Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 25

Chapter 25

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

maganar da kwashewa da dariya. Dukda furucinsa ya daki zuciyar Galadima bai nunaba, saiya mik'e yana murmushi da kallon Darma. Yace, “lallai kaine ka cancanci ayima dariya, indai camera ce tadad'e da zuwa hannuna”. Yana gama fad'a ya fice, su Nuren suka kuma sanya dariya, dukda yanayin Galadima ya tabbatar musu akwai matsala. Sunama Alhaji Darma dariya suka fice abinsu daga d'akin. A falo suka iske Galadima yanata safa da marwa cikin tsantsar damuwa, sai danna waya yake yana sakawa a kunne alamar Neman wani tak'i shiga. Cikin sassarfa duk suka k'araso garesa suna tambayar lafiya?. Bai tanka musuba, saboda Munaya ta d'aga wayarsa, “Abba ya dawo kuwa?”. abinda kawai yace mata kenan. A tsorace tace, “Miya farune?”. Tsawar data rikitata ya daka mata, “ya ina tambayarki kina tambayata?”. Cikin in ina tace, “Kayi hak'uri, bai dawoba”. “ya salam” yafad'a cikin dafe kai. yace, “Kinyi waya dashi? Ko kinji wani yayi waya dashi?”. “A'a gaskiya, Jiya da safe dai nayi waya dashi nida Munubiya, amma yau ko innarmu banji sunyi wayaba.......” Cikin katseta yace “kinga maza bincikamin waye yay wayar k'arshe dashi a gidanku, sannan kuma awa nawa dayin wayar”. “Okay” munaya tafad'a tana yanke wayar. Shima wata Number yashiga nema yana fad'in “Lallai akwai matsala, tunda kukaji Harun da Alhaji Shehu sun fad'a to sunsan misuka shiryama Abba, gashi nabaza su Ameer sumin wani aikin...” ya k'are maganar da saka wayar a kunne saboda daddy ya kira. Bayan sun gaisa ya tambayesa ko sunyi waya da Abba a yau?. Daddy yace, “eh da asuba yakirashi akan zai dawo yau”. Galadima yace, “Alhmdllh Dady wace number ce?”. Dady yace bara Na turo maka. Koda Galadima ya yanke wayar saiya kira baba k'arami shima, shima ya tabbatar masa sunyi waya da Abba bayan fitowa salla, Dan wannan al'adarsu Ce ko a ina wani cikinsu yake saisunyi gaisuwar safe da bankwanan kwanciya barci, sannan idan wani cikinsu yayi tafiya zai kira y'an uwansa yayin dazai kamo hanya. Hankalin su Nuren ma duk a tashe yake, balle uban gayya Galadima.............✍🏻 🙆🏽Turk'ashi, ana wata ga wata kuma🤦🏻‍♀. Lallai yaukam tura na shirin kaiwa bango🤦🏻‍♀. *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭👏🏻_* [8/1, 2:06 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* *_💡HASKE WRITERS ASSO...._* *_♦RAINA KAMA...!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* __________________________ *_Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, ya Ubangijin Al'arshi kama mahaifin takwara (Bily s Fari) rahama, ka yalwata kabarinsa da Ni'ima, ALLAH ka yafe masa, harda iyayenmu😭👏🏻_*. _Takwara ALLAH ya k'ara mana hak'urin rashinsu, muma ALLAH yasa randa zaka d'auki ranmu muna cikin masu imani da tsoronka, da soyayyay Manzonmu ANNABI MUHAMMADU S.A.W._😭😭👏🏻 ____________________________ *_BOOK 3_* 👉🏻1⃣5⃣ .................Duk da Munaya a rikice take haka tayi jarumtar danne zuciyarta, cikin hikima ta dinga bin jama'ar gidan d'ai-d'ai tana tambayar wad'anda tasan Abba zai iya kira kai tsaye, amma kowa yakance tun daren jiya basuyi wayaba, hankalinta a tashe ta sulale gidan innaro ba'a saniba, itama dai tace tun bayan sallar asuba bai sake kiranta ba. Munaya tafito jikinta sai rawa yake, kiran Galadima tayi, lokacin yana waya, tamkar zata fasa kuka ta cire wayar daga kunnen ta, tana niyyar sake kiranshi saigashi ya kirata. Da sauri ta d'aga. Yace, “yauwa Yayi waya da wani?”. Muryarta na zuga alamar tahowar kuka tace, “A'a, innaro kawai ya kira bayan sallar asubahi, amma yau koda su innarmu baiyi wayaba”. ta k'are maganar hawaye na gangarowa a kumatunta. Galadima ya furzar da huci daga can, a hankali yace, “Munaya”. Muryarta na zuga ta amsa tana share hawayen da bakin hijjab. Had'iye abinda ya tsaya masa a mak'oshi yayi da k'yar, muryarsa takuma komawa can k'asan mak'oshi, cikin sigar lallashin da Munaya bata ta6a sanin galadima ya iyaba yace, “insha ALLAH babu abinda zai faru da Abba, kiyi mana addu'a, sanan karki sanarma kowa wani Abu har inna, wayarki tazama kusa dake, Dan zan dunga kiranki idan buk'atar hakan ta taso”. Munaya takuma goge hawayen dasuka gaza tsayawa, cikin had'iye kukan tace, “ALLAH yabaku nasara, ya tsareku da tsarewarsa”. “Amin ngd”. Galadima ya fad'a yana yanke wayar. A bakin fanfo Munaya ta tsaya ta wanke fuskarta, akuma lokacinne Zarah da Siyama suka shigo kusan lokaci d'aya. d'agowa nayi Na kallesu ina k'ak'aro murmushin da musu sannu da zuwa. Saidai ayanda suka amsamin cikin sanyin jiki saina tsorata, nabaro bakin fanfon da hanzari zuwa garesu ina fad'in “Kai lafiyarku kuwa?”. Duk d'insu murmushi suka k'ak'alo, Siyama tace, “babu komai fa sis...”. Dukda ban yardaba haka nayi murmushi, sannan Na kar6i yaransu duk biyu Na rik'e ina yaba Girman da sukayi, saikace tagwaye. Daga Siyama har Zarah basuce dani Uffanba duk suka shige, kowa tanufi d'akin Uwarta. Duk binsu nayi da kallo, saida suka shige Na sauke ajiyar ziciya nima Na nufi sashenmu Ina tunanin mike faruwa? Dan alamu sun nuna akwai dai wani Abu a k'asa. Saidai bankai ga Shiga d'akinmu ba mamansu Yaa hameed ta tareni ta kar6i yarinyar Zarah. Ban musaba Na bata tundai ALLAH yasa Nima Na Haifa balle ace, na shige falonmu da d'an Siyama nima. Bayan Galadima sun gama waya da Munaya, number da daddy ya turo masa ya duba, ganin wadda yake da itace saiya gwada kira, switch up, ya ciza lips yana kallonsu Nuren da suma duk suka zuba masa idanu. Muftahu yace, “Ranka ya dad'e mu sanarda y'an sanda mana?”. Murmuahi takaici Galadima tayi, ya girgiza kansa yana fad'in “Hakan zai 6ata aikinmu, duk indama yake a safiyar yaune suka sameshi, akwai zoben dake hannunsa zamu iya bibiyarsa tanan, saidai matsalar d'aya dole sai wayarsa Na aiki, gashi number sa kuma switch up”. Nuren yace, “to mizai hana mu bincika kozamu samu daga inda Number tabar aiki”. Da sauri Galadima yace, “yes, yes Nuren, shawara mai k'yau.....” Shiru yay yakasa k'arasawa, saboda tuno da matsalar da Computers nasu suke ciki kuma, ya dafe kansa. Daga Muftahu har Nuren duksun fahimceshi, zuwacan kuma miya tuna saiya mik'e da hanzari zuwa cikin d'akin, babu dad'ewa yafito dawani k'aramin abu a hannunsa, lap-top yajawo ya manna a jiki, ya had'a da waya ya Shiga sarrafata cike da kwarewa. Zuwa can yad'ago yana kallon su Muftahu da tura musu lap-top d'in gabansu, yana sanar dasu titin da wayarsa ta daina aiki. Cikin takaici yace, “Sunriga da sun tsara komai, mubarma tunanin plan A, muje zuwa plan B kawai”. Cikin mamaki duk suka kallesa alamar miye plan B d'i?. Lips d'insa yad'an ciza yana d'age gira d'aya da buga yatsan saman bakinsa, Yace “maida hankalinmu a nemansa shine target d'insu Na farko wajen janye ra'ayinmu, plan d'inmu mukuma anan shine bazasu ta6a kasheshi ba inhar bai basu Camera d'inba, a yanda Na lura kuma yanada taurin kai shima, bazai ta6a basuba ko fad'a musu inda take. Sunada damar yin amfani da surukan senator halluru wajen turasu gida su nema musu camera d'in, kodai ta hanyar musu barazana da mutuwa, kokuma akan aurensu, ko kashe mahaifinsu, kodai wani Abu daban, shiyyasa dolene mumaida matsalarsa cikin plan B d'in”. Duksun gamsu, dukda sufa har yanzu yak'i sanar musu miyake shiryawa a plan B d'in. Cikin damuwa Nuren yace, “Amma nasan zasu wahalar dashi”. Galadima baice komaiba dan shikad'ai yasan azabar da zuciyarsa kemasa, bayason ya nuna karayarsane saboda karsuma su Muftahu su karaya, sannan koda sanyin jiki yanemi tasiri gareshi sai kalaman Munaya su masa allura, inhar yarinya

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});