Chapter 24
Chapter 24
yana gab da mutuwa sai a kawo masa gawarsu, daganan shima kaga ai sai tafiya shida wannan tatsitsiyar matar tasa y'ar bayi”. “Okey nagane boss”. Mamaki ya kama Harun har Muftahu. Zuciyar Harun tamkar zata fad'o waje dan mamaki, ya akai Galadima ya d'auki wannan video d'in, bayan dukkan CCTV cameras d'in dake hotel d'in saida suka saye mai kula dasu na hotel d'in aka tsayar dasu daga aiki........ Murmushin da galadima yayine ya katse tunanin Harun , cikin lumshe idanu da kad'a kai ya gyara zamansa, cikeda izza yace, “Abin mamaki ko? haka nake ni dama, kullum cikin bada mamaki, tabbas 6oyen dakai masa bazai yuwu muganiba, saidai kamanta da koda ace banida hanyar ganin naka idan ubangiji bai k'addaro ruhi na kona y'ay'ana ko matata zai salwanta a hannunka ba babu yanda ka iya, kana tunanin duhu da tsayar da cctv d'in hotel d'in zai baka dukkan dama ko? To kayi kuskure dan Muhammad Sameer kansa cctv ne, eyeglasses d'in dake idona komai duhun waje shi zai haskokane, dan camera d'in jikinsa tana tareda komai, kasan miyasa nabaka damar d'aukar yaran? Saboda hakan yana cikin k'addararsu, nakuma barka dasune danna kafa maka tarkon neman hujja da tabbatar da abinda Muftahu ya sanarmin”. Muftahu ya d'age gira saboda kallon tsana da Harun ke masa. Murmushi Galadima ya kumayi yana cigaba da fad'in “ka kira matata tatsitsiyar yarinya y'ar bayi ko? Saikuma abin mamaki ita wannan y'ar bayin, tatsitsiyar ce ta zame maka RAINA KAMA, dan lallai gashi zakaga GAYYA. itace ta haskomin kai a cikin madubin fik'irarta tunkan Muftahu ya sanarmin, takuma koyamin yanda zan fahimci makircinka da nagartar Muftahu, tabbas na yaba ma basirarka Harun, kanada basira k'warai da gaske, tunda kasan kanka kake a jikina kana cin dunduniyata, ni matsayin aboki d'an uwa mafi kusanci nake kallonka, kamar yanda mahaifina yarink'a kallon mahaifinka, ashe kud'in duk kaskane a garemu, nayi imani da cewar lallai ku jarabawane a garemu, kamar yanda k'addarar auren Munaya tazamema rayuwata alkairi, a kullum cikin aibanta Muftahu da bak'antashi kake a gareni, ashe kaine bak'in ba shiba, mimuka muku ni da mahaifinane haka da zafi? Nawa suka biyaku kuke cutar damu.............?”. “Sameer!!”. Harun ya kirayi sunan galadima cikin fushi, ya mik'e tsaye sunama juna kallon ido cikin ido shida galadima, cikin matsannan ciyar tsanar juna. “Kabar alfahari magen matarka tamaka bajinta, shawarama zan baka ka janyeta cikin wannan hargitsin, danko ubanta daya shiga a had'ari yake balle ita karan kad'a miya, wlhy Sameer ban ta6a k'aunarka ba, bakuma zan ta6aba har abadan, domin tsakanina dakai BASHIN GABANE, dan haka banida lokacinka yanzu har sai Camera ta dawo hannunmu, bar ganina anan a rufe, akwai mai sarrafa dukkan tunanina a waje, yarage naka kanemi hanyar kare Surukinka kafin aikinmu yazo kansa...”. A fusace Galadima ya mik'e shima yana dunk'ule hannu, amma sai Nuren daya shigo yanzu ya rik'eshi, “relax my brother, kainefa ka ta6a fad'amin ba'a maidama abokin gaba murtani da murtani, sannan ba'a bashi damar sanin sirrin yak'i sai an had'u a filin daga”. Galadima ya saki hannunsa daya dunk'ule da bakinsa daya cije, yatsunsa ya kad'a suka bad'a k'ara d'as! 'Das! Sannan ya zagaya hannunsa a wuya alamar I will kill you. Cikin d'aga murya Harun yace, “d'an halak ka fasa Sameer!”. Daga Nuren har Muftahu da Galadima babu Wanda ya amsa masa, a falo suka tsaya, Galadima ya Nufi d'akin da SD yake batare da yace uffanba, Nanma dai Muftahu ya bud'e masa, ya shiga cikin tsananin fusatar da Harun ya sakashi. zauna suka iske Alhaji Darma cikin kujera yana duba jarida, kaikace a d'akinsa yake. Galadima ya taune lips nashi tamkar zai hudasu da hak'ori, zuciyarsa Na k'una, lallai sai Harun da ubansa sun k'are rayuwarsu a jail inhar yana numfashi, dan barin irinsu a duniya had'arine babba, musamman a gida irinna sarauta......... Nuren ya katse masa tunani ta hanyar yima SD magana. cikin ta6e baki Alhhaji Darma ya kalli Galadima yana wani murmushin mugunta, ya ajiye jaridar hannunsa tare da hard'e k'afa. A bakin gadon Galadima ya zauna, ya kalli Alhaji Darma, sosai Darma ya tsorata da rinannun idanun Galadima, amma saiya dake. Galadima daya lura da rikitar Darma ya murmusa, cikeda k'asaita ya d'age girarsa, “Alhaji Shehu kenan, angaya maka mutum yakanci bashi ya kwana lafiya, duk wata jarumta da zaka aro kasama ranka tuni nagama bitar karatu a kanta, karigada ka shigo ramin damusa iya gudunka babu wajen 6uya, bama duk wannan ba, minene had'inka da surukina? Sanann minene yasa kuka kashe mijin y'ar uwata? Dan ko tantama banayi da hannunka a cikin kisanshi!!”. Galadima ya k'are maganar cikin matsanancin tsawar data rikita Alhaji Darma. Dukya rud'e yarasa ina zai kama, cikin in ina yace, “Ni sharri zakaimin bansan komai akan mutuwarsa ba”. Galadima yay dariya, saikuma ya gimtse fuska. Yace, “Okay, babu hannunka amma kake tursasa yarinyarsa Samha ta dinga d'akko maka sirrikana tana kawo mata? Kullum kana ma yarinya barazana da mutuwa ko? Alhaji shehu aini tun ranarda mijin aunty Mimi zai koma ga ALLAH naga idonsa ya tsaya cak akanka lokacin da numfashinsa ke bankwana da duniya na d'ora alamar tambaya a kanka, sai kuma yanda kake kaffa-kaffa da Samha a gaban mutane, yayinda itakuma take a d'arare dakai, dukkan wayar dakake mata kana sakata sato maka sirrina INA kan sani, dan nine da kaina nake ajiye mata tagani danta tura maka batareda ita kanta ta saniba, shiyyasa na jata jikina fiye da kowa a gidanmu, duk abinda Sameer zaiyi cikin ilimi yakeyinsa Darma, koda yake bamuzo wannan matakinba, miye had'inka da surikina?”. Alhaji Darma dake a rikice saboda tsoro da tashin hankalin zantukan Galadima ya had'iye yawu da k'yar yana fad'in, “B..babu ruwanka da abinda ke tsakanina dashi kuma”. “Hummm". Galadima ya fad'a cikin cije lips, wayarsa ya d'akko ya kunna wani recording daya nad'a a wayar Darma ranar da suka kamoshi kafin su d'akkoshi. Waya yake da wani cikin tsananin fusata, “Boss wai miyasa bazamu aika shegenan barzahu ba idan yak'i bamu Camera d'innan? Tunda munada hanyar da zamubi mu kar6a d'in, Nibansan miyasa kuke cewa abishi mataki-mataki ba, kasanfa y'arshi yaronan Sameer take aure, yanada hanya mai sauk'i dazai bashi camera d'innan, shi wancan banzan Alhaji Halluru babu tsiyar da y'ay'ansa zasuma mutane, kullum sai tsarin banza yake mana”. “Karka damu Alhaji shehu, mu bashi damar k'arshe daya buk'ata, tunda ya tabbatar mana a wannan karon zai kar6o camera d'in ta hanyar matan y'ay'ansa, yana son takara, yakuma San inhar burinmu bai cigaba shida takarar Governor saidai kallo”. “shikenan boss, bara naje ance nayi bak'o”. “Ok ngd”. Galadima ya gimtse recording d'in dai-dai nan yana murmushi da kallon Alhaji Darma dake tsuma dukan jikinsa na 6ari. Cikin d'age gira Galadima yace, “wannan ma ba matsalata bace? Kasanfa shikad'ai ya isheni hujjar gurfanar dakai gaban K'uliya, shikenan babu girma babu mulkin da ake mana Homa da tak'ama dashi right? ”. Mi Nuren zaiyi kuwa inba Bushewa da dariya ba, dan yatuna Alhaji Shehu ne yafad'ama Galadima maganarnan randa suka kamoshi. Cikin Fusata Darma yake kallon Muftahu da Nuren dake dariya, ya mik'e tsaye yana nunasu da yatsa, “y'an samari lokacin dariyarku baiyiba, dan camera d'in da kuke farfagandar nema tana gab da zuwa hannunmu, kunga kuwa ai kune abin dariya”. Ya k'are
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83