Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 14

Chapter 14

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tambayata ba har shekaru sukaja, ganin girma ya kamashi sosai ya rok'eni na sanar masa daga ina na fito?, dan karya bar duniya da kokwanto a ransa, banyi nauyin bakiba na sanar masa komai. Yasha mamaki kwarai da gaske, dan suma labarin ciwon Sarki yaje musu, harma da nad'a k'aninsa da akayi ya maye gurbinsa. Shine yabani shawarar fara bibiyar masarauta kozan samu wani labari akan ahalina da jikin mai martaba, daga lokacinne nafara 6adda bamin shiga masarauta, na fahimci k'anwata ta auri wani bawa, matata ALLAH yamata rasuwa wajen haihuwar cikin dana barta dashi, d'an yayata data rasu itama ta bari shine k'anwata tacigaba da rik'o, a yanzu haka shine Wanda yazama direbanka Ranka ya dad'e, wannan shine abinda nasani ALLAH ya k'yautata rayuwarka, ya d'aukaki darajarka da mulkin masarautar gagara badau.” Daga Muftahu har Galadima ajiyar zuciya suka sauke, kowanne yana jinjina lamarin a zuciyarsa, shi dama baba Rabilu ya fad'a masa kafinsuzo, kafin Galadima ko Muftahu su sami damar magana baba Rabilu ya fara fad'in “Lallai kamar yanda na sanarmaka randa nazo gareka ranka yadad'e d'an uwanane shi wannan daya bada camera d'in, da ni da shi duk aikinmu d'ayane, bayan yakai wannan camera ga mahaifin Badi, gidana ya zarto, amma saiya iske ban dawoba sai iyalina kawai, yabar musu sak'on wasik'a da address d'in inda zan sameshi, wato k'oramar bakin gari inda shi Badi ya gammu, inayin sallar asubahi kuwa na nufi wannan wajen dan ya rubutamin Cewar yana cikin mawuyacin hali, yana tsaka da fad'amin abinda ke faruwa saiga wad'annan mugaye sun biyomu, bansan a ina sukaji muna canba, na gudu ne a tunanina shima Habu ya gudu, Ashe sun kamashi, saida na fara jiyo sautin muryarsa dake amsa kuwwar karmu tsaya mu gudu, badan nasoba na gudu nabar Habu a hannunsu, wasu a cikinsu sun cigaba da bina, amma wani mai lambu ya taimakeni ya 6oyeni, kwanana biyu a cikin lambun, saida mukaga komai ya d'an natsa sannan na fito Na koma gida, duk tunanina ai basu ganniba, shiyyasa nacigaba da y'an hidindimuna domin 6adda kama, a 6oye kuma na shiga binciken wanda Habu ya bama Camera d'in, dan ya gayamin tana masarauta wajen mai kula da barga, Labarin mutuwarsu tazomin shida matarsa a bisa bincikena, saidai a masarauta ance d'ansu Badi shine ya kashesu, Sam ban aminceba, wannan ya sakani Neman Badi domin na kar6i camera d'in hannunsa, inada tabbacin shine Habu ya sanarmin cewa gashi can alokacin da mutanen nan suka iso, saidai kallo d'aya namasa muka fara gudun tsira, daga nan kowa ya kama tsaginsa. Dole na ajiye aikina saboda tsaro, na kawo rigar siyasa na sanya dan nema ma kaina girma, shekarata 6 a rigar siyasa akayi yunk'urin kasheni, ba kowa bane da wannan aikin face Alhaji Shehu Adamu Darma, har gidana ya saka aka satoni, nayi mamakin ganinsa, dan jam'iyyarmu d'aya, wani sa6ani bai ta6a shiga tsakaninmu ba, dan haka na nemi dalilin sanin miyasa zaisa a d'akkoni cikin iyalina? bayan mu y'an jam'iyya d'ayane. Ya kwashe da dariya yana nunani da fad'in lallai Alhaji Rabilu fanisau bakada hankaki, a tunaninka dukkan 6addamin da zakayi bazamu ganoka ba? yanzu dai dukma ba wannanba, ina camera?. Nace wace camera kuma? Wani wawan duka yaronsa yamin, na dafe wajen saboda azaba, Darma yakuma cemin ina camera d'in da Habu idris ya bani? nanma na sanarmasa ban saniba, wannan ne yasakashi kar6ar k'arfe ya kwad'amin a kai saboda haushi, daga nan na fad'i a wajen, ashesu duk sun d'auka a lokacin dukna mutu, shiyyasa suka jefar dani gefen hanya suka tafi, wani bawan ALLAH ne ya d'aukeni yakai asibiti, abinda yasa su Darma basuji labarina ba wanann mutum ba d'an nan yankinmu baneba, fataucine ya kawoshi, daya d'aukeni kuma saiya bar nahiyar wannan yanki dani gaba d'aya, nayi jiyyar shekaru biyu, kafin na dawo dai-dai, duniya sukta d'auka na mutu, saida na d'au shekaru bakwai banzo wannan yankinba, dan bawan ALLAHn nan yazo har nan ya kwashe iyalaina ya kaimin, bayan yamusu bayanin dazasu fahimta, bayan shekaru bakwai nakanzo nad'anyi bincikena na koma cikin 6adda kamanni, a wannan yanayinne na farga da Badi, ban sanshiba gaskiya, amma ganin yanayinsa tamkar mai lek'en asiri shine na fara bibiyarsa harna fahimci wanene shi, hakama waziri da d'ansa, na lura kullum cikin bin diddigin yalla6ai Galadima suke suma, nima wannan abun shine abinda na sani, kunji dalilin Darma na kirana Fatalwa”. Galadima da Muftahu sunyi shiru cike da tsabagen rud'ani da al'ajabi, da k'yar Galadima ya iya bud'e baki cikin muryar tsananin damuwa yace, “waishin minene a cikin camera d'in nan? Yanzu kuma wanene ke rik'e da ita?”. Baba Rabilu yace, “Duk wannan muke son sani ranka ya dad'e, yanzu haka muna kan neman wanda badi yabama wannan Camera, dan na sanar masa har yanzu batazo gareka ba”. Galadima ya sauke ajiyar zuciya yana cije lips, idonsa yayi jazur, ya kalli Muftahu sannan ya kalli Badi dake zaune kansa a duk'e, “Badi yanzu idan ka gansa zaka iya ganesa kenan?”. “insha ALLAH ranka ya dad'e zan iya, saidai idan har ya mutune, bakuma ma fatan hakan”. Shiru dukansu sukayi kowa na nazari, Galadima sai ajiyar zuciya kawai yake saukewa, shi kad'ai yasan mi yakeji, ya kalli Muftahu yana fad'in “Sarkin mota ya shigo, dan nasan baisan matsayin Badi a wajensa ba”. Muftahu ya amsa da “to ranka ya dad'e”. Cikin y'an mintuna saiga Sarkin mota tare da Muftahu sun shigo, a k'asa ya durk'usa yana musu sannu, Galadima ya kallesa yana nuna masa Badi, “kasan wannan?”. Badi da Sarkin mota suka kalli juna, a lokacin ne Muftahu da Galadima sukaga kamannin su, saidai shi Badi tsufa ya 6oyesa kad'an. Ganin sun shagala da kallon juna kowa yakasa magana sai baba Rabilu ya katsesu da fad'in “Badi kamasa bayani mana”. Dattijo badi ya kamo hannun Sarkin mota kusa da shi, yana zubda hawaye yace, “matso gareni Yunusa, nine babanka yayan mahaifiyarka, Badi ya rungume Sarkin mota suka fashe da kuka, a haka yake bashi labarin alak'arsu. Saida kwalla ta cika idon Galadima, hakanne ya sakashi tashi ya fice daga falon, Muftahu da tausayinsu ya kamashi shima ya bi Galadima da hanzari. A tsaye ya iskeshi ya tsurama flowers d'in da akama gidan ado dasu ido, hannayensa biyu duk cikin aljihu, gaba d'aya bugun zuciyarsa ya fara canjawa, sai had'iye yawu yake da k'yar, wayarsa ya zaro daga aljihu, rasa wanda zai kira yayi, sai bin numbers d'in yake da idanu yana canki canka, ya tsansa dai ya sauka kan number Munaya......... ************************** Fitowata daga wankan yamma kenan Munubiya ta shiga, yau kwana biyu duk zuciyata babu dad'i, hakannan na tsinci kaina cikin 6acin rai, harzan fara shafa mai Aryaan ya shigo d'auke da Abdurrahman yana kuka, dole na ajiye man na kar6esa, na ta6a jikinsa da har yanzu zafin zazza6in daya yini da shi bai saukaba, saboda tunda asuba ya farka da kuka cibiyarsa na ciwo, kashinsa harya canja kala, saida innaro tazo tabashi magani sannan muka samu nutsuwa, daga nan kuma sai zazza6i, shine har yanzu nake d'an jin jikin nasa da zafi kad'an, nono na saka masa a baki kozai kama, dan duk yinin yau bai shaba, na sauke ajiyar zuciya ganin ya kar6a, ina shafa kansa idona na kallon fuskarsa data fara rikid'ewa

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});