Chapter 47
Chapter 47
yana d'ora tattausan hannunsa saman nata, cikin wani salon daya saka tsigar jikinta tashi ya kar6ar spoon d'in. Babu shiri ta sakar masa. Yakuma k'asa da murya yana d'ebo abincin da fad'in, “nifa kibarmin shagwa6arnan kokuma humm”. ‘ya k'are maganar da ciza lips yana jifanta da wani kallon mai cike da sirrika’. Waro idanu Munaya tayi tana kallonsa baki bud'e. Abincin ya zuba mata yana kashe mata ido d'aya. Kunya ta kamata, Dan wlhy Galadima bashida kunya ko kad'an, kad'an daga aikinsa ya aikata duk abinda yazo masa a rai d'in, danta San halin kayanta sarai. bata k'ara yarda sun had'a idoba har yagama bata abincin, ya d'akko d'an Basket d'in da drugs d'inta ke ciki yana dubawa. Aunty Mimi data kasa hak'uri ta mik'e tana tawa, “Oh ni Haneefa, dama abinda ya hanaki cin abincin kenan da gaske dai tun d'azu kiketa cuna baki my k'anwa”. Munaya tai saurin jan d'an gyalen dake yane bisa kanta ta rufe fuska saboda kunya dataji, Aunty Mimi ma akwai iya 6aro zance, kuma ta Fiske abinta. Laraba tayi y'ar dariya itama tana bin bayan Aunty Mimi suka fice, itakam dai birgeta sukeyi sosai, komai nasu a nutse. Galadima dake binsu da murmushi ya juyo da kallonsa ga Munaya yana fad'in, “Saiki bud'e fuskar, dama haka kikeso su fita a barki daga ke sai mijinki ko?”. Babu shiri Munaya ta janye mayafin tana d'an hararsa da kwa6e fuska tamkar zati kuka. Ya ta6e baki da d'aukar ruwa ya zuba a cup yana mik'a mata, kauda kanta tayi gefe kamar bata ganshiba. Mik'ewa yay ya koma kusada ita sosai yana sakata jikinsa, “Haba dai yalla6iyan yalla6ai miye na fushin to?”. Munaya ta ture fuskarsa tana fad'in “Ni babu ruwana dakai, ka koma inda ka fito”. Yace, “Oh God Babie na sorry kinji, wani babban uzirine ya rik'eni, yanzu dai ga maganin kisha, sai amin hukuncin laifina”. Munaya ta matso hawaye sannan ta bud'e bakin ya zuba mata maganin ya bata ruwan tashanye, yakuma zuba wani, ahakadai tagama sha. Dawowa yay tagabanta ya zauna yana murmushi, “Dad'ina dake shagwa6a, amin murmushin mana”. Kauda kai Munaya tayi gefe murmushi na kufce mata. Galadima ya dawo da fuskarta suna kallon juna, cikin k'ank'ance idanu yace, “ko kefa sweedy na, kindai hak'ura ko?”. Kaita jinjina masa tana wani far da ido. Hannunta mai lafiyar ya sumbata, yace, “Thanks My Queen, Saura wanka ko?”. Munaya tai k'asa dakai saboda kunya, danta zata ya manta da maganar wankan da Doctor yace tafarayi yau indai zata iya. Murmushi Galadima yayi, dan kunyar tata na sakashi a shauk'i. Kanta a duk'e tace, “Nidai kabarni zan iyayifa da kaina wlhy”. Baice uffanba ya mik'e zuwa k'ofar ya saka key, yazo yawuce cikin bayin dake a d'akin. A sace ta bishi da kallo harya shige, ta lumshe idonta wani farinciki nabin sassan jikinta. tsaf bayin yake, dan kullum cikin gyaranshi ake, hakama kayan ammafani irinsu boket, buta da sauransu komai need yake, ruwa ya saka danya d'anyi zafi dayake akwai wuta, ya fito yabarshi. Har yanzu idon munaya a rufe suke. Saukar Numfashin Galadima da k'amshin turarensa kawai taji a kan fuskarta, ta bud'e ido da sauri, Ashe yana gab da ita, motsawar datayi saiyazama kawai fuskarsu ta manne da juna, hakan yabashi damar aikata yanda yaso cikin sauk'i. Batada za6in daya wuce mik'a masa ragama gaba d'aya, danya cancanci abindama yafi haka a gareta. Tsawon mintuna biyu ya d'ago suna kallon juna, kasa daurewa Munaya tayi ta rufe idonta, yay murmushi gefen baki yana hura mata iska a saman idon. Dole na bud'e idona nakuma sakasu cikin nasa, a hankali ya furta “I love you so much my Munaah”. Murmushi na masa mai kashe ga66an jiki, na matsa kad'an ina bashi Sumba a kumatu, lumshe idonsa yayi yana sauke wani nannauyan numfashi, ya d'ora kaina a k'irjinsa, daddad'an k'amshin turarensa ya shige hancina, nima na lumshe idanu ina shak'a da godema ALLAH. muduka nutsuwa ta musamman ta sauka a zuciyoyinmu. Wayata datai ring ce ya sani d'agowa daga jikinsa na zauna sosai ina kauda fuska saboda kunyarsa. Ganin Samha Ce na d'aga wayar cikeda farin ciki. Galadima mik'ewa yay shima ya lek'a ruwan daya saka, ganin yayi zafi saiya kashe ya juye, surkawa yay, saida yaji yayi dai-dai sannan ya fito yana cire bottoms d'in rigar shaddarsa, hankalin Munaya baya garesa, shiyyasa batasan miyakeyiba, sai ji kawai tayi an amshe wayar tareda yin sama da ita. Da farko ma tsorata tayi, zata saka masa ihu yay saurin cemata “Shiiiii!!”. Ajiyar zuciya na sauke na kallesa, ya kashemin ido d'aya. Murmusawa nayi ina janye idona daga kallonsa, dan naga lamarin nasa na Neman fin k'arfina, koya manta a ina muke oho? harda su cire rigafa. Nidai wannan wanka anyisane kawai dan banida yanda zanyi, dan dana nema yin gardama saiya had'e fuska yana hararata, dole nabarsa yayi yanda yakeso, ya d'auramin towel ya kamo hannuna muka fito, Muduka Kallon Amaturrahman mukai daketa wutsil-wutsil da k'afafu. Na zauna a bakin gadon shikuma ya jawo kujera ya zauna yana rik'o hannuna mai ciwo, fara'ar dake a fuskarsa dukta d'auke, alamar ransa yana 6aci inhar ya tuna tushen ciwon. Cikin son kauda masa damuwarsa nayi murmushi ina d'ora hannuna mai lafiya saman nashi dake rik'e da mai ciwon, d'ago ido yay muka kalli juna, nad'an juya idanuna ina fad'in “yafi k'yau a haka ko?”. Hararata yayi kawai baice komaiba. Nayi k'aramar dariya. Yiyay tamkar zai matsa hannun nai azamar janyewa ina d'ane gadon gaba d'aya dayin y'ar k'arar tsorata, kad'an yarage na haye Amaturrahman. Murmushi yayi har hak'oransa na bayyana. yace, “ga tsoro ga tsiwa”. Nace, “naji dai ba komai”. Bai kuma cewa komaiba, sai murmusawa da yay, da kansa ya shafamin mai ya canjamin riga, dukda kakkauda fuskan kunya danaitayi, shikam ko a jikinsa, kai tsaye yake lamarinsa kuma hankali kwance. A gurguje please😏😜. ********************* Satina Uku a Asibitin aka sallameni, jikina kam sai godiyar ALLAH, dan na warke sarai, saidai y'ar ramar danayi, dakuma ciwon kai dake yawan addabata inhar waje yacika hayaniya. Tunda na dawo sai kuma kewar Galadima ta tasoni gaba, su Fauziyya nata shirin komawa gidajensu, sainaji inama harda mu🤭. Tunda na fito asibiti Aunty Salamah takuma k'aumi wajen bamu kulawa, musamman ma ni, dan ita Munubiya ina asibiti akaita mata nata. Tunda aka sallami Munaya daga asibiti ta koma gida sai yaji zaman k'asarma dukya gunduresa, ganin zai saka kansa a damuwa saiya had'a inasa-inasa yabar k'asar, itama Munaya rana tsaka yazo mata da zancen komawar. Addu'ar fatan alkairi kawai tamasa, da kuma sak'on magungunan Abie, a ranar yaso shiga su gaisa da baba mai kanwa, amma sai akaje wai bayanan, d'ansa yaje kaisa wani k'auye nan kusa gaisuwar Mutuwa da akayi. ............................★ Su momma sunyi farin cikin dawowarsa garesu cikin k'oshin lafiya, sai dai y'ar ramar da yayi. Shima wani matsanancin farin cikine ya kamashi ganin jikin Abie ya k'ara k'yau, yanzu har mitsa hanunsa yakeyi sosai, ga doguwar hira da akanyi dashi batareda ya k'osa ba, ranar sunsha hira sosai, har saida doctor d'in Abie yace subarshi ya huta sannan Galadima ya tafi gida shi da Momma, ranar Aunty Mimi aka bari wajen Abie tunda ita tasan komai. Sabuwar hira Momma da Galadima suka kuma dasawa a gida, dukkan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83