Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 77

Chapter 77

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yayinda girman Innarmu yakuma yawaita a zukatansu. Mun dawo da kwana hud'u Aunty Salamah da Badeerah matar Yaa Fadeel suka sauke, babu nisa tsakaninsu Farhat d'in Nurenma ta juye, Saiga Samha ma ta haife yaranta y'an biyu duk mata, hakama matar Matawalle. Kai wannan abun dad'i da yawa yake, munsha shagulgula sunan kam babu k'arya. A lokacin ne kuma Galadima yafara k'orafin na yayaye su Abdurrahman wai kona samu nima. Dan gatan da ALLAH yay mana ni da Munubiya muna jerin mata da al'ada ke d'auke musu bayan jinin bik'i har sai sun yaye, amma nasan murzar da Galadima ke min da tuni k'ila ciki na uku na d'auka🤭🤣. Yanzuma danake kwance a jikinsa dariya kawai nayi. Nace, “su Abdurraheem basu gama yin k'wariba my king, inama laifin sud'anyi 4years haka?”. Harara ya zubamin da fad'in, “yarinya kinma isa, insha ALLAH gab kike da d'aukar wasu ukun”. Bance komaiba sai dariya da nayi ina sumbatar goshinsa domin kauda zancen, dan inhar yay zurfi zai zama rigimar da muka sabane kawai, nikuma bana buk'atar hakan. ★★★★★★★★★ Rayuwa ta cigaba da gungurawa dai-dai gwargwadon iko, yau da dad'i gobe babu, soyayya nida mijina ba'a magana. Shekarun Abie biyu kenan da dawowa cikin ahalinsa, yayinda kunnen kowa na masarautar gagara badau yake a bud'e dan sonjin makomar sarautarsa. Saidai kuma tsit babu wani bayani. Yay shiri yaje har prison wajensu Harun jikin su Alhaji Mansur yayi sanyi matuk'a, Wanda sukaso ya k'are rayuwarsa tamkar gawane a gabansu, lallai duk saurin Bawa da son nuna k'arfin iko sai ya jira ALLAH, Abie baice dasu komaiba ya juyo ya fito, shiruma maganace ga mai hankali. A 6angaren mai martaba sunata fafatawa ne shida mama Fulani tun dawowar Abie, yanason tado da maganar sarauta amma mama Fulani ta kasa ta tsare, ta hanashi. Yayinda gimbiya zulfah keta k'ulunboton asirce-asirce agefe dan kar mulki ya koma wajen Abie, duk da batada wata fawa a masarautar yanzu, saboda tunda wancan abun ya faru mai martaba ya hanata shiga turakarsa, babu kuma wani Abu dayake mata a matsayin matarsa, bai kumace ya saketa ba, dan kowa yasan Sarki a k'asar Hausa baya saki, saidai idan mutuwa ta raba. Da farko tashiga damuwa tamkar tayi nadama, amma dawowar Abie saita kuma birkicewa, musamman da Matawalle yay aure matarsa kuma ta haifi mace, duk zugarta dason 6ata Galadima a wajen y'ay'anta Matawalle baya d'auka, saima yakuma kusantar Galadima suka d'inke waje d'aya, su wambai ne dai ma sai kuma rura k'iyayyarsa suke a ransu, har Momma da Abie haushi sukeji, duk da jansu a jiki da sukeyi a banza, uwarsu da mama Fulani sun rigada sun hure kunnuwansu. Ganin abin zai kwa6e mai martaba ya shirya taro na manyan masarautar, harda gayyar papi Wanda ayanzu shima lafiya take Neman yimasa k'aranci, saboda girma, dan yanama shirye-shiryen yin murabus ya d'ora mahaifinsu Nuren. Mama Fulani batasan da wannan taronba ko kad'an, dan mai martaba bai nuna mataba ko da a fuska. Galadima na kwance a tsakkiyar falonsa yana wasa da yaransa daketa hawa jikinsa yana musu doki, ni dai ina gefe zaune ina danne-danne a laptop. Nakan kallesu nai dariya idan sukai masa wani Abu. Wayarsa dake kusa dani tayi ring, d'auka nayi na mik'a masa, ya sauke Amaturrahman dake saman fuskarshi yana duba wayar, ganin mai martaba sai ya mik'e zaune sosai yana musu alamar suyi shiru. Duk da ba wayone dasuba yariga ya koya musu hakan, duk kuwa sai suka rik'e bakinsu. Ni dai dariya nayi kawai na kauda kaina. Galadima ya amsa kiran cike da girmamawa. Yana yanke wayar ya mik'e. Kallonsa nayi da mamaki, “My king lafiya kuwa?”. “Duk'owa yay ya sumbaci goshina sannan ya zauna a hannun kujerar da nake zaune. yace, “Mai martaba ne ke buk'atar ganina wai yanzunnan”. “Tofa ALLAH dai yasa lafiya?”. “To amin, bara na kimtsa naje naji”. Na amsa masa da to. Yaran duk suka mik'e zasu bishi na kamosu ina lalla6arsu. “Haba my sweetness kuzo kuji, Abbu wanka zaiyi kunji”. Abdurraheem ya kwa6e fusaka zaiyi kuka, danshi duk yafi sauran y'an uwan k'ulafucin uban, ko barci yake Galadima yay magana saiya farka, gashi bashida yawan kwaramniya, yanda Amaturrahman da Abdurrahman zasu saki jiki suyi wasa Abdurraheem bayayi, idan har Galadima na gida to yana manne dashi. Koda ya fito zai tafi sai suka sanya kuka, lalla6asu yayi yay musu wayo ya gudu, amma Abdurraheem saiya saka kuka harda shashsheka yana shid'ewa, dole Galadima ya dawo da baya ya d'aukesa suka fita. Nikuma naita lallashin su Amaturrahman har suka saki jikinsu kuma. Abdurraheem yana ganin Abie sai kuma ya mak'ale masa, ya d'aukesa ya d'ora a cinya yana murmushi. 'Dakin taron yayi tsit kowa yana sauraren Mai martaba. Cikin nutsuwa da halin dattako yafara jawabi kamar haka. “Inama kowa fatan alkairi, nasan kowa zaiyi mamakin wannan taro na gaggawa, wasu dalilaine suka saka yinsa tilas, tun bayan kama mutane da suka cutarmin da d'an uwa babu wani zama da mukayi ko magana akan wannan matsalar, duk da kasancewar akwai namu mutane a ciki, waziri da d'ansa, da kuma sirikina, sai mahaifin mahaifiyata wato kakana kenan, tabbas abune da musalta bak'in cikin da mukayi 6ata lokacine, amma mun tura komai ga Ubangiji ya musu hukunci dai-dai da yanda suka aikata mana, a kullum kuma cikin yaba k'ok'arin d'anmu mukeyi bisa ga jajircewa akan tonuwar asirinsu, ALLAH ya albarkaci rayuwarsa da ta zuri'arsa, akwai wad'anda suka bashi taimako sosai, amma bamuyi musu komaiba. Bawai mun manta dasu baneba, sunan cikin zukatanmu. To a yanzu dai mak'asudin zamanmu anan shine inason maida sarautar dake kaina ga d'an uwana, tunda ALLAH yabashi lafiya, sai a d'ora daga inda aka tsaya”. Cikeda mamaki Abie ya kalli mai martaba, cikin Dakatar dashi ya d'aga masa hannu yana 6ata fuska. Sannan ya yunk'ura ya mik'e yana mik'ama Galadima Abdurraheem dayay barci, har yanzu bawai ya dawo normal bane, da taimakon sanda yake tafiya. Yace, “Ku gafarceni bisa katse hanzarin d'an uwana danayi, maganar gaskiya bazan kuma wani mulkiba, akwai iyayenmu anan yakamata su dubi lamarin bisa ga idon basira, har zuwa yanzu bawai lafiya Ce ta gama isataba, saidai muce Alhmdllh domin Ubangiji yamana dukkan Ni'ima, ai ko lafiyata k'alau zan iya sauka a wannan shekarun nawa na bashi dama, munyi maganarnan ni da shi nace yabarta anan, amma saida ya kawota, to wlhy, wlhy kunji dai na rantse ko, bazan sake hawa karagar mulkiba, kwanan nanma nake shirin komawa India ni da iyalina, dan ALLAH wannan maganar ta tsaya iya haka, karmu sake jayayya a kanta”. Shiru kowa ya kasa motsi, domin wannan rikici yazama na manya, hakanne ya saka papi mik'ewa ya sallami kowa, ya rage daga shi sai mai martaba da Abie a d'akin taron. *********** Na fito wanka na iske Galadima zaune a bakin gado hannunsa dafe da kai, da sasaarfa na k'araso dan nasan akwai matsala kenan, musamman da acikin y'an watannin nan sau biyu ciwonsa na tashi, duk da akowane bayan watanni uku sai munje India ganin likita shida Abdurraheem, dayake yanzu hankalinsa yana nan Nigeria akan Company da suketa k'ok'arin ginawa, zuwa India saiya zame masa sai time to time kokuma wani gagarumin Abu ya taso daya zama tilas saiyaje. Laimar ruwa da yaji a jikinsa ya sashi d'agowa da hanzari ya

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});