Chapter 48
Chapter 48
abinda yafaru yabata labari dallah-dallah, dukda Aunty Mimi tabata dama, Momma harda hawayen jin dad'i, ta rungume Galadima tana saka masa albarka shida matarsa da yaransu. Babu kunya ya ringa amsawa cikin tsantsar farin ciki. Yanzu kam koba komai hankalinsa ya kwanta, ya maida hankalinsa ga dukkan aikinsa da sana'oinsa da suke samun kud'in shiga akan jiyyar mahaifinsa. Shiri yake a gaggauce saboda kiran da Doctor d'in Abie yamasa tun a daren jiya akan yanason ganinsa yau da sassafe. Yayi k'yau cikin Orange d'in Suit, sai k'amshinsa yake mai dad'i, cikeda salon birgewa yake sakkowa daga steps d'in benen yana waya, bayin daketa aikace-aikacen k'imtsa falon duk suka zube suna gaisheshi. Hannu kawai ya d'aga musu ya nufi hanyar fita a hanzarce yana cigaba da wayarsa, ya d'ora briefcase d'insa saman motar yasa key ya bud'e, bag d'in yafara ajiyewa gefen mai zaman banza sannan ya dawo ya bud'e ya shiga mazaunin driver ya tada motar ya fice. “Muftahu kabari zamuyi magana daga baya dai kawai”. Daga can Muftahu ya amsa da to babu damuwa. Ajiye wayar Galadima yay ya maida hankalinsa ga tuk'insa, yayinda sashen zuciyarsa ke tunano masa hirarsa da Munaya ta daren jiya, kwana biyunnan idan yamata maganar dawowarta saitai ta masa yawo da hankali, yarasa dad'inmi zaman can d'in yake mata? Ai wankan jegon ya isa haka, shima yana buk'atar zama da iyalansa koya samu nutsuwa tamkar kowanne magidanci, k'aramar tsaki yaja yana furzo isaka daga bakinsa, mata kenan, wataran su baka zuma, wataran su caja maka kai. Da wannan tunanin ya k'arasa asibitin, wayarsa kawai ya d'auka ya fita a motar, kai tsaye Office d'in Doctor Ajay ya nufa, yay Knocking aka bashi izinin shiga, (Abu Na CCTV suna kallon shige da ficin kowa) Doctor Ajay ya fad'ad'a murmushi sa yana mik'ewa, hannu suka bama juna cikin Musabaha suna gaisawa, Doctor ya nunama Galadima wajen zama. Bayan sun zauna Doctor daketa faman murmushi yace, “Sameer wani abun farin ciki ne nasamo a daren jiya, shiyyasa nakasa sukune saida Na kiraka a daren domin buk'atar ganinka”. Galadima dai kallonsa yake baice komaiba. Dr Ajay yaci gaba da fad'in, “Wato wani Doctor ne mai suna Dr Erfan Fahad Sajaad, d'an k'abilar Kashmir ne, Likita ne babban masani ta fannin irin matsalolin su Abie, yanzu haka yana k'asar England akan wani aiki, nakai watanni 6 inason ganinsa akan matsalar Abie amma ban samu damaba, saboda matuk'ar Busy dayake, sai a daren jiya nasamu magana dashi, bakaji farin cikin dana samu kaina a cikiba, dan mun tattauna sosai akan matsalar Abie, yanzu haka yabamu date d'in dazamu sameshi can Kashmir a asibitinsa”. Alhmdllh Galadima yaketa ambata a zuciyarsa tunda Dr Ajay yafara bayaninsa, cikeda farin ciki yace, “Doctor lallai nayi farin ciki da wannan albiahir naka sosai, ka wuce matsayin likita kawai a garemu saidai d'an uwa”. Murmushi Dr Ajay yayi, suka rungume juna shida Galadima kowa yanajin dad'i a ransa. Galadima ya fito d'auke da wannan farin ciki sukaci karo da Akash a hanya. Akash yace daddyn Triplets kenan, kwana biyu ka 6uya?. Hannu Galadima ya bashi yana fad'ad'a murmushinsa, yace, “Sorry my friend ka ganni dai yawo kamar ruwan sama, idan bani anan aganni acan, ya aikin?”. “Gashi munata fama, ya naka?”. Galadima yace, “Alhmdllh”. “Wai sai yaushe zaka dawo mana da Mummyn triplets ne? ga bikina yanata matsowa, bafa zan muku alfarma ba”. Murmushi Galadima yayi, ya dafa kafad'arsa yana fad'in “kwantar da hankalinka, ai babu yanda za'ai bikinka babu mu a wajen”. Aksha yace, “Ato kun wanke kanku, daga ina ka fito haka cikin farin ciki?”. Bayanin komai Galadima yayma Akash, dan baya 6oye masa komai gameda ciwon Abie. Shima ya nuna tsantsar farin cikinsa kuwa, kafin suyi sallama kowa ya nufi inda zaije. Waya yaciro yana lalubo number Munaya................✍🏻 *_Zan iya cewa yanzu zaku dinga rashin ganina, wlhy ammana haihuwar da tilas saina kasance a wajen a kullum, amma inhar Na samu time zaku dinga ganin posting, dan yauma banyi tunanin zanyiba, amma saigashi ALLAH yabani iko bayan dawowata daga asibiti, nima kaina Na k'agara nagama Na huta kuma Ku huta🤦🏻♀, I love you all😘😘😘😘❤🤝🏻_* *_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻 [8/22, 8:27 AM] Aysha Galadima: [8/9, 5:40 PM] 🙇🏻♀Da Rarrafe🙇🏻♀: [8/9, 12:53 PM] 🙇🏻♀Da Rarrafe🙇🏻♀: *_Typing📲_* *_💡HASKE WRITERS ASSO...._* *_♦RAINA KAMA...!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_BOOK 3_* 👉🏻2⃣3⃣ .................Mud'in mun kasance wasu yankin ahali daga wannan masarauta, sai dai nasan al'ada da ak'idar masarautar ta jima da shafemu daga kasantuwar tsatsonta. Iftila'in al'ada Nak'in kar6ar d'iya mace a matsayin y'ar farko ga Sarki mai mulki shine silar barin iyayenmu damu kanmu, sarakuna da yawa sun shud'e labarinsu ya shafe tamkar yanda Na Sarki Madou Amadi yazama shud'ad'd'e” inna ta share hawayenta, sannan tacigaba da fad'in, “Lokacin da mahaifinmu yake bisa karagar Mulki da k'arfin iko sai ALLAH ya azurtashi da haihuwa ta a matsayin d'iyarsa ta fari. Haihuwata ta girgiza k'arfin mulkinsa matuk'a, Dan Al'adar masarautar shine tilas d'an Sarki Na farko ya kasance d'a namiji, acewarsu d'iya mace rusa masarauta takeyi da tsiyatata, dan ita bata mulki, kamar yanda ake korar duk wani Sarki da matarsa ta haifi y'a mace a haihuwar farko ga mahaifinmu sai bai yuwuba, saboda k'arfin iko da ALLAH ya bashi, anbuga-anbuga yak'i sauka, danshi burinsa ya canja wannan al'adar masarautar, har ALLAH yasa Na cika shekaru 7 a duniya. A tsakaninnan bayyana harmutsi da hayaniyar da taita faruwa 6ata lokacine, Dan mahaifinmu Sam yak'i sauka daga Matsin da suke masa. cikin amincin ALLAH sai kuma ga cikin Rabi'a babu zato, har wannan lokacin babu wani kwanciyar hankali a masarauta, saidai bayyanuwar cikinta yasa akace za'a dakata aga mizata haifa, idan d'a namijine shikenan. Saidai kash, daga lokacinda Rabi'a ta canyara kukan isowa duniya sai masarauta tayi tsitt, Dan kuwa dai kowa yaji macece. Dandanan fa aka tada Sabin bore akan dolenefa sarki ya ajiye a wannan karon, amma mahaifinmu saiya k'i a wannan karonma, danshi burinsa ya canja wannan mummunar al'adar kowa ya fahimci itama d'iya mace tanada tata darajar fa, kufa namijin bai fitaba, domin itama ALLAH ya haliccetane danta bauta masa tamkar namijin, dukansu kuma idan sunk'ibin ALLAH wuta zai sasu, idan sun bishi Aljanna zai kaisu, amma Sam sai suka bijirema dukkan tunatarwarsa, masuma goya masa baya suma sai suka daina, watan Rabi'a 1 kacal a duniya akai mana korar kare daga wannan masarauta dama yankin baki d'ayansa, muna kuka muda mahaifinmu haka muka tafi, mukabar ahalinmu, yankinmu , al'ummarmu. Saboda mummunanr Ak'ida, saidai kuma babu inda muka Sani, Dan haka iyayenmu suka yada zango awani k'aramin k'auye dagacan bakin gari, anan muka rayu tsawon wasu shekaru dahar nakai girman zama minzalin budurwa, itama Rabi'a ta girma, rana tsaka saiga tawagar masarauta wai ankai mata bayanin mahaifinmu baibar wannan yankiba, halan akwai abinda yake shiryawa? Dan bazai yuwu ayi sarki biyu cikin nahiya d'aya ba, sarkin ma da aka d'ora bayan korarmu shima matarsa mace ta haifa, tuni sun korashi, Na yanzunma kuma hakance ta faru, dalilin korarsane ma sukaji labarin mahaifinmu yana a wannan waje tare damu. Korar cin zarafi da akai mana a wannan lokacin tamafi Na farko, Dan alokacin munada wayo muma, munsan zafi munsan d'aci, a wannan karon bama Nahiyarmu ba, k'asar gaba d'aya muka bari, tafiya ta tsawon wattani da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83