Chapter 49
Chapter 49
yada zango ce takaimu Nigeria, a wahalce a jigace, inda muka samu mafaka a tashar da suke lodin motocin da suke zuwa kasuwanni, makonmu uku a wajen, Dan bamu rasa abincin dazamu ciba iftila'in rayuwa da k'addara ta fad'amin, Wanda muka wayi gari da rashin mai taimakonmu sai wani bawan ALLAH (Malam fharuku kakansu Munaya😅)” Inna taci gaba da bada labarin k'yautatawar dasu Innaro sukai musu, har mutuwar iyayensu da aurenta da Abba, Dana mama Rabi'a, da zuri'ar da suka samu harda jikoki, ko kad'an bata fad'i muzanwa ko cin fuska da Innaro taita musuba sai alkairin mijinta da y'ay'anta. Nanfa kowa ya shiga matse hawayen tausaya musu, hardamu, Dan munji abinda koda wasa bamu ta6a saniba balle tunanin kasantuwarsa, Dama iyayenmu jinin sarautane mai girma irin haka? Amma kullum suka kasance cikin shanye k'ask'anci da gorin talauci Dana ahali, lallai wannan banzar al'ada batada wani abin birgewa. Shikansa sarkin saidai yay hawayen tausayinsu inna, Yakuma buk'aci su matso garesa, hakama tsohuwarnan rungumesu tayi tana kuka. Innaro dai anyi zugudim tana kallon ikon ALLAH, Wanda ya girma ya d'aukaka, kunya da d'unbin nadamar Dana Sani sun dabaibayeta tagaza koda kwakwkwaran motsi balle d'aga ido ta kalli su inna, yanzu nan dukkan cin kashi dacin zarafin dataitama su Ai'sha musammanma ita shine zata lullu6e bak'in mugun halinta ta wanketa da alkairin mijinta Dana y'ay'anta? Wace irin k'yak'yk'awar zuciyace da wannan baiwa haka?. Munsha kukan tausayin su innarmu, sannan munyi murna matuk'a da tarbar da akai musu damu kanmu, Su Abdurraheem dasu Aiyaan, da Aryaan, Ahmad, dake k'anan duk an janyesu, kowa yana d'aukarsu cikeda tsantsar so da k'auna. Saida akad'an lafa sannan Sarki yay bayani cikin nutsuwa da dattako. “Lale marhabin agareku y'an uwana, kun kafa tarihin da tilasne a yaba muku, Dan babu wasu da suka sake waiwayen wannan masarauta bayan korar da akaimusu, sun tafi ba'a kuma jin labarinsuba ko inda suke. Bak'aramin durk'usar da wannan masarauta waccan Mummunar Al'ada tayiba, mun rasa ahalinmu masu d'inbin yawa, masarauta dake cikeda dangi yau takoma sai tsirarune a cikinta, kunganmu nan dudu iyakarmu kenan muka rage, wasu sarautunma sai hannun jama'ar gari da bayi ta koma, saboda babu masu rik'ewar, haihuwa itace yad'o, mukuma mun nisanta kanmu da wannan yad'on, masarautar nan ta dad'e tana korar ahalinta saboda haihuwar y'ay'a mata, ALLAH kuma yayta jarabtarmu da samunsu a matsayin y'ay'a, bayan shud'ewar marigayi Sarki Madou Amadi sarakuna kusan 20 sun shud'e a dalilin hakan, bamusan duniyar da sukeba, saida mahaifina yahau ya tsaida wannan al'adar gaba d'ayanta, saboda ganin wataran lallai sai kowa dake cikin ahalinmu ya k'are inhar wannan al'adar tacigaba da wakana, muna baku hak'uri, muna kuma Baku hak'uri, a yanzu wannan masarautar ba ita bace waccan da kukasani, mace Nada daraja sosai a yanzu, tanada kima da k'arfin fad'a aji, muna fata bazaku sake nisantarmu ba, zakuzo mu had'a k'arfi da k'arfe wajen kuma samun yad'uwar wannan masarauta ”. Innarmu da mama Rabi'a Na hawaye suka amsa masa da insha ALLAH. Zayyana muku farincikin daya cigaba da gudana 6ata lokacine, mun shige cikin dangin mahaifanmu munata warkajami, kulawa ake bamu ta musamman da birgewa, aranar aka canja mana masauki Na musamman dayafi wancan k'awatuwa da komai, aka zuba mana hadimai masu hidima, su Abba kam ko ganinsuma bakayi, gagarumin biki Na musamman aka shiga shiryawa Na murnar dawowar su innarmu. Kai lallai munashan kallo, kukadai najin dad'i da farinciki mun shashi, INA y'an gidanmu? Suzo suga abin al'ajabi daban mamaki, innaro dai baki ya mutu murus, saima dukta tsangwami kanta a cikinmu, aiko mukaita zuba mata habaici muma, Dan ganin su innarmu yama gagareta gaba d'aya, sun shige cikin y'an uwansu tamkar dama ciki suka taso, duk wannan hidima batasani mantawa da kewar mijinaba, musamman da Saurayin jiya yafara takurani da kallon tsiya har a ranar, nikuma ban daina antaya masa hararaba, saida nagaji nake sanarma su Munubiya, suma sukace ai duk hakan yake musu, itadai Munubiya tasamu tayi maganinsa ta hanyar mak'alk'alema mijinta, dukda kuma suna tare da Yaa Marwan d'in duk inda yasa k'afa, hasalima Yaa marwan ya koma sashensa gaba d'aya. Daganan tasamu lafiya, saiya koma kanmu ni da Ayusher, dukda wani lokacin yakan Gaza banbantamu ni da Munubiya, inhar baya ganta tare da yaa Marwan bane, itakuma Ayusher ta fini jiki, musamman ma ramar danayi ta jiyyar Dana sha, ita kanta Munubiya tafini jiki a yanzu. Gashi su Abdurrahman sun gagareni d'auka balle nima Na fahimtar dashi inada aure, inkin gansu a wajena shayar dasu zanyi, tokuma bazan iya hakan agabansa ba. Wannan saurayi dai d'ane ga Sarki, Dan shine magajin masarautar ma yanzu. ___________________________ Muna zaune awata rumfar Bunu a washe garin da muka cika kwanaki buyu a masarautar, ranarda za'a gudanar da bikin dawowar su innarmu, zaune muke da wasu y'anmata kusan 8 masu kama damu, duk kuma bazasu wuce sa'annninmu ba, saidai wane ya girmi wane da wata 1 ko biyu, hira muke cikin so da k'auna juna, da d'okin kasantuwarmu ahali d'aya. Suna bamu labarin yanda bikin al'adunsu ke gudana irinsu bikin sallah dana aure, muma muna basu namu, saidai maganar gaskiya ni hankalina ya rabune gida biyu, rabi garesu rabi ga Galadima. Munubiya ce ta lura da hakan, ta d'an ta6ani Na juyo Na kalleta. “Sweetheart mike faruwane wai?”. Cikin marairaicewa nace, “Munu Galadima mana, yakamata yajini koda a wayane, kinga anama mahaifinsa Magani, baikamata ace koyaya bana bibiyar lamarin Yaya lafiyarsaba, karyaga kamar ban damubama”. Cikin gamsuwa tace, “zancenki gaskiyane, shiyyasa kike burgeni wajen hangen nesa, inaga yakamata mu nemi sim card mu saya”. Naji dad'in shawararta, Dan haka muka tambayi y'an matan. 'Daya a cikinsu mai suna Badeera tace, “yanzunan kunason yin amfani da waya shine bazaku kar6i namuba? Amma bamuji dad'iba gaskiya, Ashe bamu zama d'ayanba kenan?”. Hak'uri muka basu, Maryamu ta d'oramin wayarta a jiki tana fad'in gashi kiyi kiran duk Wanda zaki kira, bara a sanarma Yareema issifa yasa akawo muku. (Nayi amfani da namune saboda wasu dalilai, yarenmu ba d'ayaba Dan haka abubuwan da suke fad'a bazai zama d'aya da namuba, to amma Raina kama anginashine bisa wani bigire daban, zanyi amfani da iya abinda Na sani, Dan ban zurfafa bincikeba gaskiya, ALLAH yasa zaku fahimceni😅🤝🏻). Da mamaki nace, “waye hakan?”. Cikin dariya sukace magajin wannan masarautar mana, Wanda kike k'orafin ya dameku da kallo”. Baki nad'an ta6e cikin mamaki, nace, “To wai Issifa sunane?”. Nanma dariyar sukayi, Dijahma tace Youseefa kenan fa. Nace, “tab, sunayenku kukam wasu iri wlhy, nidai bara kuga naje Na nemo mijina”. Dariya duk suka sanyamin. Natashi zuwa cikin masaukinmu. d'akinmu Na shiga, Na lalubo wayata a handbag wadda tunda mukazo suka zama marasa amfani agaremu. ************************** A 6angaren Galadima kam suma Alhmdllh, Abie yanata samun kulawa ta musamman ga Dr Erfan Fahad, Dan da iya k'yautatawar yakema Abie abu, kodan sanayyar dake tsakaninsa da Galadima wadda saidaga baya ya tuna wanene Erfan Fahad d'in, sunyi karatun addni wajen malami d'aya a time d'in bazasu wuci shekaru 9 ba, har lokacin da suka kai 17years shi Erfan Fahad iyayensa suka d'aukesa daga wajen Sheaik Mu'azzam Abdul-aziz, saboda zasu koma Kashmir a lokacin, dama aikine yakawo mahaifinsa India, tundaga nan basu sake had'uwa ba sai yanzun, lokacinda Sheaik Mu'azzam Abdul-aziz ya rasu shi Dr Erfan Fahad yazo gaisuwa, amma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83