Chapter 15
Chapter 15
zuwa kamannin mahaifinsa wayata ta shiga Ring, d'auke idona nayi daga kan Abdurrahman na maida ga wayar, nayi mamakin ganin yalla6ai, danna canja sunan tun a waccan ranar, na daiyi picking a d'arare na saka a kunne. yau dai banjira k'orafinsa ba nace, “Ina yini”. A yanda ya amsa min sallamar da gaisuwar saida gabana ya fad'i har na cire ma Abdurrahman nono ban saniba, aikam ya fashe da kuka. Hakkane yakuma rikita Galadima daga can, yace, “miya faru? Waye ke kuka?”. K'aramin tsaki naja, nace, “Abdurrahman ne, wai dama ka dawo?”. Bai amsa min na k'arshen ba saina farkon, yace, “mi'akai masa?”. “Babu komai, bayajin dad'ine kawai”. Lips d'insa ya cije yana fad'in “yanzu zanzo gidan”. Bai jira cewar Munaya ba ya yanke kiran. Sororo nayi ina kallon wayar, kai kace zan ganosa a wajen ne, Munubiya data fito ta katseni da fad'in “mikike kallo haka? ga ruwan nono kin bari yana zuba a jikin yaro”. Ajiyar zuciya na sauke, sannan na gyara ina kwantar da Abdurrahman d'in dayay shiru. Munubiya dai takuma tambayata, fad'a mata zuwan Galadima nayi, tace, “oh shine kikema wannan mamakin ko miye?”. 'Dan hararta nayi, amma bance komaiba, itama ta ta6e baki tana kamo hannuna ta zauna a stool d'in Mirror. Wai sai tamin kwalliya. Da faro k'in yarda nayi, saida naga ta 6ata rai sannan na hak'ura dai tamin inata tura baki gaba.....................✍🏻 *_ALLAH Sarki, wlhy harna fara missing d'inku, waya tamana tsiya😢, yanzuma da wayar Oga nayi typing, koba komai Comments naku na sakani nishad'i, I Miss you so much all😔😘😘😘❤❤_* Insha ALLAH vary soon zan dawo gareku😂. *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭👏🏻_* [7/29, 5:47 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* *_💡HASKE WRITERS ASSO...._* *_♦RAINA KAMA...!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_BOOK 3_* 👉🏻1⃣1⃣➖1⃣2⃣ .............Mintuna basufi 20 da gama kwalliyar ba saigasu Aiyaan sun shigo dad'an gudunsu, Munaya na cikin d'aki tak'i fitowa, wai kunyar su inna suganta da kwalliya takeyi. Inna ta dakama su Aryaan tsawa saboda batason wannan gudun. Nutsuwa duk sukayi. Tace, “Gudun mi kukeyine?”. Y'ar rige-rigen fad'a suka fara, kowa yana ture d'an uwansa akan shine zai fara fad'a, ana cikin haka Yaa Anas yay sallama. Hayaniyar su Aiyaan ta hana aji, sai laraba ce ta farga dashi, shine Yakuma yimasu Aiyaan tsawa suka nutsu, kowa ya zauna gefe yana tura baki. Yaa Anas ya gaishe da laraba da innarsu munaya, Munubiya ma ta gaisheshi, ya Amshi Ameen dake hannun inna yana fad'in “inna Yalla6ai Galadima ne fa agidan namu, gashi kuma duk su Abba basa nan, shine nace ko'a kawoshi nan ne”. Inna tace, “A'a Anas, ai ba'ayi hakaba, bara na d'akko makullin d'akin Abbanku saika bud'e masa nan ya shiga”. Anas yace, “to inna”. Laraba dake taya Munubiya shirya su Amaturrahman tayi murmushi, a ranta tana yaba yawan karamci na ahalin Munaya, mutanene masu dattako da sanin darajar d'an Adam, shiyyasa kullum take kuma taya Galadima murna da samun tsatson wannan mutane....... Tunaninta ya katse lokacin da inna tadawo da key ta bama Anas, Ameen ta kar6a a hannunsa shikuma ya fice. Munubiya tace, “innarmu ajiye wannan ki k'arasa sama Abdurraheem kayan Dan ALLAH, sainaje na had'ama Abbansu abincin, nasan yanzu yayi”. Inna ta harareta, “kai nifa kunma maidani Nanny d'inku, nizan ke muku hidimar y'ay'ane?”. “please mana innarmu, basune masu kawo miki kaza kina ciba sannan kin tsufa”. Laraba tayi dariya tana fad'in “Gaskiyarki kuwa Maman 2, ALLAH dai yaja da rai”. Inna tace, “iya kema biyema shirmennan nata zakiyi?”. Laraba takuma darawa tanama Abbdurrahman rawa. Itadai Munubiya ta fice tabarsu, laraba na bama inna amsa. Duk ina jiyosu daga d'aki, haka kawai sainakejin wani iri, yanzu dole ta gaban su Innarmu zanbi natafi wajensa? Na kalli kaina a mirror kunya ta kuma kamani, dukda Simple kwalliya Munubiya tamin nayi k'yau, dan d'aurin kaina ya zauna dak'yau, fuskata ta kuma nutsuwa, har rantsuwa tamin inhar na canja wani Abu saitayi 2weeks batamin maganaba, nasan kad'an kenan daga abinda Munu... Zata iya, shiyyasa dole na hak'ura na bari..... Shigowar Munubiya yasani waigawa na kalleta, ta harareni tana matsowa tamin kallon tsaf, nasan sotake taga mina goge kona canja, ganin komai yana yanda tayishi saita kuma d'aukar soson hoda ta gyara, ta d'akko turare tana kuma fesamin, hannunta nai saurin rik'ewa ina 6ata fuska, “Wai Sweetheart bazaki barshi haka bane? Turaren nan har hawa kaifa yake, Ni wlhy kunyarma fita nakeyi”. Munubiya ta fisge hannunta tana dariya da fad'in “to kibi ta k'ark'ashin k'asa kawai mana, kuma wlhy ki nutsu, idan yauma tsiwar zaki masa saiki bada himma, anacewa mutum Idan ya haihu yana hankali kedai bakiyiba, saima rashinsa kika k'aro, malama muje yana jiranki”. Yanda kukasan na make Munubiya haka naji, amma saina k'yaleta, nima nasan ta hanyar da zanbi na rama, gyalen data samin a kafad'a nabi da kallo. nace, “haba Munu, amma wannan d'an gyalen Dan ALLAH?”. “Okay, wajen surukinki zakine? ALLAH ki kiyayeni”. Baki na murgud'a mata. Tace, “oho dai, kije kimasa kidawo ta cinyayyen lips, danba barinki zaiyiba”. Juyawa nayi na kalleta, amma saita d'auke kai tamkar bama itace tayi maganarba. Nayi kwafa kawai muka fito. ALLAH ya soni babu kowa a falo sai su Aiyaan, hakkane ya sakani sauke ajiyar zuciya nad'an saki jikina. Gwaggon Haleematu dake kaikawo a kitchen da tsakar gida saboda itace ta kar6i girki tabimu da kallo, gulma nacin ranta, daga ni har Munubiya d'auke kai mukayi tamkar bamu gantaba, muka shige falon Abba da takalman Galadima heif cover milk ke a k'ofar. K'amshin turarensa yafara amsa mana sallama, na shak'a na lumshe ido. Hankalinsa nakan yaransa da duk suke jikinsa, yana sanye cikin milk d'in shadda harda hular zanna bukar itama milk da d'an kwalliyar Brown kad'an, sosai yamin k'yau amma saina d'auke kai tamkar banma gansa ba. Munubiya tace, “To Abban 3 gatanan nakawo maka”. Murmushi yayi, idonsa sanye cikin farin eyeglasses, cikin muryarnan tasa mai kama da anmasa dole yace, “Thanks you Auntynmu”. Murmushi itama Munubiya tayi, ta jinjina masa kai ta juya zata fita, har takai k'ofa ya katseta da fad'in “Su twins rowarsu akemin?”. Hannu ta saka ta dafe bakinta, saikuma ta janye tana cewa, “A'a Abban 3 zasuzo su gaida abbansu insha ALLAH”. Baice komaiba sai murmushi daya sakeyi. Ta harareni sannan ta fice, Nina ramawa nayi. Koda Munubiya ta fice saiya kuma maida hankalinsa ga yaran ya shareni, abin yabani haushi, jinaima kamar na fice abina, amma na danne zuciyata na matsa gabansa. Wajen tiren abincin na durk'usa, na d'auki jug d'in zo6on na zuba a k'aramin cup, d'agowar da zanyi na kamashi yana kallona, amma saiya basar, baki na tura kad'an, na mik'a masa cup d'in. Bai kar6aba, sai wani bina da kallo yake tundaga sama har k'asa, a raina nace rainin wayo. Idonsa ya janye daga kaina, ya fara kwantar da yaran d'ai-d'ai a gefensa, saboda a doguwan kujera yake. Saida ya gama nakuma mik'a masa cup d'in, hannuna ya had'a da kofin ya rik'e, na d'ago ido muka kalli juna, duksai na daburce, danya cire eyeglasses d'in, kamar mai koyan magana na had'o kalmomin gaisuwar da gyar. Nace, “i...na..yini”. Wani Munafukin murmushi yayi yana lumshe idanu, ya kuma bud'esu a kaina yana d'age girarsa d'aya da cizar lips, a hankali ya furta “ke matsoraciya Ce, miye na rikitar daga kallo
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83