Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 79

Chapter 79

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

shekarunta, ana gama shagalin na Sauban tareda amaryarsa Ni'imatullah d'iyar Mom da biyu, itama ta tare gidan mijinta professor Ibraheem Macid'o, musalta muku yanda mukasha shagali 6ata lokacine. Bayan bikin da kwana biyu Galadima ya fara koya min mota, koya motar da taso zama shiririta, wai dole saidai na zauna a cinyarsa ahaka za'a koyan, banida yanda na iya dole nayi hakan, cikin amincin ALLAH a sati biyu nagama kwarewa, kwana biyu da faruwar hakan na yaye su Amaturrahman bisa dagewar Ubansu akan shima k'annensu yakeso, danga Munubiya da ciki🤭🤣. Dole nayi wannan yaye yara suka koma wajen Momma. Kwanaki 10 cif dayin yayen saiga bak'ona yazo, karkuso kuga murna wajen Galadima, wai hanyar samuwar ciki ta bud'e. Ni dai shiru namasa ban tankaba. Randa kuwa nayi wanka ai babu d'aga k'afa, ALLAH mai iko da falala kuma ya amince masa, koda wata ya dawo babu jini babu alamarsa, hankalina ya tashi na birkice masa, sai yayta tuntsuramin dariya da fad'in “Yarinya an fad'a miki nid'in na wasane, zan zama Abbu a karo na biyu, ALLAH yasa su zama 3+3=6”. Tashinai nabar masa falon ina zun6ure-zun6ure, shikam yayta tuntsura dariya. Nima nayi farin ciki da samuwar cikin, tunda naga hakan shine burin mijina da farin cikinsa, sai kuma fatan ALLAH ya sauke mu lafiya, dan wannan karon dai mun sa6a ni da Munubiya. *_BAYAN WATA 6_* Cikina ya fito sosai, ina samun tattali da kulawar mijina, kai kace wannan shine cikin farko daza'a Haifa masa, ga shak'uwa mai yawa dake tsakaninsa da yaransa, abin akwai birgewa mai yawan gaske. Ranar wata juma'a kawai mukaga an tashi da wani gagarumin biki dabamusan na miye ba a masarautar, dama kusan kwanaki uku kenan bak'i nata sauka, ni dai harna kasa hak'uri na tambayi Galadima, yace, wlhy shima bai saniba. Ana sakkowa daga massalaci sallar juma'a aka hana Galadima shigowa gida, papi ya umarcesa da zuwa ya zauna inda aka tanada dominsa. Mamaki ya kamasa ganin gurin dank'am da jama'a, addu'a kawai aka gudanar papi yabada umarnin fara abinda ya tara mutane, daga baya koma mikenan jawabi zai biyo baya. An umarci Galadima da tasowa zuwa saman daddumar dasu Abie da manyan sarakuna ke zaune, ya zauna a tsakkiya shidai zuciyarsa na faman tsitstsinkewa da bugun mamaki. Turaki ya mik'e a tsanake zuwa gaban mai martaba Sarki Jalaludden Abubakar, yay gaisuwa tare da risinawa sannan ya zare rawanim dake kansa, gaba d'aga wajen aka d'auki kabbara, Abie yay k'asa da kansa yana share hawaye, shidai dan anfi k'arfinsane kawai, amma daba yanke wannan hukuncinba wlhy. tuni bugun zuciyar Galadima ya k'aru ganin Turaki ya nufo garesa, zaiyi maganar papi yay masa alamar yay shiru🤫. Dole ya maida bakinsa ya tsuke yana had'iyar yawu da k'yar. Tsohon Sarki Jalaludden ya taso da taimakonsa Turaki ya cire hular saman kan Galadima aka d'ora masa sabuwa dal, sannan aka fara nad'a masa rawani akai, jikin Galadima sai tsuma yakeyi, ya kafe papi da Abie da ido ko k'yaftawa bayayi, shikad'ai yasan a halin dayake ciki, zufa sai tsatstsafo masa take a kowacce mahudar gashi dake a jikinsa. Tsaf aka gama nad'a masa rawani jama'ar wajen suka d'auki kabbara, yayinda za'a saka masa alk'yabba sai dogarai suka baza riguna ana masa kirari. Galadima yay k'asa dakai idonsa na kwararar hawaye lokacin da kunuwansa ke jiyo masa jawabai daga bakin sank'ira. *_“ALLAH ya d'auki rawani ya maida bisa kan matashi kuma adali tsohon Galadima a yau yazama Sarkin wannan masarauta ta gagara badau bisaga adalcin tsohon Sarki mai murabus a yau, masarautar gagara badau tayi sabuwar amarya, a halin yanzu Mai martaba Muhammad Sameer Saifudden Abubakar shine Sarkin wannan adalar masarauta, ALLAH ya tayashi rik'o, yabashi ikon koyi da k'yawawan halaye irinna manyan wannan gida”._* Tuni waje ya harmutse da surutai, kowa na fad'in albarkacin bakinsa. Galadima kam saida papi ya rungumesa a jikinsa sannan yafara samun nutsuwa, yayinda aka kawo Matawalle shima aka zaunar aka nad'a masa rawanin wazirci, shine zai zama wazirin d'an uwansa Sarki Muhammad Sameer Saifudden Abubakar. Ai tuni guri ya rinca6e, babu maijin zancen wani, kafafen yad'a labarai da social media duksun d'auka, masu murna nayi masu bak'in cikin nayi, (kusan shigabanci, dolene kasamu masoya da mak'iya😭). Mama Fulani da labarin ya Isar mata zarewa tayi, sai surutai take Wanda ba kowa ke fahimtaba, Gimbiya zulfah kuwa yanke jiki tayi ta fad'i wanwar, koda aka zuba mata ruwa ta farfad'o saita kama aman jini zuciyarta yariga ya buga. Ba'a katse su papi daga abinda sukeba aka nemo doctor dazai dubata, saidai bata d'auki wani dogon lokaci ba tare ga garinku nan. Haka duniya take, lokacin da wani ke zuwa sannan wani ke ficewa, hakanne ga gimbiya Zulfah, tatafi a randa Galadima ya zama Sarkin gagara badau.🤴🏿😝😁👍🏻 Ni kaina da labarin zaman mijina Sarki yau babu zato ya zomin saina rikice, na rud'e, ganin lamarin nake tamkar tatsuniya ko mafarki, ga ciki, nama rasa murna zanyo ko kuka. Ban fita a wannan magaginba saiga zancen halin da gimbiya zulfah take itada mama Fulani, saikuma ga abinda ya girgiza kowa shine mutuwarta. ********* Koda aka buk'aci jawabi daga bakin Galadima kasawa yayi, shifa ganima yake a mafarki komai ke faruwa, shima Matawalle ya kasa cewa komai, sai zirar da hawaye kawai sukeyi Wanda hakan ya birge kowa da bada mamaki. Abubuwa sun rinca6e fiye da yanda bakwa zato a masarautar gagara badau, bayan an sallaci gawar gimbiya zulfah aka kaita makawancinta na gaskiya y'ay'anta na kuka da y'an uwanta. Kiri-k'iri ganin mijina ya gagareni har dare, Abdurraheem sakin k'ulafucin Uba sai kuka yake yak'iyin barci, su Amaturrahman da sukayi nasu na lallashesu sai suka kwanta, dan sunsaba da yayi sallar isha'i yana tare dasu, amma yau shiru babu amo babu labari. Nikam sainaji abin yana cizon zuciyata, indai wannan mulki zaisa mijina yin nesa dani bana farin ciki, saigani da kuka rurus. Sai misalin 12pm Sarki Muhammad Sameer yasamu rakkiyar zuwa sashenmu. Ina zaune afalo nayi tagumi naji alamar mutum tsaye a kaina. A firgice na d'ago kaina ganin mijina saina mik'e a firgice tare da fad'awa jikinsa na saki kuka. Shima rungumeni yayi sosai yana sakin nasa kukan, sannan ya d'aukeni cak zuwa cikin bedroom d'in ya ajiyeni a saman gadon, kuma rungume juna mukayi muna cigaba da kukan mu. Tsawon lokaci muna haka, sannan yafara dakatar da nashi yana lallashina. “Munaya kinga abinda su papi sukaimin ko, ni dai banason sarautarnan, amma sunk'i saurarena, wlhy banaso munaya, banaso nidai”.... Yakuma fashewa da kuka. Tausayinsa saiya kuma kamani, nakuma rungumesa tsam a jikina, abinda kaga ya saka Galadima kuka aiba k'arami beneba kuwa. Daure zuciyata nayi na shiga lallashinsa. Na kuma rungume sa sosai cikin nutsuwa ina fad'in, “Mijina ba komai ne ake tuntu6e dashi bisa shiryawa kaiba, wani abun tunkan kasan tuwarmu gudan tsoka rubutaccene a littafin k'addararmu, babu wani d'an Adam da alk'alamin k'addararsa ke a tafin hannunsa, gudun zuciya yafi na k'afafu sauri, idone kawai ke iya banbance fari da bak'i, baki kuwa d'and'ano kawai yake tantancewa, aikin kunne kuwa jine kawai da banbance k'arar sauti, baka tunanin duk mutum mai baiwa ALLAH ke ba damar banbancewar? Irinku kune kuka cancanci mulkin al'umma, domin kuwa bashine burinku ko damuwarkuba, kune zaku iya adalci da tausayin na k'asa daku, ka amince dayin

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});