Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 81

Chapter 81

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wataran a 6ata ma koka 6atama wani. Zuwa yanzu kam munyi rashin wasu daga cikin iyaye y'an uwa zuwa kakanni, ALLAH yayma Abbanmu rasuwa shida wasu matan gidanmu biyu, inno ma haka, yayinda innarmu ta gama takaba sai danginsu sukazo suka tattarata zuwa k'asarta ta haihuwa, muna kuka tanayi hakama jama'ar gidanmu da y'an anguwa, Dan bamason tafiyar tata, amma hakan gatane a gareta komawa cikin ahalinta, a gagara badauma kam mun rasa da yawa, tsohon Sarki jalaludden Abubakar ALLAH ya masa rasuwa sakamakon ciwon hanta, wadda ya dad'e da ita a jiki Ashe, wannan ma shine dalilinsa na dagewa akan Abie ya kar6a mulki. Saida rayuwa tazo gangara yake sanar ma Abie d'in Wanda shima zuwa yanzu girma ya kamashi sosai, Dan yatsufa komai ma sai an masa, danma ALLAH yabashi gwarzuwar mata Momma, dukda itama girman ya kamata bata gajiyawa da hidimarsa. Sarki Muhammad Sameer Saifudden Abubakar, adalin Sarki da talakawa ke alfahari da mulkinsa, musamman ma matasa da akullum cikin bin hanyoyin inganta rayuwarsu yake, suna zaune lafiya shida wazirinsa kuma d'an uwansa, babu wani y'an ubanci ko k'iyayyar juna, k'yawawan zukatansu sun sakasu kawo canji mai yawa a wannan masarauta, da farko su Talba ne sukaso kawo musu hargitsi, tunda suka fahimci haka sai aka sakasu barin k'asar tilas suda iyalansu, tun daga nan masarauta tadawo dai-dai. 6angaren Harun ma ya fito tun lokacin daya cika shekaru goma, amma bisaga karamci Na adalin Sarki Muhammad Sameer saiyasa aka kawosa fada, yay masa hidima mai yawa, wadda ta sakashi kuka da gurfana gaban Sarki Muhammad Sameer Neman gafara da nadama akan abinda ya aikata, Muftahu da ayanzu yake rik'e da sarautar matawalle yay murmushi yanama Sarki Muhammad Sameer magana da ido akan ya yafe masa tunda yayi laushi, Sarki Muhammad Sameer ya jinjina kansa yana murmushin nan nasa Na k'asaita da cizar lips. Yafewar da Sarki yamasa Ce tabashi damar Neman gafara ga Uwargida Sarauniya Munaya itama, babu wani ja'inja tace ta yafe, ba'a barsa ya zauna masarauta ba, anmasa hidima mai yawa da aure aka sakashi komawa wata k'asa, Dan bawai kowa ya gamsu da tuban nasaba, ayanzu kuma Sarki da wazirinsa basa buk'atar duk wani mai ru6a66iyar zuciya a kusa dasu. Sarauniya Munaya uwargidan sarki mai fad'a aji a wannan masarauta, jarumar mace mai nagartacciyar zuciya, hamshak'iya wadda ayanzu tazama babbar mace jerin manyan mata sahun faro wajen dattako da mulki dama dukiyar itada y'ar uwarta Munubiya. A yanzu yaranta takwas a duniya, Amaturrahman, Abdurrahman, Abdurraheem, Abdul-fatah, Ai'sha, Zeenah, Saifudden, jalaludden Auta kenan, Ai'sha da Zeenah da suke kira da Safah da marwah tagwayene, bayan haihuwar Abdul-fatah tayisu suma, daga nan sai mai sunan Abie, dakuma auta takwaran tsohon Sarki babansu matawalle konace waziri, ayanzu kam duk sunzama manya, musamman su Amaturrahman da suke manya duk suna a jami'a, suna k'asar India tareda uncle d'insu Sauban da ayanzu shima yazama babban mutum, yazama babban d'an kasuwa bisaga jagorancin dukiyar d'an uwansa, yayinda su Aiyaan da Khaleel, Aryaan, Ahmad ke taimaka masa, kaga matasan samari abokan juna kenan, kansu ahad'e yake su hud'unnan, sune yanzu duniya ke yayi take son gani a fanin na'ura mai kwakwalwa wato Computer, Wanda ayanzu Abdurraheem da Abdurrahman suke k'ok'arin dannesu, Dan matasan samarin biyu sun zama magada kwakwalwa irinta mahaifinsu Sarki Muhammad Sameer suma. Itama Hafsat yaranta hud'u, biyu mata biyu maza, wad'anda duk suka taso a hannun Munaya, akwai zaman lafiya da k'aunar juna tsakanin Hafsat da Munaya mai birgewa, Wanda ya kawoma Sarki Muhammad Sameer kwanciyar hankali da k'yautata musu gwargwadon k'arfinsa, kamar yanda suma suke k'yautata masa da dukkan iyawarsu. Yaran Munubiya itama 6, Dan itama 8 d'inne ta haifi biyu babu rai, Ameen yana tare dasu Abdurraheem, yayinda meenal takanyi Rabin rayuwartane a masarautar gagara badau, saboda batada k'awa wadda tawuce Amaturrahman. Inhar basa Masarauta to sunacan gidansu meenal d'in, sun zama y'an mata ababen birgewa, ita meenal tana masifar son Abdurraheem ne shikuma k'asaita da muskilanci irinna ubansa Sarki Muhammad Sameer tariga tazama jinin jikinsa, yata basar da ita kenan, wannan Abu Na cimata rai, amma aduk sanda ciwonsa zai tashi tafi kowa shiga damuwa, idan kuma taga yanda Ameen da Amaturrahman ke soyewarsu saita kumajin kanta a damuwa, shikam Abdurrahman Niger ya tsallaka, Dan d'iyar Sarki Issifa da Sarauniya Ayusher Rabi'a (Amatullah) yakeso da k'auna, ya rikice sosai, haka kawai saiyayi shiri wai yatafi yima Inna Hutu, nanko wajen Amatullah yaje. Wannan hutune Na k'arshen shekara daya kasance duk yaran suna Nigeria, saboda bikin su Aryaan da akasha babu dad'ewa. Sarauniya Munaya kishingid'e a kilisarta hadimanta nata hidima a gareta, matasan samarin y'ay'anta suka nemi ison shigowa gareta. Izini ta basu, tareda sallamar dukkan Hadimanta. Abdurraheem da Abdurrahman suka shigo, Kansu d'aya, kamanninsu d'aya, halayyace kawai ta banbantasu, Abdurraheem halin Sarki Muhammad Sameer ne gaba d'a a jininsa, yayinda Abdurrahman yazama mai irin halayyar Uncle Sauban da Abie. Har suka zauna idonta Na kansu, sukai zama irinna k'asaita suna gaisheda mahaifiyar tasu. Fuskar Sarauniya Munaya d'auke da Murmushi ta amsa, takai dubanta ga Abdurraheem dashi ko kad'an bashida yawan magana. “Abdurraheem saunawa zan maka magana akan aske sumarnan ne?”. Lips d'insa ya cije (d'an gado kenan😂) yanad'an 6ata fuska. “A gafarceni Ummu, wlhy zan Aske, jiya nafita zanje shagonki askin sai takawa yayi kirana ya Sani wani aikin, amma Ummu shima Abdurrahman kimasa magana ya yanke wannan k'umbar, ALLAH k'yank'yaminta nake.......” Harara Abdurrahman ya zuba masa, zaiyi magana Sarauniya Munaya ta katseshi tana tashi zaune, “Abdurrahman naga hannunka”. “Ummu karki yarda da gulmar yaronnan ALLAH, yatsa biyunefa”. Ya k'are maganar da kuma harar Abdurraheem daya ta6e baki ya cije lips. Sarauniya Munaya tace, “Yimani shiru, nabaku nanda dare wlhy kowa ya cire k'azantar jikinsa, ina kuma fata anje an bama Abie magungunansa?”. “Eh Ummu, Abdul-fatah ya bashi, yanzuma daga sashensu muke barci yakeyi, amma su Amaturrahman nacan sun cikama Momma kunne da surutunsu Na tsiya itada Meenal”. Murmushi Munaya tayi, Dan ita babu abinda take gani tattare da Abdurraheem sai Mijinta, shikuma Abdurrahman rashin iya R kawai ya gado shida Safah da Marwah duk basu iya R ba, to ga Saifudden nanma akwai k'asaita tsiya, d'an k'arami dashi sai mulkin tsiya, ga jarabar son girma, bawani girman jalaludden yayiba amma inkaga yanda yake basa umarni saikaci dariya, hakama yaran Hafsat. Sarauniya Munaya tacigaba da hira da yaranta da musu nasihar tsare mutuncin Kansu kamar yanda ta saba. Wayarta da sak'o ya shigo ta d'auka tana dubawa. Sarkine da kansa. *_Gaskiya ina buk'atar jin d'umin my mata._* Murmushi Sarauniya Munaya tayi tana kallonsu Abdurraheem da suka satar kallonta, idan kaga irin wannan murmushi ga mahaifiyarsu to akan Abbun sune kawai. Tad'an hararesu tana fad'in “Takawa ba yana fada ba?”. “A'a yana turakarsa, Dan zamu shigo nan mukaga fitowarsa daga fada”. Nanma murmusawa Munaya tayi kawai, ta tashi zaune tana gyara zaman alk'yabbarta, “Kuje Sweetheart Na nemanku, amma Ku dawofa da wuri, kunsan yau ranace ta musamman da takawa ke zaman hira damu, karkuyi sakacin dazata wuceku, akwai sak'o a d'akina saman mirror Ku d'auka akai mata, zan kirata namata bayani”. A tare suka amsa da to Ummu. Ta mik'e ta shiga bedroom d'inta, mintuna kusan biyar saigata ta fito tabi wata hanya da zata sadata da sashen Sarki Muhammad Sameer kai tsaye batare da kowa

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});