Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 27

Chapter 27

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,209 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Yana yanke wayar nafito, cikin dabara nashiga d'akin innarmu, key d'in d'akin Abba Na d'akko, dukda nasan kowama yana dashi cikin matansa, fitowa nayi naje cikin dabara da sauri-sauri Na saka key d'in cikin k'ofa d'in, cikin addu'ar Neman nasarar kozai karye a ciki, amma ko gezo baiyiba, hannuna sai azabar zogi yake, danma nayi amfani da wani abin sarrafa k'arfene, cirewa nayi nakoma ciki kozan samo wani k'aramin k'arfe dazai iya Shiga, saida nasha wahala nanma sosai kafin Na samo, gashi duk a tsorace nake kar wani ya fahimci abinda nakeyi, cikin kafar makullin Na turashi, Alhmdllh nasamu ya shige, nagwada saka key amma yak'i Shiga, nasan babu yanda za'ayi wani key ya sake shiga wajen harsai mai gyara yazo, tunda kuma Abba bayanan ai babu buk'atar hakan, Dan duk wanda zai buk'aci shiga yanzu lallai akwai manufa. Dukda haka saida nasamo kwad'o nakuma sakawa sannan hankalina yad'an kwanta. ************************** *_9:00pm_* Fitowarsa kenan daga wanka baiko tsaya shafa mai ba ya hau shiri cikin wandon da riga k'ananu, fuskarnan babu alamar walwala tattare dashi, komai yana yinsane cikin karsashin fushi da damuwa, ya kammala tsaf yad'an saka turare. A k'ofar sashensa ya iske Nuren yana jiransa, sauran Hadeemansa dabasuyi barciba suka shiga masa barka da fitowa, kansa kawai ya d'aga musu, d'aya daga ciki ya bud'e masa bayan motar, amma sai bai shigaba ya d'aga masa hannu ya bud'e gaba da kansa ya Shiga, Nuren yay murmushi kawai, yasan yau mazan a wuya suke. Shiga yay shima mazaunin driver yaja suka fice. Gidane matsakaici sabo, dagani ko dad'ewa da gama gininsa ba'ayiba, saidai anzuba komai Na amfanin gida, ahaka suke buk'atar badashi haya. Dan haka da saleem yanemi hayar suka bashi kai tsaye. Suna isowa Muftahu ma ya iso d'auke da su Harun, Alhj Darma, Farhat d'iyar Minister sai mal. Saminu driver Alhaji balala, kusan shima yana hannunsu har yanzun. Ameer ya mik'e da Sauri yana salute d'in Galadima, hararsa yayi, Ameer yay murmushi yana yin k'asa da kansa. Cikin girmamawa yace, “Ranka ya dad'e wad'annan sune phones d'in yaran da tarkacen kayamsu”. Jinjina kai Galadima yayi, hannunsa duk biyu goye a bayansa yana zagaya table d'in da aka zube wayoyi, da lap-tops, iPad's dukna wad'anda aka kawo d'in, ya kalli Ameer cikeda k'asaitarnan tasa yace, “Suna INA?”. “Duk suna sama ranka ya dad'e, Dan inaga yakamata kazauna acan, danka ke ganin motsin kowa daga waje, dukda ansaka cctv a ko ina na wajen”. Galadima ya kad'a kai alamar gamsuwa da bayanin Ameer. Cikin takunsa na izza da lafiya ya nufi saman benen dake gidan, Muftahu da Nuren suka kalli Ameer cikin neman k'arin bayani, murmushi yamusu, yana tattare wayoyin yabi bayan Galadima dasu. A k'aramin falon k'asan ya iskeshi tsaye yanabin komai da kallo, Ameer yace, “ranka ya dad'e yazamuyi da wad'annan phones d'in nasu?”. Galadima yad'an ciza lips yana kallon Ameer, yace, “inasu Nuren d'in?”. “Suna k'asa”. Galadima baice komaiba, hakan da yayi ya saka Ameer fahimta su shigo kenan, saiya ajiye abin hannunsa ya sauka k'asan Dan kiransu. Saleem yafito daga wani d'aki ya taso k'eyar wani matashin Saurayi k'yak'yk'yawa, daka gansa kasan hutu yagama ratsashi, kallo d'aya Galadima yamasa ya d'auke kansa, Saleem yaja kujerar dining d'aya ya zaunar dashi, sannan yasaka igiyar daya d'auka ya d'auresa jikin kujerar, saurayin sai zaginsa yakeyi, amma Saleem ko kulashi baiyiba, saida yagama tsaf sannan ya kalli Galadima, wata alama yamasa da ido. Sai kawai naga Saleem ya d'auke saurayi da wani shegen mari, Wanda yasaka su Nuren dake shigowa jan birki suna kallon Saleem, bakin saurayi bai mutuba, Dan haka Saleem yakuma zuba masa wani har hancinsa Na fashewa, azaba ta sakashi kama bakinsa yay shiru yana huci da had'iye hawaye. Galadima ya ta6e baki yana d'age kafad'a. Alamar sudai suka sani. Haka Saleem yayta fiddosu d'aya bayan d'aya harsu 7, maza 5 mata 2, sai Farhat cikon ta takwas, amma su matan babu wacce aka d'aure, mazanma idan har bakayi gardama ba ba'a ta6asu. Saleem yagama jerasu reras gaban Galadima daya d'ora k'afa d'aya kan d'aya cikin kujera yana danna lap-top hankali kwance. Muftahu da Nuren dai sunyi mutuwar zaune, basu ta6a tunanin Galadima zaibi wannan hanyarba, gashi yak'i basu wata fuska dazasu masa magana ko tambaya. Saleem da Ameer suka kamo Harun shima aka d'aureshi a gefe ba cikin yaranba, shi baima cikin hayyacinsa, Dan su Nuren saida suka shak'a masa Abu, Alhj Darma da m. Saminu ne kawai ba'a d'aureba, suma dai aka kawosu gabansa aka zube. Galadima ya d'ago yana kallon su Muftahu dasuka Gaza barin kallonsa, cikin ta6e baki yace, “kallonfa?”. Ajiyar zuciya suka saki a tare, Nuren yace, “Brother mufa bamu fahimtaba”. Lips yad'an ciza yana ta6e baki da fad'in “Duk wannan dalla-dalla d'in da akai muku?”. Shiru sukayi Dan inhar a fahimtarsuce dai yau sunzama Kidnappers Na gaskiya kenan🤭😂. Galadima yace, “Well, Ku ajiye zancen fahimta gefe, kuduba phones d'in su Wanda babu charge a saka, Dan zuwa safiya duk za a fara aiki dasu, daganan mai buk'atar barci yaje ya kwanta kawai, sauran aiki sai safiyar gobe”. Babu Wanda ya iya cewa komai, dan sunsan dai Galadima bazai sakasu a had'ariba saboda son zuciya, Ameer ya fidda Chargers suka saka dukkan wayoyi ajikin caji, Dan akwai wuta. A wannan daren Galadima ya tura sak'o ga dukkan iyayen yaran, lokacin duk sunbar wajen Abba sun koma gida, anbarsa da garadan samarinnan akan sai washe gari, Dan sun tsarama su Zarah duk yanda zasuyi. Babbar magana, Alhaji Mansur habibu Uba yana shirin kwanciya barci wayarsa tayi tsuwar shigowar sak'o, sharewa yayi, hakan kuma saiya saka matarsa a zargi, tatashi zata d'auki wayar ya hana, saita kuma tsarguwa, a zarginta wata shegiyarce ta turo masa, ganin ta fusata saiya bud'e sak'on. Babu shiri ya dirgo daga gadon a tsorace yana tambayarta ina nerh-nerh take?. Da mamaki race, “batace ta sanar maka zataje wajen Rahma ta kwanaba?”. A rikice yace, “Rahmar ubanwa, maza kiramin ita yanzunnan su Abubakar suje su d'akkota”.. Bata fahimci inda ya dosaba, amma rikicewarsa saiya sakata d'aukar waya ta kira nerh-nerh d'iyarsu, wayar na Shiga amma ank'i d'agawa, cikin tsantsar tashin hankali ta sanar masa, ya daka mata tsawa yana fad'i “ki kira Rahma d'in ko wani d'an gidansu mana!!”. Maida akalar kiran tayi kan Rahma, itama dai ank'i a d'aga, bataso kiran Hajiya yalwa ba, dan atunaninta kota kwanta, amma dole ta kiratan. Hajiya yalwa Na zaune kusada mijinta Alhaji Abdul-Naseer Nafi'u kiran ya shigo, tayi mamakin Kiran, Dan hajia Marya bata kiranta a irin wannan time d'in, saitayi tunanin ko takasa hak'urine da rashin nerh-nerh abinka ga auta. Cikin raha tayi picking tana nunama mijinta wayar da baki, yay y'ar dariyarsu ta manya yana kuma kishingid'a da zubama matar tashi idanu. Tambayar da Hajiya Marya tama hajiya yalwa ce ta rikitata, ta mik'e zumbur tana fad'in “bara Na duba to, Dan wajen 3pm suncemin zasuje zaga gari, amma 7 zasu dawo gida, to wlhy bak'i mukayi suka d'auke hankalina nikuma ban nemi ganinsuba, tunda ina tunanin sundawo suna sashen Rahma”. Duk kiranda Alhaji Abdul-Naseer kema hajiya yalwa batajishiba, hakan ya sakashi biyota. Kusan atare suka iso sashen Rahma d'iyarsu, y'an aikinta guda biyu Na zaune a falonta sunata gyangyad'i, kai kace sashen wata mai aurene ba budurwa

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});