Chapter 56
Chapter 56
ma barci yakeyi, mura ke damunsa, amma bara Na duba ka shigo”. Cikeda tausayawa Muftahu yake fad'in “Kai aikam mura Na wahal dashi sosai Idan ta damk'esa, shiyyasa bayason zuwa Nigeria lokaci irin wannan Na sanyi, aini banga ta shigaba, bara naje muzo da doctor jalal daganan nasamo muku abinda zakuci, yanzu haka yinin yau baici komaiba”. Godiya namasa ya juya ya fita, nikuma na nufi k'ofar falonsa. Tun a falon na tabbatar mai d'akin babu lafiya, Dan komai a kashe yake har AC, Wanda inhar yana gidan AC yini yake yana aiki, koda uake akwai sanyi yanzu, shi ko damunsa bayayi ma, Na k'arasa k'ofar Bedroom d'in, harna kai hannu zanyi knocking kuma saina fasa, tura k'ofar nayi a hankali da sallama Na shiga, d'akin dund'um da duhu gashi bansan ina makunnar fitilar take bama ni, tsaye nayi ina tunanin mafita, na komane ko nayi magan...? Galadima dake kwance yau yini guda cikin halin ciwon kai da zazza6i, salla Ce kawai ke tadashi, abincima da k'yar ya had'a shayi yasha bayan sallar la'asar, tunda ta shigo yana jinta, saidai baisan wanene ba, shi a tunaninsa ma wanine yazo cutar dashi, jin anyi shiru ankuma k'i magana ya mik'a hannunsa da k'yar ya kunna fitilar dake dirowar gefen gadon. Baya nad'anyi kad'an danni tsoratama nayi, harma na fara zaton kobaya d'akin, sai kuma na nutsu waje d'aya ina kallonsa, yana cikin bargo ya lullu6e har kansa, janye bargon dake lullu6e da fuskarsa yayi yana kallona ta cikin d'an hasken fitilar. Idanu ya zuba mata cikeda mamakin yaushe tazo gidan? Ya ciro hannunsa daga bargon yana min alamar nazo. A hankali na cigaba da takawa, zuciyata cike da d'unbin tausayinsa, koba komai ta sanadina ciwon ya sameshi, na zauna a bakin gadon idona a kansa, hannuna ya kamo cikin nasa dakeda zafi alamar zazza6ine ma a jikinsa. Ina had'iye kukan daya tahomin nace, “Sannu, ya jikin?”. Idanunsa ya lumshe da cije lips. Na kama bargon zan yaye yakuma rik'e d'ayan hannun yana girgizamin kai, ahankali yace, “Sanyi”. Sannu na kuma masa, sannan na zare hannuna zan mik'e, amma saiya rik'oni da sauri, jiyowa nai ina kallonsa. Ahankali Yace, “Ina zakije?”. Badan ina kallon la66ansa ba dabama zan fahimci miyace d'inba, Dan banjiba. Dawowa nayi na zauna, nad'an matsa hannunsa, “zan had'a maka ruwane kasamu kad'anyi wanka, kaci abinci kuma”. “Zan daiyi wankan kawai?”. “Abincin fa?”. Kansa ya girgizamin alamar a'a. Kamar zanyi magana saikuma na fasa, tashi nayi na shiga toilet, dukda babu wani datti dai sai naga yakamata na wanke, na cire mayafin jikina na tsaftaceshi, na saka air freshener sannan na had'a masa ruwa mai d'an zafi ba canba dai, yanda zai masa dad'i. Zaune na iskeshi a bakin gadon ya dafe kansa, kallo d'aya namasa na d'auke kai, Dan dagashi sai boxer. “Ga ruwan na had'a”. 'Dago idonsa yay ya kalleni yana sauke hannunsa daya dafe kai, yanda tawani k'asa dakai kamar tana gaban surukinta, yad'an murmusa danshi kunyar nan tata birgeshi take. Duk saina takura da kallon dayakemin, gashi kunyar motsawa nake daga wajen, Dan sket d'in jikina ya kamani sosai, maganarsa Ce ta katsemin tunani. Na d'ago ido naimasa kallon fisha na janye ina fad'in “Towel?”. “Uhumm”. Kawai yace yana cigaba da kallonta. Ahankali na dunga tafiya saikace wata mai tatata, Dan inaji a jikina kallona yakeyi har yanzu, saida na d'akko gyalena dake jikin k'ofar bayi na yafa sannan na d'akko towel d'in. Duk abinda takeyi idosa na kanta, towel d'in da hannunna ya had'a ya rik'e, na kallesa fuska a marairaice ina f'ad'in, “karfa ruwan ya huce yalla6ai”. Ya zubamin jajayen idonsa ga jijiyoyin kansa sunyi rad'a-rad'a, baice komaiba ya zare towel d'in ya yafa a jikinsa yana mik'ewa da k'yar, saiya kuma bani tausayi, Dan na lura k'arfin haline kawai yakeyi. Bedsheets d'in saman gadon Na cire bayan Na kunna fitilar d'akin ya gauraye da haske, Na bud'e wardrobe d'in kayansa Na d'akko wani bedsheets d'in Na shinfid'a, Na share d'akin, banyi morping ba tunda darene, nasaka turare sanann Na fita. Yauce rana ta farko dana shigo kitchen da nufin dafama miji abu, sainakejin karsashi da alfaharin nimafa yanzu matar aurece tamkar kowacce mace, natashi daga matar Contract yanzu, wasu hawayen jin dad'i suka zubomin, nasa bakin mayafin Na share, a kayan da mukazo dasu Na ciri kayan k'amshi, ina d'auraye tukunya laraba ta shigo, juyowa nai ina kallonta. Tace, “ya jikin nashi?”. Ajiyar zuciya nad'an sauke. Nace, “da sauk'i iya, amma kwance Na iskeshi rijib ga zazza6i, zan dafa masa ruwan zafinne da d'an abinda zaici”. “ALLAH ya k'ara sauk'i, dama mura bata masa da sauk'i, dan yasha zuwa can yanayi kota sameshi a can, namiki karambani Na dafa ruwan zafin gashinan”. “Nagode iya, wlhy babu wani karbani, taimako dai, mun saki aiki ga gajiyar tafiya”. Dariya tayi tana gyara tsayuwa. Tace, “Aini gajiyarnan kam ta gudu, ras nakejina, kunedai dayake ba wahalar kuka saniba koyaya kuka motsa sai jiki yayta ciwo”. Nima dariya nad'anyi, ina cigaba da had'a komai akan k'aramin tire. Laraba tace, “To yanzu Yaya za'ayi kenan da abinci? Kinga dai ba'a barshi da yunwa ba?”. Nace, “Iya ga Muftahu can ya tafi samo masa abincin”. Tace, “To shikenan hakanma yayi”. 'Daukar tiren nayi natafi kai masa. Har yanzu bai fitoba, mamakin dad'ewarsa ta kamani, ajiye tiren nayi a k'aramin table glass d'in dake gaban gadon nima Na zauna ina tsumayen fitowarsa. Kusan mintuna 3 da zamana saigashi ya fito. Ban kallesa bama gudun karnaga abinda yafi k'arfina, kaina a k'asa ina wasa da stones d'in jikin mayafina. Shikam tunda ya fito idonsa Na kanta, ya zauna kusa da ita yana tsane ruwan fuskarsa zuwa kai da towel. Kallonsa nayi kad'an, ganin bathrobe ce a jikinsa saina samu nutsuwa. Da hannu yay min nuni da mansa, na mik'e Na d'akko, amma saiyak'i kar6a. Nad'anyi shiru da tunanin miyake nufi?... Katsemin tunani yayi da fad'in “Manma nizam shafa?”. A hankali yayi maganar, kuma fuska babu walwala. Ni mamakima yabani, amma to da banzo ba waye yake shafa masa?, bance komaiba na zauna kusa dashi ina zuba man atafin hannuna da mutsukashi, kunya tasa narasa dama ina zan fara?. Lura da hakan dayayi saiya mik'amin hannu kawai, banida za6in daya wuce cika umarninsa, anutse na shafa masa man dan banida yanda zanyi. Kaya na d'auka masa marasa nauyi, ya tashi zaune daga kwanciyar da yayi ya saka, nidai kauda idona nayi gefe harya gama. Natashi na had'a masa tea d'in da ruwan kayan k'amshinan, yana zaune akan sofa ya zubamin ido saikace wata television, dana mik'a masa mug d'in saiya had'a harda hannuna ya rik'e, da ido namasa alamar da zafifa cikin marairaicewa. Shima saiya min nasa salon da ido alamar da gaske. Nakuma narke fuska tamkar zanyi kuka, zame mug d'in yayi yana wani miskilin murmushi. Ya d'ora cup d'in akan bakinsa yana kallon yanda take tatta6a tafin hannunta, a ransa yace hajiyar tsiwa kenan, andawo koya kuma zamu kwashe?. Tea d'in yamasa dad'i, Dan saiya tuna masa da inno, itace kan masa wannan had'in inhar yana mura, yanasha yana kallona a k'asan ido, saika rantse kuma ba kallon nawa yakeba, amma ni inaji a jikina. Knocking k'ofar da akaine ya sashi kallon cctv, ganin Muftahu da Dr jalal sai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83