Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 12

Chapter 12

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

fa ba d'ayaba, sai nace “Ina yini”. Ya amsa da “lafiya. Ina abin cikin kwan?”. Kamar bazan amsaba saidai nace, “waye mai wannan sunan?”. Galadima ya murmusa yana cija lips, “karki damu kwanaki kad'an zakiji wasu ukun ko biyu a jikinki, daga nan saiki tuna mai sunan”. Da sauri nace, “can gasu gada, idanma hakan tafaru to sai dai ga masoyina mai zuwa, wanda yadamu dani, ina maka albishir nasamu mijin aure”. Murmushi Galadima yakeyi yana shafa kansa, yace, “Ayya natayaki murna gaskiya, sai dai shifa mijin ina tayashi jajen rashin iya za6e”. Wani haushine ya kamani, na yanke wayar ina tsaki. Dariya sosai ta kama Galadima, ya ajiye wayar yana fad'in “kujimin yarinya, ke kika kawo zance, miye kuma najin haushin?”. Ta6e baki yayi ya tashi zuwa gaban wardrobe yay shirin barci hankalinsa kwance. _____________ Tunda na yanke wayar sainaji kuka na Neman tahomin, amma na daure na danne abina, komawa nayi cikin d'akin na haye gado, Ayusher tamin magana akan nazo muci gaba dacin abincin amma nace na k'oshi, lallashina sukaitayi itada Feena, nak'i saurarensu, Munubiya kam uffan bata ceminba, hasalima ko kallon inda nake k'inyi tayi, dukda nasha jinin jikina akan haushina takeji saina shareta nima. Har dare muna tare dasu Ayusher, sai bayan isha'i Yaa Marwan yazo d'aukarsu, nafita kawo masa ruwa saboda na freight d'inmu ya cika sanyi, yace kuma bazaisha mai sanyiba, koda na dawo saina tarar basa nan shi da Munubiya, Ayusher tace, yace nakai masa d'akinmu. Ban kawo komai a rainaba na nufi d'akin cikin karsashina, saida naje tsakkiya sannan idona yay mugun gani, daga Munubiya har yaa Marwan da suka farga da shigowata suka d'ago kowanne ya zubamin harara. Babu shiru na dangwarar da ruwan a wajen nima ina murgud'a baki na fice abina............✍🏻 🤣Ya Marwan kamin dai-dai kaida Munubiya🤨 su o'e sai a canja hali, dan duniya saida kud'i lahira kuwa sai da hali🤸🏻‍♀, ko ya kukace my Guys😂😜?. *_Duk wanda yamin magana PC shekaran jiya yaga babu reply yamin afuwa, wayar tawace hawan madara ya kamata, sai kawai ta goge komai, shiyyasa nai zuciya jiya naki muku typing, dan nayi ya goge😢_* *_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻 [7/26, 10:14 PM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* *_💡HASKE WRITERS ASSO...._* *_♦RAINA KAMA...!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_BOOK 3_* 👉🏻9⃣➖🔟 ..............Kwana biyu Galadima ya k'ara suka dawo Nigeria shi da Sauban, burinsa a yanzu ya fuskanci abinda ke gabansa da iyakar k'arfinsa da basirarsa, bai shiga masarauta ba saida ya had'u da baffi yabashi wasu takardu. Dole yay barcin wasu awoyi domin samun nutsuwar gajiyar tafiya, sannan yay shirin fitowa, ya lek'a sashen mai martaba dansu gaisa saiya tarar yanada bak'o, jakadiya sarkin gulma ta gutsiri goronta tana kallon Galadima, “Ranka ya dad'e ai takawa yana tare da bak'one, bak'on kuma Na lura Wanda ba'ason sanin dami yazone, dan kullum ganawar sema k'unshe yakeyi da takawa”. Shiru yamata tamkar bai jiba, danshi mutumne da baya shiga abinda bai shafeshiba, kowa yasan haka a masarautar, shiyyasa Duk makircin masarauta bazaki ta6a samun wani ya sakoshiba, kokuma kawo masa gulmar wani. Ganin haka itama jakadiya sai taja bakinta tayi shiru. Galadima ya mik'e yana kallon agogon hannunsa, “Bara naje, zan dawo anjima”. ba tare da ya kalleta ba yay maganar yay kuma ficewarsa. Da kallon ta bishi tana cigaba da 6allar goronta, tace, “wannan murd'ad'd'en da ace zai saurara dana bashi sirrika da yawa wlhy, amma ina, maganama ta kud'ice a garesa, ka huta wlhy, wai gurgu ya za6i zaman waje d'aya😏”. 😂😂🤭 _______________________★ Kwance yake jikin seat d'in mota idonsa a lumshe, duk yanda yaso ture zancen jakadiya a ransa karyay tasiri ya gaza hakan, sai kaikawo zancen ke masa, tabbas bak'o mai muhimmanci ne kawai zai iya ganawa da mai martaba har cikin turakarsa, to mike faruwa ne haka?, bashida amsa dan haka ya cije lips d'insa, tafiyar tasu yau dagashi sai sarkin mota, ya hana dogaransa binsa, gidan da su Nuren suke ya isa, dukda shi Nuren ma baya nan yaje gida saboda kiran gaggawa da papi yamasa, Muftahu kam dole kullum a Masarauta yake kwana, saida taka tsantsan ma yake zuwa gidan da rana, saboda rashin ganin Harun yanzu motsin kowa lura akeyi dashi. Su Ameer ne suka bud'e musu k'ofa Sarkin mota ya shiga, yanayin parking suka bud'ema Galadima ya fito, cike da girmamawa suka gaisheshi, ya amsa musu da d'an sakin fuska, sannan ya tambayesu Yaya aiki?. Da Alhmdllh suka amsa. Har cikin falon sukai masa rakkiya, babu kowa cikinsa, amma ko ina k'al yake a gyare, ga k'amshi mai dad'i yana tashi. Yayi zama yakai Na 10minutes saiga baba Rabilu shida wani dattijo da zai iya girmarsa kad'an, kokuma wahalace ta girmamawa tsufan nashi oho. shidai Galadima kallon mutumin yake tamkar ya sanshi, amma ya manta a ina. Zama sukayi, cikin girmama juna suka gaisa, sukaima Galadima barka da dawowa, da d'an guntun murmushi ya amsa, har yanzu dai idonsa akan dattijonnan. Lura da hakan da baba Rabilu yayi saiya murmusa, yace, “Ranka ya dad'e ka shaidashi ne?”. Galadima ya hard'e k'afafunsa yana murmushi, yace, “baba rabilu inadai masa kallon Sani kam”. Baba Rabilu yay k'aramar dariya yana kallon dattijon dake durk'ushe a k'asa shima yana Murmushi, sannan ya dawo da kallonsa kan Galadima yace, “Zaka sansa Ranka ya dad'e, amma gaskiya kana tare da k'uruciya lokacin, Sunansa Badi, mahaifinsa shine mai kula da dawakan Sarki a wancan lokacin”. Da sauri Galadima ya sauke k'afafunsa daya hard'e, cikin tsantsar mamaki yace, “Baba Rabilu kana nufin wannan Badi ne?”. Dattijo ya risinar da kansa k'asa alamar girmamawa ga Galadima. Yace, “Nine ranka ya dad'e”. Rasama abinda Galadima zaice yayi. Sai bakinsane ke motsawa alamun yanason maganar amma ya kasa. Sai ido daya tsurama Badi cikeda tunosa a lokacin da shi yake d'an shekara 5 kacal a duniya, dukda bazai yuwu ya iya tuna komaiba, amma tabbas yasan fuskarsa, yasan kuma shine mai kulawa da barga ta dokunan masarautarsu shi da iyayensa, a lokacin inhar baiyi k'aryaba Badi bazai wuce shekaru 33 ko 35 ba. Amma yau gashi zaune gabansa furfura da girman tsufa duk sun bayyana a garesa...... Sallamar Muftahu ce ta katse tunanin galadima, Muftahu ya zauna suka gaisawa da Baba Rabilu, sannan ya gaida galadima, idonsa dai nakan Badi shima. da k'yar Galadima ya amsama Muftahu gaisuwarsa. Badi dakema muftahu kallon sani ya gaisheshi cike da girmamawa (Dan ALLAH yayisa mutum mai yawan rik'o). Muftahu dai kasa hak'uri yayi, ya kalli baba Rabilu yana neman amsa. Murmushi baba Rabilu yayi, ya gyara zamansa yana fad'in, “Yalla6ai baka ganesa bane?”. Muftahu yace, “Banma ta6a ganinsa ba alhaji”. Badi ya kalli Muftahu sannan yay k'asa da kai. Yace, “Nikuwa kaga Na ganeka yalla6ai, dan bazan manta sanda kukan rako Yarima ba idan za'a fita da shi bakin ruwa shan iska, ka kan nace sai a doki d'aya zaku tafi kai da sauran abokan nashi”. Murmushi Muftahu yayi, ya kalli Galadima dayay shiru yana kallon Badi kawai, yasan yana tuna bayane, kuma akwai tambayoyi fal ransa sai dai ya kasa furtawa, janye idonsa yayi ya maida ga Badi, yace, “Amma Badi minene ya faru da kai harka bar masarauta? dan bazan iya tuna wani abuba a wad'ancan shekarun namu, yanzu kuma daga ina kake?”. Zama Badi ya gyara. Yace, “lallai labarine

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});