Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 52

Chapter 52

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

nazo gareshi. Tamkar mai tsoron a kamata tana satar naman miya haka nake tafiya garesa, dan kallon da yakemin ba k'aramin haddasamin kasala da sanyin jiki yayiba. Na k'arasa gabansa ina zama a kasalance, zaman danayi ya kalla, ya min jinjina irinta saraki👍🏻. Kallon kaina nayi nima, dan banga minayi ba dahar za'amin wannan jinjinar. Cikeda k'asaitarnan tasa yace, “Kallon fa?”. Ajiyar zuciya Na sauke, dan narasa bakin magana, ya tashi zaune sosai yana janye tum-tum d'in dake a tsakkiyarmu, ya matso jikina sosai yana wani shinshinata da lumshe idanu, murya a sark'e yace, “Amaryar Muhammad Sameer wannan k'amshin yayifa 100%”. Yanda yay maganar a dokin wuyana saida tsigar jikina ta tashi, cikin magana d'ai-d'ai nace, “Wai dama Kaine d'an Sarki da aketama wannan shirin?”. Murmushi ya saki, ya matsar da bakinsa saitin kunnena a wani salo yace, “koban cancantaba ne?”. Kaina Na girgiza masa alamar a'a. Ya kuma shigewa jikina sosai, “Wai miya kashe bakin tsiwarne haka yau?”. “Mamaki mana”. “To miye abin mamakin? Ni d'in ko zuwan nawa?”. Nace, “Duka”. Wani miskilin murmushi ya saki, ya lalubo hannuna dake 6oye cikin alk'yabbar ya saka nashi ciki yana murzawa da wani salo, juyawa nayi Na kallesa muka had'a ido, idanunsa duksun wani k'ank'ance, ya sark'e nawa yanda nakasa koda motsi balle samun damar janyewa, akan la66ansa yace, “I miss you”. “Humm” nafad'a nima a hankali INA kauda kaina gefe. Hannunsa ya sak'alo ta bayan wuyana ya matso da fuskata dab da tashi, numfashinmu Na had'uwa waje d'aya, kasa jurar kallonsa nayi saina lumshe idonuna Na bamik'a masa wuya 100%, yayi duk yanda yakeso, dan da gaske missing d'in nawa mai yawa Nagano cikin kwayoyin idanunsa. Da sauri yarima Issufu da Yaa Marwan suka koma baya, dan dama suna tare da shine aka aiko kiransu, sunata sauri su dawo dan karsu barshi cikin kad'aici, ashema yana tare da matarsa. Sunyi sallama takai 6 jin ba'a amsaba sukayi tunanin kobaijibane, shiyyasa suka shigo Kansu tsaye, dan basuyi zaton samunsa da kowaba, ALLAH ma ya sosu k'aramin gani sukayi🤭😂. Yareema Isaufu da mamaki ya kasheshi ya kalli Yaa Marwan yana fad'in, “wai dama duk yarannan masu kama da juna sunada aure?”. Murmushi Yaa Marwan yayi, ya dafa kafad'arsa, “biyu sunada aure mana, su tagwayene, ina auren Hasaanar, shikuma Yarima Sameer yana auren Hussaina, d'ayar itace bata da aure, dan nasan Ayusher kake nufi, tunda Feena bata kaisu girma da shekaruba, amma miyasa kamin wannan tambayar?”. Yareema Issufu yay k'aramar dariya yana cewa “zan sanar maka amma ba yanzunba, saida safe Na banbancesu”. Komai Yaa Marwan baiceba yay murmushi kawai suka cigaba da tafiya. Mukan bama musan sun shigoba balle fitarsu, motsawar da Abdurrahman yayi yana k'ananun kukane yasamu dai-daita, duk muka kalli inda suke. Matsawa Galadima yayi inda suke dan sunfi kusa dashi, Ashe showal d'inne ya rufe masa hanci, ya gyara masa sannan ya juyo ya kalleni yana murmushi. K'asa nayi da kaina nima ina murmushin. Nace, “Ina yini? Kazo lafiya?”. “Kin fita daga mamakin yanzu dai kenan?”. Yay maganar tamkar bayaso. Nanma Murmusawa nayi ina 6oye fuskata. “Humm”. Ya fad'a yana gyara zama. “Kayannan sun miki k'yau gaskiya my mata”. Nad'an d'ago ina fad'in, “Da gaske?”. Ido d'aya ya kashemin yana cizar lips. Nima Na juya idanuna cikeda salo. Har cikin ransa saida yaji wannan sak'on. Na katse masa tunanin da fad'in “Ya jikin Abie?”. Zamansa ya gyara sosai, ya d'auki butar shayin zai zuba nai saurin d'aura hannuna akan nasa ina girgiza kai. “Aikin ai nawane yalla6ai”. Murmusawa yayi yana sakarmin. Nima Na zuba masa fuskata d'auke da Murmushi, Na mik'a masa. Cikin lumshe idanu yace, “Thanks”. Kaina Na jinjina masa kawai, a nutse ya shiga bani labarin dukkan abinda ya faru, harda tsadar allurai da drugs d'in da Abie kesha, ya k'are maganar da fad'in ammafa Alhmdllh, bazan baki labarin komaiba sai kinje kinganema idonki yanda Abie yake yanzu, banta6a tafiya mai cike da nutsuwa ba irinta wannan karon, dan nasan nabaro farin ciki ne zan kuma iske farin ciki, lallai Na yarda da zancenki, HAK'URI shike bada komai, duk saurin Bawa saiya jirayi UBANGIJI, dan shine mai kowa da komai, a watanni biyu kacal da suka shud'e ganinake komai ma bazai zoba balle ya wuce, amma gashi harya zama labari, wataran muma masu bada labarin nemarmu za'ayi a rasa, mun shud'e saidai bayanmu, ALLAH ka rabamu da SON ZUCIYA, dan k'arshedai 6ACINTA, Ko'a yanzu akace babu Muhammad Sameer to naci ribar rayuwa, dan burina nason ganin mak'iyan mahaifina ya cika, Abie yasamu sauk'i, ga yarana, Na mallaki jarumar mace kamila Mumina wadda Na mallakama dukkan kaina da ZUCIYATA, To nikam minene ya ragemin kuma MATATA!?”. 'Dago idanuna dake cike da kwalla nai ina kallonsa, a hankali nace, “Sai addu'ar samun aljanna my King”. Ya lumshe idanunsa yana murmushin daba koyaushe yake yinsaba yana min jinjina 👍🏻. Nima na jinjina masa ina k'aramar dariya. Muncigaba da hirarmu a tsanake cikin so da k'auna da nunama juna kulawa. Yauma langaremin yayi saida nabashi abinci da kaina yaci, nima dai haka ya ciyar dani da kansa. Ban bar sashenba sai wajen 12, shima su Yaa Marwan muka tausayamawa, dukda kowa da d'akinsa, falone kawai ya had'asu. Da kansa ya d'akkomin Absurraheem da Amaturrahman, ya rakoni, aiko muna fitowa yace, “ya salam, my mata dama haka wajennan keda sanyi?”. Cikin tausayawa Na kallesa, dan nima Na manta kayan dake jikinsa k'ananune, dan ciki akwai d'umi sosai, bama zaka tuna ana sanyiba, “kawosu kawai ka koma, kar mura ta kamaka”. “No muje da sauri Na rakaki, dan sunmiki yawa ai”. Har k'ofar sashen da muke ya min rakkiya, Na lek'a Na kira Wanda ke kusa danya taimaka min, Ayusher Ce ta fito itada Zuhuriyya, Na kar6esu d'ai-d'ai daga wajensa ina mik'a musu, yayinda suke gaisheshi sukuma yana amsawa da kulawa. Suna shigewa ya jawoni jikinsa, waige-waige Na fara dan gudun kar wani ya gammu, shikam ko'a jikinsa, ya mannani da gini yana yanda yaso, kusan mintuna 2 sannan ya sakeni yana fad'in “Good night”. A hankali tare da d'agamin yatsunsa biyu. Kasa magana nayi harya 6acema ganina, Na sauke ajiyar zuciya ina shiga ciki a sanyaye tamkar wadda tama sarki k'arya. Duk sunyi barci, sai Ayusher da Maryamu da Zuhuriyya ne kawai ido biyu, sai bina da wani kallon tuhuma suke. Na zauna ina fad'in, “waiku lafiya kukemin kallon har hanji?”. Dariya suka sanyamin, Ayusher tace, “Hajiyata ina janbakin Dana Sanya miki?”. Harara Na zuba mata nace, “oho miki sa idiniyya”. Natashi nai shigewata. Aiko mizasuyi inba dariyaba, nima Na shige ina k'unshe tawa. Shirin barci nayi nai kwanciyata, har suka shigo suka kwantar da yaran ban kulasuba saima nayi tamkar barci nakeyi. Dama Laraba Na iske tayi barci abinta ita tuni, Na dad'e banyi barciba, kasancewata tare da Galadima ta tsayamin arai, kai wannan Bawa akwai iya salon d'auke zuciya iri-iri, duk hanyar dazaibi ya dabaibayeki ya Sani. Shima a 6angaren Galadima da k'yar yay barci, da badan kar ace yayi abin kunyaba da babu inda matarsa zata ta barsa, yana buk'atarta a kusadashi ainun, amma ya zaiyi, dolene ya had'iye kwad'ayinsa harsu dawo kusa dashi. Haka yayta juye-juye harya samu barci ya d'aukesa. *_Washe gari_* Ban samu damar ganin Galadima ba har a zuhur, dama gashi an tashi da sanyin

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});