Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 76

Chapter 76

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

mai afkuwa ta afku, dan kuwa ALLAHn daya bamu Innaro yau ya d'auke abarsa, ta koma garesa tafiya mai nisan zango, saiga su baba k'arami na kuka da idanunsu, mahaifiya dabance, komai mugun halin mutum idan giji tazo dolene ka saduda dajin k'aunarsa ta musamman, kuka kam mun cisa tamkar babu gobe, yau gidanmu saiyay tsitt. Gwaggo Safiyya ta mata wanka a d'akinta, aka sallaceta a k'ofar gida da raka gawarta gidanta na gaskiya, hardasu Galadima kuwa, Wanda shima saida ya share hawaye, halayyar tsohuwar kan sakashi nishad'i haka kawai, danshi bayajin haushin masifarta, saima birgeshi da takeyi, musamman idan ta kafe akan Abu, bayan tasan gaskiyane amma tace sam ita ba hakaba. Ranar a gida muka kwana harsu Fauziyya, washe gari aka cigaba da kar6ar gaisuwa, a kwana na biyu saiga dangin su Innarmu daga Niger, harda Ayusher dake fama da tsohon ciki. Ranar addu'ar uku saiga su Abie da mai martaba sunzo gaisuwa suma, dasu akayi addu'ar uku ma. Aranar duk muka koma gidajenmu cikeda kewar innaro. ********* Ranar addu'ar bakwai d'in Innaro muka samu shiga wajen baba mai kanwa ni da Galadima. Mun iskeshi shima dai lafiyar sai a hankali, dan yanzu ko fitama bayayi, muka gaidashi cikeda girmamawa, ya amsa mana da fara'a, harda tsokanarmu da cewar, “Sai yau nake ganin ango da amarya?”. Duk murmushi mukayi cikin jin kunya. Shima ya kuma murmusawa da fad'in, “Mi kukeson Sani y'ay'ana?”. Nace, “Baba mai kanwa abinda ALLAH ya baka ikon Sani game damu”. d'an Murmusawa yakumayi yana gyara zaman hularsa, ya nisa cikin sauke numfashi. Yace, “Da farko dai niba maye bane, bakuma muguba kamar yanda wasu sukasha fad'a tun ina yaro, saidai ina tare da wasu aljanu da bansan ta Yaya suka kasance daniba tun k'uruciya. Tun farkon zuwan kakanninki gidan Malam fharuku aljanun dake tare dani suka sanarmin da dukkan asalinsu, harkuma suka rasu da matsalolin da mahaifiyarku taita fuskanta ga marigayiyya, abinda yasa na barsu ban ta6a maganarba saboda komawarsu a wancan lokacin bashida amfani, ina tausayinsu kuma k'warai da gaske, aljanuna sunsha d'aukata su kaini har cikin masarautar su Ai'sha, kullum cikin bibiyar musu ko ansamu canji nake, amma ba'a daceba har ta samu haihuwarku. Abinda yasa lamarin Galadima ya shigo rayuwaki a labarin shine, Maharbi daya taimaki Badi a jeji ranarda ya bama Auwalu babanki abin d'aukar hoto ne. Ba mutum bane wancan maharbi, aljanine yazo masa a suffar mutane, kuma har Badi yabar wajensa shima bai saniba, wannan aljani shine ya ta6a taimakonka a India lokacinda ciwonka ya tashi ka fad'i a titi, shine kuma ya kwad'aita maka wasu zantuka akan matar dazaka aura, a lokacin shekarun su Hussaina 12 kacal a duniya😊, badan yasan itace matar takaba ya fad'a, saidan maka fatan hakan, dan yata6a sanarmin akwai al'amari mai k'arfi dake tattare da y'an biyun Ai'sha, kuma bisa dalilin abinda akabama Auwal abin yake, sai dai shima baisan mineneba, saidai mujura hukuncin ALLAH. tun daga wannan lokacin wannan aljani ya baza y'an uwansa aljanu suna kula da dukkan motsinka Muhammad Sameer, suma su Hussaina haka itada y'ar uwarta har suka kai adadin shekarun girma. Yafara zuwama Hassana a mafarki, amma saiya fahimci batada k'arfin zuciyar da zata iya shan gwagwarmayar rayuwa dakai, hakanne ya sakashi komawa kan Hussaina, amma ita sai aka dace, wannan shine mafarkin da kuka dingayi keda y'ar uwarki Hussaina, nikuma na cigaba da d'oraki mataki-mataki akan kar6ar Muhammad a matsayin miji, Haidar da kike gani yazo har aka saka ranar aurenku ba mutum baneba, aljanine dagashi har iyayensa da sukazo neman aurenki”. Ba k'aramar zabura nayiba, hartaso bama Galadima da baba mai kanwa dariya. “Kinga kwantar da hankalinki, ai ko driver dayay masu Muhammad aiki akan satoki ba mutum bane ba, k'arfin jini da ALLAH yabaki kikaso fahimtar hakan kuma, daga ke har Muhammad kunsha mu'amulla da aljanu a matsayin mutane ai har lokacin da ALLAH ya k'ulla igiyar aurenku, aiko cikar taron d'aurin aurenku akwai d'unbin aljannu da suka Halarta a ciki, dukkan bayanan danai muku yanzu zan baku tabbaci, wani turaren tsinke ya d'aga lamusashshiyar katifarsa ya zaro, ya k'yarsa ashana ya kunna, dandanan hayak'i da k'amshi ya gaurasye d'akin, saiga sallama munji a k'ofar d'aki. Matashin saurayi ya shigo, Wanda Munaya bazata ta6a mance fuskarsaba, wato Haidar, hakane ya sakata zabura ta mak'alk'ale Galadima. Haidar yay murmushi kawai yasamu waje ya zauna, saiga kuma dattijo da Galadima yata6a had'uwa dashi a India, shima dai da kallon k'urilla ya bishi, basu fita a mamakiba saiga Driver daya ta6a d'akko Munaya lokacin dayace suyi auren Contract shima ya shigo, saikuma mabanbanta fuskoki Wanda sun had'u dasu a mabanbanta gurare, harda masu zuwama Munaya a k'awaye, saida duk suka zauna suka nutsu sannan suka gaisa da baba mai kanwa, Galadima ma dai a d'arare ya yarda yabasu hannu sukayi musabaha, nikam uwar y'an tsoro ai ina mak'ure a bayansa, ALLAH ma yasoni banzo dasu Abdurraheem ba, suna gidanmu. Baba mai kanwa ya nuna manasu yana fad'in, “Ina fata duk kun ganesu?”. Duk muka amsa da eh a d'arare. Dattijon daya had'u da Galadima a India ne yafara magana a nutse, “Muhammad Sameer ya bayan rabuwa da gwagwarmayar rayuwa?”. Galadima ya amsa da “Alhmdllh”. Tsoho mai sihirtaccen k'yawu zam jinin indiawa yace, “ka tuna na fad'a maka matarka Ce fitilarka? zuwa yanzu ka tabbatar?”. Galadima ya gyara zama yana Murmushi har hak'waransa na bayyana, yace, “Lallai ban mantaba kaka, saidaima nabama wasu labarin, nakuma mik'a godiya ta musamman agareku da fatan ALLAH ya had'amu daku a aljanna, ya kuma biyaku da mafificin alkairi bisaga taimako na mussaman da kuka bama rauwarmu ni da matata, duk da kasancewarmu ba jinsi d'ayaba”. Gaba d'aya suka amsa da amin, haidar ya nema izinin Galadima domin Neman afuwar Munaya. Galadima ya bashi izini. Haidar yace, “ki gafarceni bisa ga kalmomi masu zafi dana fad'a a gareki a wancan lokacin, hakan ta farune bisa k'ok'arin janyo hankalin mijinki domin jin tausayinki, kasancewarsa mutum mai tausayi da gudun shigar wani matsala ta dalilinsa”. Munaya ta murmusa tana kallonsu. Tace, “na yafe maka wlhy, kuma komai yawuce, fatana ALLAH ya tabbatar da addu'ar mijina a garemu baki d'aya”. A tare aka amsa da amin. Mun dad'e muna tattauna abubuwa da dama, kafin daga bisani sumana sallama su tafi, Wanda bai saniba saiya d'auka da gaske mutanene, baba mai kanwa yay mana doguwar nasiha mai ratsa jiki, wadda harta d'arsa tsoro a ranmu, yakuma ja mana doguwar addu'ar. Galadima ya ajiye masa alkairi mai tsoka mukayi masa sallama muka fito, bamu dad'e a gidanmuba muka koma gida jikinmu a sanyaye da abubuwan da suka faru tsakaninmu da baba mai kanwa da su Haidar. Kwanaki uku da faruwar haka labarin rasuwar baba mai kanwa ta riskemu, mutuwarnan itama ta girgizamu k'warai da gaske, munkuma jema iyalansa gaisu. Manyan dake kula da matsalolin gidanmu duk Ubangiji ya d'aukesu, yau babu Innaro babu baba mai kanwa. Zuwa yanzu kam ko ina su Amaturrahman zuwa sukeyi, sunyi wayo sosai da girma, hakama yaran Munubiya danasu Safara'u datai hak'uri takoma gidan mijinta suke zaune lafiya da kishiyarta da haihuwa yau ko gobe. Ayusher ta haihu namiji, dan haka muka d'unguma Niger suna k'wanmu da kwarkwata, hardama y'an gidanmu Wanda wanannne zuwansu na farko, sunkuma gano abinda yafi k'arfin shirmensu kuwa,

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});