Chapter 31
Chapter 31
sashen dayake gulma, sunyi gungu-gungu suna tayi, sai anga wani babba zai wuce saikiga an watse. Mai martaba ya kira papi, dukda yasan shima yaga komai, bayan sun gaisa a mutunce irin gaisuwar d'a da uba, suka shiga tattauna abinda ke faruwa, papi yace, ya kirashi amma wayarsa a kashe, yakira Nuren ma shima waya a kashe, Dan yasan lallai a tare suke shuka wannan tsiyar. Mai martaba yace, “To amma Abba kaga kuma yanzu ga surukin namu sun fiddo kamar yanda ya buk'ata. Ina ganin akwai wani Abu da Sameer keson ankarar da jama'a Wanda mu bamu San dashiba, nasan halin yaronnan yanada k'yawawan halaye ababen koyi......”. Cikeda 6acin rai papi ya katse mai martaba, “Jalaludden komai k'yawun halin Muhammad a yanzu ba kowane zai gansu koya yarda dasuba, dukda inaji ajikina bawai ganganci ya sakashi yin hakanba, dama yanada hujja, amma miyakai Na kisa?, a labarai sun nuna ya kashe yaron Alhaji Bana, shin wannan halin mutanen kwaraine? Wannan hanyar dayabi fa bazata ta6a 6ullewa da shiba sai 6ata masa suna damu kanmu, daga fitowar maganarnan zuwa yanzu nasamu kira babu adadi”. Mai martaba yace, “kayi hak'uri Abba. Insha ALLAH zan shirya naje wajen zuwa anjima kad'an”. “Shikenan. Idan naga nima abin yayi tsamari zan taho”. Sallama sukayi kowa yana jimami akan lamarin. Tunda labari yakaima mama Fulani tashiga tafa hannu tana sallallami da fad'in “A lallai zai iya zai aika, yo wannan yaron mai ido a tsakar goshi, fitinanne zai 6atama masarautarmu suna akan wani banzan talakan surukinsa, akuwa yanda ya kashe d'an mutane shima kasheshi za'ayi, idan munan ya rainamu yanzu kam ya d'ebo ruwan dafa kansa, fand'ararre kawai gagararre”. Haka taita k'ananan magana da jifan Galadima da munana. Oho shi baimasan tanayiba☹😏. ******************** A asibiti likitoci sun Shiga bama Abba taimakon gaggawa, Dan ba'asan minene ya sumar da shiba, tunda babu wani alamar duka ko harbi ko makamancin wannan a jikinsa.. ************** Suma police sun buk'aci Galadima ya basu gawar Ahmad. Murmushi yay yana kallon Ahmad d'in dake zaune yana shan ruwa saboda tsoratar dayayi sosai ta harbin da Galadima yayi, har yanzu yakasa sakin jikinsa, salla ma da sukayi a d'arare yayita, yazata da gaske shid'in aka harba, saida Galadima yayma Saleem nunin abashi ruwa, Saleem yakawo ma Ahmad ruwa, a lokacinne ya farga da Ashe yanada rai bai mutuba🤣😜. Ya kar6i ruwa kuwa jiki Na rawa ya shiga kwankwad'a idonsa akan Galadima dake masa murmushi, yana bama su IG amsa da fad'in “karku damu yalla6ai. Inada freight d'in dazan dunga saka gawarsu anan, bayan aiki ya kammala saisu d'auki y'ay'ansu sumusu sutura, idan kuma sunyi abinda nakeso kaga magana ta k'are, gawar Ahmad kawai ce a k'asa dai yanzun, sai idan ank'imin yanda nakesone za'a samu fiye da hakan dai”. C.P ya jinjina kai yana gyara tsayuwa, idonsa nakan ginin, yace, “to miye buk'atarka ta gaba yanzu?, tunda gashi an maka ta farko ai”. “Eh tabbas anmin, dukda dai ankawoshi ba'yanda Na soba”. “amma ranka ya dad'e suma ai ankashe musu yaro d'aya”. Gira Galadima ya shafa da d'an yatsa yana ta6e baki, “ito dakuma wannan Dan wannan fa, yanzu dai inaga buk'atata tagaba shine ku kama mutanen nan guda 11 dazan lissafo”. “Muna saurarenka, dawa-dawa?”. Ajiyar zuciya Galadima ya sauke, cikin Nisawa ya gyara zamansa yana d'aukar takardar dake gabansa ya shiga lissafosu. “Alhaji Balala, Alhaji Bana baba gana, Alhaji Abdul-Naseer Nafi'u, William Solomon, Hajiya A'i Barnawa, Alhaji Sageer Sulaima Sulaiman, madam Victoria, Mansur Habibu Abu, Josaya bamma, Alhaji Mamman k'afur, Alhaji Halliru garba”. Kallon kallo aka tsayayi tsakanin IG da sauran police, sai C.P ne yasamu k'arfin halin cewa “amma to Ranka ya dad'e akan wane dalili? Kasan dai bazai yuwu muje kama mutane babu dalilin komai damuka saniba”. Wani muskilin murmushi Galadima yayi, ya kwantar da kansa jikin kujera yana lumshe ido da cije lips, “Dalilin ai a fili yake yalla6ai namu, bisa dalilin Samun Alhaji Auwal Fharuk a hannunsu mana, dan yakamata asan dalilin samunshi a hannunsu, miya musu? Mi suke nema a wajensa? Baniba nasan dukan jama'ar garima abinda sukeson ji kenan, kunsan dai bazan ajiye ayukan gabana da jiyyar mahaifina nazo Nigeria Na zauna Ina kama yaran mutane saboda rashin aikinyiba ai, aimin kokuma nakuma aika yaronsu biyu barzahu yanzunnan!!”. Galadima ya k'are maganar cikin tsawa da matsanancin fushi. Tsawarsa saida ta kad'a hanjin yaran, hatta da Harun dasu Muftahu saida suka rumtse ido, suma haka police d'in dake sauraren Galadima. IG ya mik'e daga zaunen dayake yashiga safa da marwa Na mamakin wannan lamari, sukan ai ansakasu a tsaka mai wuya, cikin tsakkiyar fad'an manya. C.P ya kira suka koma gefe suna tattaunawa. ............................★ A can kuwa hankalin su Alhaji Sageer ya kuma k'ololuwar tashi, Alhaji Mamman yace, “lallai yaronnan anyi tsinanne, dama wannan ranar Na ringa gudu tun boss nada rai (tanderu yake nufi), amma wasunmu sukace yaron bai Isa mana komaiba, gashinan rana tsaka yana Neman zame mana RAINA KAMA....” “Yama zama ai, Dan gayya kawai muka fara gani yanzun”. ‘Hajia A'i ta fad'a a tsorace’. Duk sun kasa zama waje d'aya, Miracle yace, “yanzu nan da mutuncinmu za'ace wai y'an sanda su kamamu a k'asarnan?, lallai yaronnan yataro March wlhy”. “Kokuma mune muka taro March d'inba”. Alhaji Bana dayake cikin kukan mutuwar d'ansa yafad'a yana share hawayen. ...............................★ IG sun yanke shwarar bin umarnin Galadima kawai, kodan tseratar da yaran, yad'anyi magana da manyan dake kusa dashi dukda shine Oga kwata-kwata, kowadai yabada goyon bayan a kamasun kawai. Dan haka IG da kansa yay kiransu, Yakuma basu dama a girmamame akan sukai Kansu kawai station d'in dake kusa dasu, kodan rayukan yaransu, daga baya za'asan abunyi insha ALLAH”. Galadima dake saurarensu a zuciyarsa yace, abinyi kuma ai saidai a prison. Duk sunk'i amincewa, wasunsuma sai bak'ak'en magana suke fad'a. waya Galadima ya jawo yana daddannawa, sannan yayma Marcel nuni yazo, Dan yaji babansa yafi kowa zak'ewa, jikin Marcel sai 6ari yakeyi, ahaka ya rarrafo gaban Galadima. Galadima yace, “'Dauka wayarka anan”. Jikin Marcel na rawa ya d'auka. “Kira daddynka”. Dandanan yay kiransa, bugu d'aya kuwa ya d'auka shima jiki yana 6ari, duk suma sukayi tsitt suna jiran mizaice. Galadima ya d'orama Marcel binduga a tsakkiyar kai, ya juya idanunsa alamar yay magana. Marcel ya sanya kuka saboda tsoro. Rikicewa daddynsa yayi yana tambayar mi aka masa? Badai yay musu komaiba ba ko?..... Katseshi Galadima yayi da fad'in “Zandai yimasa, Dan kaima yanzu d'anka zai wuce Inda Na Alhaji Bana yatafi”. “kai kai dakata please ka dakata, nidai Na yarda zan mik'a wuya, karka ta6amin yaro kaji Na rok'eka”. Cire bindigar Galadima yay yana maida kunamar da fad'in “shawara mai k'yau, lallai kanason d'ankan nan, ka tambayi abokanka, Wanda bazai mik'a wuyanba saiya fad'a yanzun nan”. “karka ta6a mana yara please, duk zamu mik'a wuya”. Galadima ya tuntsire da dariyar da wanima zai iya rantsewa bai ta6a ganin yayiba, yace, OK, good dattijan k'asa, saina jiku acan”. 🤣🤣ana shagali a Nigeria yau kam🤸🏻♀🤸🏻♀🤸🏻♀🤸🏻♀ amma Nigeria novel ba tamuba😜. Su Alhaji balala dai kam sun mik'a wuya, da Kansu suka kai Kansu police station mafi kusa, daga can suma d'aukesu zuwa inda IG yace. Galadima yay hamdala ga ubangiji dukda bawai komai yagama kammaluwa bane, amma lallai an d'akko hanya. Ya bada Umarnin tashi suyi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83