Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 21

Chapter 21

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

saka bottoms d'in a tsananin hanzarce, haka dai ya k'arasa shirin a gaggauce, ya d'auki abinda zai d'auka yafito, babu gaisuwar Wanda ya amsa, hannu kawai ya d'aga musu yanufi mota yashige da kansa yaja ya fice daga masarautar, Wanda yatafi kiran Sarkin Mota duka iso tare, duk mamaki ya kamasu, yau Galadima da kansa yaja mota, anya kuwa lafiya?. Ganin wannan bazai musuba sarkin mota ya shiga mota shima ya bishi. Yana tuk'i suna waya da Vijay abokin aikinsa Na India, a haka ya iso gidansa dake bayan gari, kusan lokaci d'aya suka Isa da sarkin mota, ganin Galadima zai fita ya bud'e gate da kansa, shi saiya kashe motar dayake ciki da sauri ya fito yazo ya bud'e masa ya shige, bai bisaba, tunda Alhmdllh yaga dai inda yazo, maybe kuma baya buk'atar kowa a wajene shiyyasa ya buk'aci tahowa shi kad'ai. Wani d'aki dake cikin bedroom d'in gidan ya bud'e ya Shiga, bazaka ta6a tunanin akwaima d'aki a wajenba, da y'ar k'ura a d'akin, amma hakan bai damu Galadima ba a yau, k'yallen da aka rufe kujeru da Computers d'in d'akin yashiga yayewa, da sauri ya fito zuwa can bayan d'akunan, yad'anyi ajiyar zuciya saboda ganin Gen... d'in gidan akwai fetur, dayake yad'an zazzo gidan kwannan, tadawa yay ya kuma komawa cikin gidan, ya kunna komai sannan ya zauna a kujera, medical eyeglasses ya saka, idonnan yayi jazur saboda 6acin rai, duk jijiyoyin kansa sun mimmk'e, hakama gashin jikinsa, kallon farko zai tabbatar maka ran maza ya 6aci. Koma a yanda yake sarrafa Computers d'in. Abinda ke kunnensa kawai naga ya danna yanayin kwatancen d'akin da za'a sameshi. Mintuna 3 tsakani saiga Sir Isa da Baffi sun shigo, saikuma ga Sauban Wanda harsun d'auki hanya Muftahu ya kirashi akan ya dawo, dole ya dawo masarauta, shine suka fito shida Muftahun. Sir Isa da Sauban duk zama sukayi, Galadima Na Sanar musu abinda zasuyi. “Gaskiya shegene guy d'innan yalla6ai, wlhy yasan Computer, kagafa yana Neman lalata mana dukkan security d'inmu.......”. ‘hankali tashe sir isa yake magana. Sauban kam har kwalla ta cika masa ido. Galadima baice komaiba, aikinsa yake iya iyawar k'arfin zuciya dana k'wanji. Sai Baffine yad'an bubbuga kafad'ar Sauban yana fad'in “ka kwantar da hankalinka Sauban, insha ALLAH bazasuci nasaraba, kacigaba dayin komai a nutse kaidai”. Sauban ya kad'a kansa yana share hawaye. Galadima dayay zufa sharkaf ya kalli Sir Isa, yarigada yaci k'arfinmu kafin muzo, k'ofa ukuce kacal ya rage masa bud'ewa yasamu dukkan komai, abinda zamuyi mu bud'e masa sauran kawai, bayan yashiga ciki insha ALLAH inada wata dabara”. Muftahu yace, “Amma Ranka ya dad'e hakan riskine gaskiya, idan kuma shi yanada plans akan hakan fa?”. “Gaskiya ka fad'a Muftahu, amma hakan shine kawai hanya mai sauk'i da zamubi, inhar muka bari harya bud'e da kansa lallai zai lalata komaine, Dan wannan shine shirinsu”. Sir Isa ne mai maganar. Galadima ya danna abin kunnensa yana fad'in “Vijay mubashi dama kawai, a lokacin daya shiga kaikuma ka tabbatar da ka zuk'e dukkan nasa shirin, ga wata akwatinan dayake yawo da ita a bayan handle d'in Computer d'insa, karka ta6ata Dan makircine ya shirya a cikinta, munayin kuskuren ta6awa labari zaisha Banban. Alex yay gaggawar had'amin sabbin Securitys muga kozasu ja hankalinsa can, ga hoton yaranan zan d'ora masa, dasu zaiyi amfani, dan dolene mu kauda masa hankali, yasan mi yakeyi sosai”. “Ok! Ok! muje zuwa kawai” vijey ya amsa a hanzarce. Da sauri Galadima ya maida kallonsa ga Sauban yana fad'in “dakaje duk ka d'auki su Amaturrahman ne?”. “Eh yaya dukna d'aukesu”. “A lokaci d'aya ko daban-daban?”. Na d'aukesu lokaci d'aya, nakuma d'auki kowa shi kad'ai”. “Alhmdllh taso nan”. Tashi Sauban yayi ya matsa inda Galadima yake, wani glass Galadima ya tura masa, yace, “'Dora duka hannayenka anan mugani”. 'Dorawa Sauban yayi, bayan ya ta6a wani farin Abu da Baffi ya bashi, shatin hannun yaran suka bayyana, dayake yayi musu wasa sosai, amma kuma hakan bazai gamsarba. Daga can Alex yace bazaiyiba, dole akawo yaran. Shima Galadima ya tabbatar bazaiyinba, sai hankalinsa ya kuma tashi, yaran sunyi k'ank'atar daza'a fito dasu daga gida. Muftahu yace, “Ranka ya dad'e bara kawai naje Na kawosu inaga zaifi sauk'i”. Baffi yace, “hakan shine kawai dai-dai sai dai bakai yakamata kajeba, a kira mahaifiyarsu tabama Wanda zai iya 6adda bamanni wajen kawosu, kuringa tunawa sumafa idonsu nakan kowane motsinmu a yanzu, shiyyasa tun a jiya naima Sameer hannunka mai sanda akan hakan”. Galadima daya zubama Computers d'in ido kawai yana kallon 6arnar da ake shirin masa. Ya mik'e tsaye yana fad'in “Muftahu ka kira mai taxi d'innan yaje inda yata6a ajiyeta za'a kawo masa yaran”. fitowa yay daga d'akin yana k'ok'arin neman number Munaya ya kira. Bugu biyu Munubiya da wayar ke hannunta ta d'aga, tana mannama Munaya wayar a kunne, bai amsa sallamarta ba yace, “Yanzunnan ki bama Innaro da laraba su Abdurraheem, sufito bakin layinku akwai mai taxi zai d'akkosu”. Cike da mamaki Munaya tace, “yalla6ai ban ganeba?”. A tsawace yace, “basai kinganeba, Dalla malama kibasu karki 6atamim lokaci”. Sosai Munaya ta tsorata da tsawar tasa, kad'an yarage wayar ta su6uce mata ta daiyi azamar rik'ota, batada za6in daya wuce bin Umarninsa, dukda hankalinta bai kwantaba da hakan. Yanda yace ayi haka tayi, innaro da laraba Na fitowa suka samu mai taxi yana jiransu. Cikin mintuna k'alilan suka iso, Muftahu da Sauban sukazo suka kar6i yaran, akabar su innaro a mota zasu jira. Akan wani Abu akad'an d'orasu, da hotonsu ya fota a Computer d'in sai'a ciresu, sud'uka duk aka d'ad'd'orasu, sannan su Muftahu suka maidasu wajensu innaro aka koma dasu. Sudai duk mamaki ya cikasu akan miya faru? Basuda mai basu amsar wannan lamari. Bayan su Galadima sun turama su Alex hotunan yaran sai duk suka koma gefe suka zubama Computers d'in ido, sauran lamari sunbarma ubangiji. Suna kallo wancen ya shige inda yakeso, bayan sun bashi dukkan dama, tashin hankalin Galadima shine, mutumin lalata komansa yakesonyi bawai d'auka ba, idan da ace d'aukace hakan mai sauk'ine, k'iris yarage wancan ya cinmusu, Galadima ya lumshe idonsa zuciyarsa Na k'una yana ambaton sunayen ALLAH, abinda ya d'auki tsawon shekaru yana tanadinsu ga wani banza zai gogesu cikin seconds, hakan ya tabbatar masa da Harun ne yabada wani yanki Na sirrinsa, saboda yasan abubuwa da yawa akan aiyukansa, sauban ma k'asa yay dakai yana hawaye, shikenan dukkan hujjojinsu da suke ganin zaisa su samu a hukunta masu laifi suntafi, baffi da sir Isa da Muftahu ma duk jikinsu yayi sanyi, kowa sai zuciyarsa Ce ke bugawa...... Sauban yace, “Yaa Sam!”. Galadima ya tashi zaune sosai yana bud'e ido da kallon Sauban, batareda ya amsaba. Sauban yace, “yaa Sam mizai hana mu gwada dabaran kashe Computers d'insu, kaga seconds 30 kawai yarage ya cimma burinsa”. Ajiyar zuciya Galadima ya sauke, murya a sark'e yace, “Sauban abinda ya rage mana yayi kad'an wajen yin hakan, kuma zamu iya kuskuren da komai zai goge d'in da kanmu, kubarsa kawai yayi yanda yakeso......” Katseshi baffi yay da sauri, “Sameer mu gwad'a d'in kawai, maybe a samu dacewa”. Badan Galadima yayi tunanin samun nasaraba yatashi zaune jiki a sanyaye yana dannawa, Sauban yakuma fad'in “yaya Please kayi da yak'ini, saura 20 seconds fa”. Tamkar Sauban yayima Galadima allura ne, yafara komai cikin hanzari,

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});