjina mata kai da lumshe idanu alamar tabbatarwa. Batace komaiba ta maida kanta k'asa. Hanunta ya saka anashi yana matsawa, a marairaice yace, “Kokinason Muhammad Sameer yamiki kukane Munaya? Sannan ki yarda nayi nadama? Wlhy nayi nadama da gaske”. Jikinsa kawai ta fad'a takuma sanya masa wani kukan, shima ya rungumeta yana sakin wasu mugayen ajiyar zuciya, jiyake kamarma ya had'iyeta gaba d'aya ya huta, suzama abu guda d'aya kawai. Momma dake bayansu tashiga tafi tana takowa cikin d'akin. Da sauri Munaya tabar jikinsa tana 6oye fuska, shikansa Galadima yaji kunya, yay k'asa da ido tana murmushi. Momma ta zauna tana fad'in “Alhmdllh ya Ubangijin talikai na gode maka, ALLAH ka d'orar da wannan zama har'a aljanna”. A saman la66a Galadima ya amsa da amin. Munaya dai kunya ta hanata kallon kowa. Momma tace, “Nima yau zan sanar muku abinda baku saniba”. Daga Galadima har Munaya kallonta duk sukayi. Ta gyara zamanta tana murmushi. Tace, “Tun farkon Aurenku nasan komai”. Da mamaki duk suka kalli juna sannan suka maida kallonsu ga Momma. Murmusawa takumayi, “Lokacin da Muh'd ya yarda zai auri Munaya amatsayin auren contract Muftahu ya sameni ya sanarmin komai, danshi burinsa Muh'd ya Auri Munaya ne aure na gaskiya tamkar kowa, a lokacin kuma yasan cewar Gimbiya Zulfa itace ta saka aka muku wannan 6atancin, domin 6atama Muh'd suna, abinda yasa Munaya ta shiga matsalar ranar da kuka had'u a filin idine, shikuma Erfan dayazo miki da suna Fu'ad an sakashi sakama Muh'd idone, saikuma ya ganku tare, duk zatonsa akwai alak'a a tsakaninku shiyyasa yayta bibiyar lamarinki harya kaiku plaza, saidai kuma ya rikice yagaza banbanceku lokacin daya fahimci sewar Ku y'an biyune, shi Muftahu a lokacin bazai iya tunkarar Muh'd da ainahin gaskiyar abinda ya saniba gameda Gimbiya Zulfa da Harun, shiyyasa yayta cusamasa ak'idar aurenki a zuciyarsa, Dan aganinsa hakan zai girgiza zuciyarsu gimbiya zulfa, maybe su aikata abinda Muh'd zai iya farga dasu, ammashi sai rashin yardarsa ta tsiya ta hanashi aminta dake kanki. Gudun karta kwa6e agaba yasaka Muftahu zuwa ya sanarmin komai, yakuma fad'amin nagartarki data ahalinki, ya tabbatar min sai kowa yayi alfahari dake acikin masarautarnan, dansu suna ganin idan Muh'd ya auri y'ar talaka zai k'ask'anta bazaiyi sarauta ba, sun manta ALLAH shine mai komai da kowa. Muh'd yanada tausayi sosai Na tabbata inhar wani Abu ya shiga tsakaninku bazai ta6a sakinki ba, wannan dalilin ya sakani bama Muftahu pills ya saka muku, Dan ta wannan hanyar ne kawai zaku iya zama Abu guda”. Munaya da Galadima duk suka kalli Momma da mamaki, saikuma sukayi k'asa da kai saboda kunya. Murmushi Momma tayi. Tace, “Yes nice nabashi danna kafeku a waje d'aya, nakuma san Munaya zata iya bore akan ka saketa, shiyyasa a washe garin faruwar abin nasaka ka tilas ku taho nan, wannan shine mataki na biyu, mataki na uku saka Munaya tak'i kwantar maka dakai dannasan halinka da bak'in rashin yarda Muh'd, wannan na kula itakuma bata d'aukar saita kwana, shiyyasa abin yamin dai-dai, nadad'e da fahimtar son dakake mata, amma na shareka harsai ka gano dakanka ka fad'a mata. Cikin Munaya shine babbar ribar danaci, wadda nakema ALLAH godiya akowace dak'ik'a ta rayuwata, nake kuma jin k'aunarta har cikin jinina, badan na rabaku na rik'e Munaya ba, nayine dama danna tabbatar da nadamarka, itama ta kuma tabbatar da lallai da gaske kana k'aunarta, ta daina kokwanto a ranta, ALLAH yayi muku albarka, ya k'ara baku zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba, yabama Sauban mace tagari shima irin Munaya, itama Haneefa yabata miji nagari kamar mijinta daya bar duniya koma Wanda ya fishi, jikata Samha itama ALLAH yabata miji nagari Wanda zai rik'e mana ita”. Atare muka amsa da amin. Galadima zaiyi magana Momma tace, “kaga d'auka matarka ku tafi dare yayi, da safe ma k'arasa, nikam barci nakeji”. Kunya ta kama Galadima da Munaya, amma Momma saitayi tamkar batasan sunaiba. Tamkar munafukai haka suka mik'e sum-sum suka fice a d'akin, yanda basuyi yink'urin d'aukar yaro ko d'ayaba haka Momma bata tuna musuba itama🤣👍🏻...................✍🏻 *_Masoyan Raina kama amin afuwa dajina shiru, wlhy abubuwane sukaimin yawa, amma Alhmdllh yanzu nafara daidaita, kuma zanyi k'ok'arin gamawa nan kusa da izinin ALLAH, ina muku barka da salla baki d'aya, inakuma jiran naman layya😅🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀._* _wad'anda suka tura hoto kuma Na yafe muku wlhy har zuciyata, wancan write up nayisane lokacin raina a matuk'ar 6ace, yanzu kuma Na huce😅, nayi HAK'URI bisa koyarwar manzon ALLAH, Maman Haneefa ngd kema sosai ALLAH yabar zuminci, yakuma yafe mana baki d'aya, dama raina ya 6acine saboda bansan iya inda hotunan zasu kaiba, idan wani ya gani da k'yak'yk'yawar zuciya wani zai iya munanani ta mummunar hanyar dabanjiba ban ganiba, duk mace tagari bazataso pictures nata suke yawo a social media ba, musamman ma mai aure, kobaka da aure mace darajane da ita, saikuma mutunta kanka ALLAH zai kareka, masu ganin Abu kuna yad'awa jikinku Na rawa kubari wlhy, kokad'an hakan bashida k'yau, Dan kuma bazakuso hakanba, ALLAH ya k'ara mana hak'uri baki d'aya._👏🏻😘😘 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻 [8/22, 8:36 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* *_💡HASKE WRITERS ASSO...._* *_♦RAINA KAMA...!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ______________________ Gaisuwa da fatan alkairi.😘👌🏻 *_Takwara Billy Badaru, Maman Haneefa, Jameesha, my Hussy, my Dee.., Maman sayeed, Maman Sa'eed, Rahila Abba, Umman Murtala, lalai, Melerh zbi, Rally garba, Nana yakaku, Aysha Umar Abubakar, Aysha Galadima, Aunty Fareeda (ta group d'in Rano) Ameerah Ibraheem, xeecul, Bilkisu Ogun, Maman Mu'allim, zaujatu takwara Hussain 80k, Dan Mom._* Masha ALLAH akwaiku da yawafa my sweet sister's and brothers😅😘😘👍🏻 ______________________ *_BOOK 3_* 👉🏻2⃣7⃣ ....................Koda muka fito daga d'akin momma tamkar kwai ya fashemin a ciki haka nake tafiya, yana gaba ina binsa a baya, yayinda yafara taka steps d'in saiya juyo yad'an kalleni, k'asa nayi da kaina, yayi wani miskilin murmushi mai cike da ma'anoni, oho bansan yanaiba. A step d'in k'arshe ya tsaya yana nunamin hanya wai Na wuce, ra6awa nayi ta gefensa na shige, yanzu kam ina a gaba yana bina a baya buka shiga bedroom d'in, yana nan yanda Na sanshi cikin k'amshi da tsafta, Na zauna a saman sofa ina sauke numfashi. Tsaye yay kawai yana kallona, nikuma nakasa d'aga nawa idon Na kallesa, saima naji Na takura kallon dayakemin d'in. Kusan mintuna biyu sannan ya zauna a teble d'in dake gaban sofa d'in, ya kamo hannayena

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});