Chapter 22
Chapter 22
yayinda sir Isa ke taimaka masa. Muftahu da Baffi dai y'an kallone, Dan basusan komai dangane da wannan harkarba. Saura second 1 ya rage Galadima yasamu damar kashe Computers d'insu dana wad'ancan. Suda ke murnar samun nasara duk sai sukayi tsit, su Galadima kuma Sauban ya sanya ihu. Hararsa Galadima yayi, yayinda su Baffi sukai dariya. Dukda suna addu'ar samun nasara hankalinsu bai kwantaba, Dan sai an kunna Computers d'in zuwa wanu lokaci, idan an tabbatar da samun nasara sannan. *************** Hankalim Munaya bai kwantaba saida taga su innaro sun dawo k'alau, babu kunya taita d'aukar yaran tana jujjuyawa wai kozataga wani abinda aka musu, saidai kuma bataga komaiba. *************************** Baffi ya kalli Galadima dayay shiru ido a lumshe, yace, “Sameer dolenefa komai yazo k'arshe yau, kabi ta hanyar da katsara domin zuwansu hannu gaba d'aya, daga baya saimu cigaba da Neman camera, dan Na tabbata bazasu hak'ura ba, shiyyasa tun a jiya Na sanarmaka”. Galadima ya jinjina kansa batare da ya bud'e idoba yace insha ALLAH komai yazo k'arshe Baffi, safiyar gobe zaku tashi dajin yanda ta kasance, Nuren yana hanyar dawowa. Zamu tafi matakin k'arshe yau”. Atare suka had'a baki wajen addu'ar ALLAH ya bada nasara. Galadima ya amsa akan la66a da amin...............✍🏻 Lallai gobe da kallon kenan. Galadima manmu ka cika musu aiki kawai🤸🏻♀🤸🏻♀🤸🏻♀🤸🏻♀. *_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏼 [7/31, 9:08 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* *_💡HASKE WRITERS ASSO...._* *_♦RAINA KAMA...!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* _________________________ _Masoyan RAINA KAMA... Alkairin ALLAH yakai gareku aduk inda kuke❤❤❤❤, bilyn Abdull nayinku fiye da yanda kukeyinta._ *TASKAR LITTATAFAN HAUSA*😘👌🏻 *ZAUREN HASKE*😘 *KUNDIN HASKE*😘 *RAINA KAMA FANS CLUB* GROUP 1,2,3,4,5 duka Na gaisheku, Wanda Na bud'e da Wanda masoya suka bud'e, inayinku over wlhy, I love you irin Trillion's d'inan fa🤸🏻♀😘. *ZUREN BIEBIE ISA*😘👌🏻 *NICE N COOL NOVELS*😘 *PHARTY NOVELS*😘 *HUGUMA CONVERSETION*😘 *RANO NOVELS* 😘 *MANSHAT NOVELS*😘 *XUMUNTA NOVELS*😘 _Aradun ALLAH kunada matuk'ar yawa, gashi bana kusa balle naita jeroku babu gajiyawa, ina missing naku gaba d'aya, irin babu dad'i d'innan😔😂._ I love you all irin manya-manya d'innan😘😘😘😘😘😘😘🤸🏻♀👌🏻 __________________________ *_BOOK 3_* 👉🏻1⃣4⃣ .................Duk da dai sumbar komai a halin k'ila wa k'ala haka kowa yafito jiki a sanyaye, Baffi da Sir Isa suka wuce, Galadima ma kallon Sauban yayi daya zuba uban tagumi, yad'an murmusa yana fad'in “Haba autan Momma, miye kuma Na damuwar haka? katashi kuwuce kawai kar yamma tayi”. Shagwa6e fuska Sauban yayi yana kallon yayansa, yace, “please Yaa Sam kabarni sai gobe saina wuce insha ALLAH”. Galadima yay shiru alamar tunani, saikuma ya girgiza kansa, “uhm-uhm Sauban ka wuce yau, Dan gobennan akwai riski”. Kamar Sauban ya tambaya dai amma yay shiru, yasan halinsa mawuyacine ya sanar masa. Dan haka saiya amsa da to kawai. Badan yasoba yaymusu sallama shima driver dazai kaisa yad'aukesa suka tafi. Ajiyar zuciya Galadima ya sauke, zuciyarsa Na k'una da tsantsar damuwa. tausayinsa ya kama Muftahu dake zaune shima yayi shiru damuwa da tausayin d'an uwan nasa fal ransa. ★★★★★★ Gaba d'aya zuciyar Munaya takasa sukuni gameda yanda taji muryar Galadima, tunda kuma aka maido yaran saita kasa zaune ta kasa tsaye, Munubiya dai da innarsu duk suna hankalce da ita, kamar Munu zata shareta saidai tamata magana. “Nikam aganina da wannan zagaye-zagayen da kiketayi Sweetheart ai gara ki kirashi kisan damuwarsa, koma ladan kwantar masa da hankali k'yasamu”. Munaya dake kwance akan gado ta kifa meenal saman cikinta datai barci ta kalli Munubiya, amma sai munu ta basar tamkarma ba ita tayi maganarba. Ajiyar zuciya Munaya ta sauke, yayinda Munubiya ta tashi tamayi ficewarta daga d'akin duka, harta fice Munaya nabinta da kallo, saida tabar ganinta sannan ta janye idonta a k'ofar tana cigaba da shafa bayan meenal. Shawarar Zuciyarta dake cigaba da k'arfafa mata shawarar y'ar uwarta ta addabeta da k'awato mata Galadima a damuwa, da alk'awarin dataima Mahaifiyarsa. Kasa daurewa tayi saboda tausayin ahalinsa dashi kansa daya kamata, ta jawo wayar tana lalubo number sa, dukda k'irjinta Na dukan gama-goma Na tsoron tsawar daya mata d'azu da yanda suka rabu jiya. Haka dai ta dake tayi dialing number sa. Galadima suna zaune cikin halin shiru da Neman mafita a zukata shida Muftahu kira ya shigo wayarsa, sharewa yay tamkarma bai jiba, ganin zata tsinke muftahu ya taso yay picking da sauri ganin *My Mata* yasan dai Munaya Ce, a kunne ya saka masa, Galadima ya bud'e jajayen idonsa ya kallesa, Muftahu yamasa alamar please da fuska. Baice komaiba ya kar6a wayar yana maida idanunsa ya lumshe, Muftahu kuma ya fice abinsa. Munaya tayi shiru takasa magana, kamar yanda shima yak'i cewa k'ala, sai sautin ajiyar zuciyarsa take jiyowa kad'an-kad'an, daurewa tayi tace, “Assalamu alaika”. Dukda yasan itace saida yaji sanyi a ransa, Dan ita kad'aice kemasa haka a waya ya jure, saida ya d'auki wasu seconds kafin ya amsa sallamar. Yanda ya amsa sallamar kawai ta tabbatar akwai matsala, Cikin aro jarumta tace, “Ranka ya dad'e barci kakeyi?”. Yad'an murmusa, a zuciyarsa yace yarinyarnan a kwai wayo, “Uhm-uhm”. ‘yafad'a a sanyaye’. Ganin tafara samun dama saita kuma saita muryarta tace, “'Dan gatan Abie, to mikakeyi ne haka? naji muryar taka can k'asa”. Zamewa Galadima yayi ya kwanta cikin kujerar, yanzunma tamkar bazai amsaba, saida ya gama basarwarsa sannan yace, “k mikikeyi?”. Munaya tayi murmushi mai sauti har yana jiyowa, ta shafa kan Meenal tana fad'in “kwance kawai nake ina tunanin rayuwa da abinda ta k'unsa, harma da Wanda ke gudana a cikinta”. Yace, “Humm kamar mikenan?”. “Kanason ji?”. Ya kuma cewa “Uhm”. “humm yalla6ai nakula duk yanda bawa yakai da samun komai Na rayuwa saikaga wata damuwa ko tawaya mai kutse acikin al'amuransa, bana manta maganar nan taka da kata6a fad'amin wani lokacin murmushin da jama'a kanyi iyakarsa fuskane, amma zuciyarsu sune kad'ai sukasan sirinta, lallai wannan gaskiyane, amma kasan mike birgeni da k'aramin k'warin gwiwa a rayuwata koda ace Na tsinci kaina a fagen sanyin jiki?”. Galadima yace, “uhm-uhm”. Munaya ta sauke wata sassanyar ajiyar zuciya da Galadima yajita har cikin ransa, yayinda wani Abu ya tsarga masa ta cikin kai har zuwa yatsan k'afa, ya gyara kwanciyarsa yana jiran jin mizatace. “Komai girman fad'uwa inhar da yak'inin HAK'URI dana k'arfin ZUCIYA to lallai akwai tagomashin sirrin samun NASARA, hak'uri da juriya basa ta6a zama fad'uwa, inhar kaga bawa yayi hak'uri babu kuma NASARA a ciki to lallai hak'un nasa kad'anne, sometimes gaggawa aikin shaid'anne, saikuma ansha wahala ake shan dad'i, abinda kawai muke kasa fahimta shine riba akan sameta ne a muhalli biyu, walau a duniya kokuwa a lahira, duk wadda bawa ya samu sunanta nasara, amma kowa yafi fata da samun ta duniya, saidai ta lahira ita yakamata mufi d'oki da addu'ar samu, meybe tazame mana tsani Na zuwa inda bamuyi zatoba, hikimar Ubangijice yabaka nasarar anan kokuma a can, Dan babu yanda za'ayi a zalunceka mai kowa da komai sarkin Rahma da jink'ai ya bari, bai yarda da zalunciba, yakuma haramtashi agaremu mu bayinsa”. Wasu k'ananun hawaye suka gangara ta gefen idon Galadima, fuskarsa d'auke da murmushi, yayinda kalaman munaya ke tasiri adukan magudanar jininsa da zuciya, wata nutsuwa ta musamman daya rasa tashiga ratsashi da bashi k'arfin gwiwa, a hankali yace, “ke y'ar baiwace matar Contract”. Dukda maganar k'arshe ta sosa zuciyarta saita murmusa, cikin kuma kwantar da murya tace, “Ni a suwa Mijin contract ”.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83