Chapter 34
Chapter 34
da Galadima kai tsaye”. Alk'ali ya bada damar hakan. Dandanan kuwa aka had'a Galadima da kotu, Wanda dama shi tuni yana ganin duk abinda sukeyi, sunedai basa ganinsa. Galadima dake zaune a falon gidan da yake tsare dasu harun ya mik'e tsaye domin girmamawa ga alk'ali, sannan ya gabatar da sunansa kamar haka, “ya mai shari'a sunana Muhammad Sameer Saifuddin Abubakar, ma'aikaci a hukumar bincike ta DSS”. Wani sabon kallon kallon aka koma, Wanda yaja hankalin mutane fiyema dana d'azun, hattada y'an masarautar gagara badau basusan da wannan aiki Na Galadima ba. Alk'ali ya kuma tsawatarwa, sannan ya maida hankalinsa ga Galadima yana fad'in “To Muhammad Sameer minene alak'arka da iyayen yaran dakake rik'e dasu, danmu ka rikita mana tunani, da farko kallon Criminal muke maka, saikuma gashi sunanka yafito a d'aya daga cikin manyan hukumominmu Na tsaro masu muhimmanci?”. Murmushi Galadima yayi yana gyara tsayuwa, ya hard'e hannayensa a k'irji yana sauke numfashi da cije lips, yace, “ya mai shari'a wannan labarine mai tsawo, amma tabbas abinda lauyana ya fad'a shine gaskiyar zance, Camera dake hannun Alhaji Auwal Fharuk itace babbar alak'ar dake tsakanina dasu, wadda nad'au tsawon shekaru akan nemanta, sai a shekararnan ne cikin watanni shida nasamu labarin inda take dukda banida tabbacin ita d'ince, bansan mike cikin camera d'inba, amma su Alhaji Balala duk sun Sani, tunda har suka iya salwantar da rayuka da yawa akanta, shi kansa Wanda suka hara a yanzu ALLAH ne kawai yasaka yanada tsawon rai, amma da tuni sun kasheshin, ni kaina rayuwata tasha hare-hare iri-iri harda jariran yarana da aka sace kwanaki 7 kacal da zuwansu duniya”. Alk'ali da yay shiru yana sauraren Galadima yaja dogon numfashi yana ta faman jinjina kai tamkar k'adangare yaga abinci mai manja😱🤭. Yace, “lallai wannan Court tana buk'atar jin cikakken bayani daga Muhammad Sameer Saifuddin, dan haka ta d'aga wannan k'ara zuwa nan da kwanaki uku masu zuwa, kotu tana bama y'an sanda Umarnin subar Muhammad Sameer Saifuddin ya fito daga wannan gida a ranar da Court zatayi zama Na gaba batare da koda masa hararaba, sannan kuma kotu ta bada Umarnin a cigaba da tsare su wad'annan mutane guda 11, likitoci kuma su cigaba da bama Alhaji Auwal Fharuk kulawa ta musamman dan shima kotu Na buk'atar ganinsa a zama Na gaba saboda son sanin mike cikin camera d'in”. Alk'ali ya buga gudumarsa yana mik'ewa. Gaba d'aya kowa ya mik'e har alk'ali ya shige. Galadima yay wani k'asaitaccen murmushi yana zaunawa cikin kujera bayan shigewar alk'ali. Muftahu, Nuren, dasu Harun dake zaune gefe suma suna kallon komai tun farkon Shari'ar duk sunyi mutuwar zaune tun lokacin da Galadima yafad'i kasancewarsa cikin hukumar C.I.D. Ameer ne kawai yay murmushi yana k'amewa da salute d'in Galadima. Shima baki sake su Nuren suka bishi da kallo suna nunashi alamar dama yasani shi?. Murmushi yay musu har hak'oransa Na bayyana ya had'e hannayensa waje d'aya alamar tuba a garesu. ★.....................................★ Yau kam Galadima wani farin ciki Na musamman ya tsinci kansa a ciki, ya shige d'akin da yake matsayin nasa a yanzu ya fad'a gadon yana rungume filo idonsa Na zirar da hawaye, ko a haka aka tsaya lallai yaci nasara, dan ya nunama su Alhaji Abdul-Naseer d'an zaki ya girma. Wayarsa dake saman gadon a can gefe yasa hannu ya janyo, ya kunnata, massages ne sukaita shigowa a jere-jere kamar jira, bai bud'e ko wanneba ya shiga binciko number Munaya, ya dad'e yana kallon Number amma ya kasa dialing, yaja wasu seconds kafin yatsansa ya sauka akan number ya danna kawai. Munaya Na zaune a falo tare da su Ayusher da kullum sai sunzo, d'an kunne ne ya shige cikin jikin Amaturrahman yanata cin jikinta basu saniba, sai yau da an ta6a fuskarta koyaya saita fashe da kuka, Munaya tarasa mike damun yarinya, dukta rikice ita kanta, saida laraba tace ta bata nono, tana kwantar da ita ta wajen kunnen sai takuma d'ad'ewa da kukan da Munaya ke jinsa har cikin jini, d'agota tayi tana duba wajen, Laraba tace, “Anya ba kunenta ke ciwoba?”. Munubiya dake kusada Munaya ta amshi Amaturrahman ta kifata a cinyarta tana dubawa, sai taga d'an kunne ne ya shige Ashe duk bayan kunnen yayi ruwa, tsoro ya kama Munubiya, cikin zaro ido waje tace, “innalillahi, d'an kunne natacin kunen yarinya bamu saniba”. Da an fara k'ok'arin ciremata saita kuma fashewa da kuka tana mimmik'ewa, gwaggo safiya data shigo yanzu saboda jiya ta iso akan abinda ya faru da Abba, ta k'araso cikin falon tana fad'in “mike faruwane?”. Bayani feena tai mata, gwaggo safiyya ta kar6i Amaturrahman tana cewar asamo mata ruwan d'umi da k'aramin handkerchief. Ana cikin hakane Galadima yayi kiran Munaya, tashitai tabar wajen tana had'iye kukan dake shirin taho mata saboda tausayin yarinyar. 'Dakinsu ta shiga, ta fad'a saman gadonsu ta kwanta tana amsa wayar. A hankali Galadima ya sauke ajiyar zuciya yana gyara kwanciya. Murya can k'asan mak'oshi yace, “babu fad'a miya kawo gaba yalla6iya?”. Murmushi Munaya tayi tana share hawayenta. Tace, “Kodai Kaine za'aima wannan tambayar?”. Jimm yayi saboda jin muryarta ba ayanda yasaniba. yace, “mike faruwa kike kuka?”. Mamaki ya kama Munaya, ta Yayama ya gane kukan take, cikin k'ok'arin kare kai tace, “ba kuka nakeba yalla6ai, ina yini”. bai amsa gaisuwarta ba yace, “kina wasa da sanin danai miki ko?”. Yay maganar cikin d'an kausasa murya. Munaya sai bataji dad'iba, tace “kayi hak'uri, dama Amaturrahman ce d'an kunne ya shigema a jiki taketa kuka, amma gashi can suna cire mata d'an kunnen”. Babu shiri Galadima ya tashi zaune yana fad'in “k ya akayi har d'an kunne ya ringa cin jikinta baki saniba? Anya kuwa kinason yarannan Munaya?”. Wani haushine ya kamata, tama rasa mizata Ce masa. Shima bai jira amsartaba yace, “maza ki tashi kuje asibiti a dubamin yarinya, karkuce zakuyi gangancin cire mata a gida wata matsalar ta biyo baya”. “Uhumm”. Kawai Munaya tace ta yanke wayar. Ta jefar da wayar gefe tana hawaye, shi kawai yaransane damuwarsa, harma zaice yafita sonsune dazai dinga jifanta da bata sonsu kulum-kullum, itafa wannan Abu yafara kaita bango wlhy. A can kuwa shima Galadima duk sai yaji ya damu, jiyake tamkar yay tsuntsuwa yafita yakai yarinyarsa asibiti da kansa, amma babu damar hakan. Ya dad'e jikin window tsaye yana kallon mutane daketa zirga-zirga a anguwa da police d'in dake zagaye da gidan har yanzu. Fita munaya tayi dan ganin ko ancire?, ta iske an cire ana gasa kunnen, Amaturrahman taci kuka harta koma ajiyar zuciya, Gwaggo Safiyya tace, “zoki zauna kibata tasha sai'a k'arasa gasawar”. Zuwa Munaya tayi ta zauna tana kar6ar Amaturrahman. K'in k'ar6ar nono tayi, sai ajiyar zuciya taketayi, Laraba tace, “yaranan zuciya irinta Magajin gari suke da ita, yanzu inba sa'a ba bazatashaba”. Dariya su Ayusher sukayi. Dak'yar dai Munaya ta turama Amaturrahman nono abaki ta kar6a. Akad'an kuma gasa kunnen dayay uwar huda naman wajen yafita sosai, k'ofar tazama babba. Munaya dake kallonta tasaka hannu tana goge mata zufar data taru mata a goshi, saikace wata babba. Galadima yanata kiran Munaya yaji kosun tafi asibitin amma bata d'agaba, dayake ta bar wayar a d'akinsu. Saida Ayusher taje d'akin ta gano, ta d'akko da sauri ta kawo mata tana saka mata a kunne. Maganarsa kawai munaya taji yana fad'an ina ta ajiye wayar. Ajiyar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83