Chapter 78
Chapter 78
kalleni, kafin nace wani Abu sai kawai ya rungumeni tsam a jikinsa, sai kace zai maidani cikine, kusan mintuna 3 muna a haka, sai sauke tagwayen ajiyar zuciya yakeyi, nikam ina shafa gadon bayansa a hankali. Nutsuwar daya samu ta sakashi d'ago muka zubama juna ido, murmushi mai kashe zuciya namasa ina shafa sajensa, cikin sanyin murya nace, “Waye ya ta6amin Barden gagara badau ne?”. Lips d'insa ya ciza yana rik'e hannuna, cikeda damuwa yace, “Munaya sosuke kawai sudawo da abinda ya wuce”. Nace, “Mikenan?”. Ya sauke nannauyan numfashi ya zamewa ya kwanta, kansa bisa cinyata muna kallon juna yacigaba da fad'in, “Akan mulki mana, tun sanda Abie ya dawo na fuskanci Abba nason maida masa mulki, amma mama Fulani na hanashi, sannan a gefe mahaifiyar su Matawalle tana nata k'ulle-k'ulle, dama kwanaki mun fara maganar ni da Momma da Abie, saboda rikicin dake Neman 6arkewa tsakanin mama Fulani da mai martaba, a lokacin bansan kuma miya dakushe lamarinba, sai yau da rana tsakarnan mai martaba yace zai maidama Abie sarauta, wannan shine mak'asudun zaman gaggawar, kinsan kuwa wannan kujerar itace ke hana kowacce masarautar zaman lafiya da hargitse-hargitse, harta kai ga asarar rayuka, shiyyasa da Sarki yafara ciwo burin kowa ya mutu hattada y'ay'ansa da matarsa mai manyan y'ay'a saboda burin y'ay'anta su gaji mulki? Wlhy ina cikin tashin hankali, hankalinmu ya kwanta kowa yasamu nutsuwa a masarautar nan gawani bala'innan zasu 6alloma mutane, inaga kawai zamu tattara mu koma India harsu Abie da zaran anyi bikin Sauban. Da aunty mimi”. “Ina bayanka wlhy my king, wannan itace babbar mafita kawai, domin cigaba da samun zaman lafiya mai d'orewa, hukuncin daka yanke yayi sosai”. Ya lumshe idanu da shafo fuskata saboda jin dad'in goyon bayan dana bashi, domin k'ara masa nutsuwa saina d'ora bakina akan nashi nashiga masa wani salo mai cikeda kwarewa fiyeda yanda ya koya min, tamkar jira yake ya birkicemin, kafin kicemi labari ya canja salo, saigani da sake sabon wanka babu shiri.🤭 Tun daga ranar bamu sake jin maganarba daga bakin manya, sai munafunce-munafunce da sukaita wanzuwa, bakuma mujiba daga bakin Abie ko papi, dan aranarma ya koma inda ya fito, wannan dalilin Galadima ya samu yafara shirin komawarmu India da Zarar an kammala bikin Sauban daya rage sati biyu kacal. Ana saura kwana biyu d'aurin aure ya zauna da bayin ALLAH da suka hidimta masa akan su tanderu. Baffi, Baba Rabilu, Badi, Muftahu, Nuren, Saleem, Sir isa, su Ameer. Dukansu ya bisu da k'yauta ta girma, tare da musu godiya ta musamman mara iyaka, yakuma y'anta Badi tare da k'yautar muhallin zama mai nagarta a cikin masarauta, hakama sarkin mota, ya basu hak'uri bisa ga jinsa shiru, abaya tattalin arzik'insa ya raunana ne, koyace zai karramasu bashida k'arfin hakan, amma yanzu kam alhmdllh komai ya dai-daita. Suma sun masa godiya ta musamman a garesa da k'yak'yawar Addu'a, daga k'arshe ya kaisu ga Abie da Momma, sunci abincin rana tare da adalin tsohon Sarki wato Abie, sannan suka sha hira, dama kowa yasan Shiba mutum bane mai girman kai, ga yawan tsokana, shima yamusu k'ayuta ta musamman, hakama Momma tayi nata. Washe gari ana gobe d'aurin aure kenan da tashin hantsi yasakani shiryawa wai namasa rakiya wani waje. Kamar ko yaushe Sarkin Montane ke Jammu, yayinda dogaransa ke binmu a baya. Mun Isa wani waje kusada birnin gayu plaza, wajen ya had'u iyakar had'uwa, a da shagunane kawai a wajen, amma yanzu kamar an rushe anyi wani gini na musamman. An saka k'aton allo mai d'aukeda hotunan kayan gyaran gashi dana kwalliya, an rubuta *_LADIES MIRROR_* da manyan haruffa, hakama jikin k'ofar wajen dayasha glass, an saka babban allo a sama mai kawo wuta da d'aukewa, shima dai irin rubutun farkone a nan, wato *ladies mirror*, abin ya k'ayatar dani, yana rik'e da hannu na muka shiga. Ashe wajene na musamman na gyaran irin duk Wanda mace take buk'ata, gyaran jiki, saloon, kwalliya, kunshi, dakuma waje na musamman da kayan shafe-shafe na kwalliyar mata ake siyarwa, da glasses aka rarraba shagon, kowanne da 6angarensa, bayan ka fara iske reception a farko, sai office dayaji komai zam dake can k'arshen shagon, shima dai duk glass d'inne, amma daga ciki zagaye yake da labuloli, ba'a buk'atar ganin Wanda zai zauna a ciki kenan. Bayan mun gama zagaya ko ina muka Isa Office d'in, Galadima ya saka hannu ya yaye wani allo da aka lullu6e da farin k'yalle. Kallonsu nayi da mamaki, saiya nunamin rubutun jikin allon.. *_“Wannan tukuycine a gareki my mata, badan biyanki hidimar da kike daniba, dan idan biya zanyi abinda na mallaka kaf bazai iya biyankiba matata abar k'aunata, bugun zuciyata komaina Munaaya”._* Da tsantsar mamaki na d'ago ina kallonsa, yad'an ta6e baki da d'agamin kafad'a alamar gaskiyar kenan. Kawai jinai hawaye sun gangaromin, na fad'a jikinsa ina sakin wani kukan farin ciki. Hannu biyu ya saka ya rungumeni yana murmushi, sannan ya jani muka zauna bisa sofa guda d'aya dake a office d'in, ban tsaya wata-wataba na manna la66ana saman .....🤭. Caraf ya cafke tamkar dama jira yakeyi, gaba d'ayama mun manta a inda Muke, mun tsunduma duniyar masoya wad'anda suka soyu a soyayyarma, saida naji yana Neman kauce hanya sannan na dawo hayyacina. Na kuma rungumarsa tsam ina jero masa godiya wadda nama rasa wace iriya zanyi masa yasan naji dad'i. Ya rik'e fuskata cikin tafin hannunsa yana bina da kallo, “My mata babu godiya a tsakaninmu, inma akwaita to nine ya cancanci nayi miki, domin kinmin abubuwa da baki bazai iya lisafosuba, kedai kawai ki rik'eni Amana ni da yaranna da k'anensu masu zuwa, idan kinkai hakan kin gamawa Muhammad Sameer komai, na haramta miki yimin godiya inhar akan wannan d'an wajenne”. Ya kamo hannuna yana zaro key d'in mota a aljihu ya d'oran a hannu. Kallonsa nayi sannan na kalli hannayenmu, ya d'aga min gira da cije lips sannan ya mik'e. Tamkar sokuwa haka na bisa da kallo, gaban loka k'arama dake office d'in ya nufa, ya kwaso wasu file ya dawo inda ya barni tamkar wata gunki, d'ayan hannun nawa ya kamo yana d'oran files d'in, “Wannan sune bayanai da form na ma'aikatanki, angama d'aukar kwararru a kowanne fanni, wannan takardun wajene da kowanne lasisinsa, ko gobe kika shirya ma'aikata zasu fara aikinsu.................✍🏻 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏼 [8/22, 8:36 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* *_💡HASKE WRITERS ASSO...._* *_♦RAINA KAMA...!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_BOOK 3_* 👉🏻3⃣2⃣ *_🔚END!! 😢✋🏻_* ...............Ban San yanda zan musalta muku halin dana tsinci kainaba bisa ga wannan tukuyci na Galadima, saidaifa kafin wani dogon lokaci dukkan Wanda keda alak'a dani yasan da zaman wannan k'yauta, y'an uwa sai tayani murna sukeyi. Y'an gidanmu dai saida sukaji wannan bak'ar al'adar tasu ta hassada, amma sun d'an danne zukatansu sukaimin murna. Washe gari bayan d'aura auren Sauban da aunty mimi Galadima yaja gayyar abokansa da yayuna sukaje aka bud'e wajen saloon d'ina. Akuma ranar ma'aikata suka fara gudanar da aiki, dan a can naje na iske Galadima ni da tawa tawagar, na gana da dukkan ma'aikatana tare da basu umarnin duk Wanda ya shigo wajen a ranar amasa abinda yakeso k'yauta, Washe gari sai a fara na kudi. Bikin Sauban ya gudana cikin k'ayatarwa, itadai aunty mimi koda aka d'aura auren shikenan, tace wane biki kuma a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83