Chapter 40
Chapter 40
rok'o muka fahimtar dashi manufarmu, amma saiya fusata, yakuma jamana gargad'i karya kuma ganin koda masu kama damune a masarautarsa, kuma lallai shi da kansa zai nemi shugaban k'asa mai mulkin wancan karon ya sanar masa manufarmu, munta k'ok'arin fahimtar dashi amma yak'i saurarenmu, daga k'arshema saiya koremu daga masarautarsa, wannan shine dalilinmu Na shirya cewar zamu kasheshi, amma daga baya saisu Mike suka kawo mana shawarar masa allurar poison, bamusan ya akayi wannan d'an jarida ya San da shirinmuba harya biyomu inda muka ke6e dan tattaunawa, munta bibiyar rayuwar d'an jarida amma bamu sameshiba, marigayi tanderu ya k'arfafa mana gwiwa akan karmu fasa yin shirinmu, waziri zai kula da motsin kowa a masarautar, a ranar Waziri yatafi da wannan allurar guba, dakuma asubahin washe gari yacika mana aiki, bamu sakejin labarin d'an jarida ba saida Sarki Saifudden yacika watanni uku da fara jiyyasa, saigashi cikin yaranmu wani ya samoshi, sun bishi dansu kasheshi amma saiya 6oyema ganinsu, Ashe yabi motar mai dawakai ne daya gani akasuwa yazo sayen abincin dawakai. Wani bawane yaga wannan d'an jarida tareda mai dawakai a barga, shikuma bawan yana d'aya daga cikin wad'anda waziri ya baza a masarautar domin saka ido, dan yasan komai Daren dad'ewa d'an jaridarnan saiya so kawo camera d'in a masarautar, a lokacin yasaka ancigaba da bin d'an jarida, yakuma k'yale su mai dawakai har zuwa dare yaje garesu. Camera dai tacigaba da walagigi, har muka samun kashe d'an jarida, a lokacin bamusan Alhaji Rabilu munafuki bane yasan komai, har yazo ya shiga jikin mu da cewar yazo shiga tafiyarmune, Ashe munafuki yasan komai, dan bamuga fuskarsa ba lokacin damukaje fadamar bayan gari, shi Badi shikad'ai muka gane tunda dama waziri ya sanar mana. Muncigaba da Neman Badi har tsawon shekaru 4 amma ko labarinsa babu, saidaga baya cikin shekara ta biyarne muka samu labarinsa a wani k'auye, munta bibiyar rayuwarsa daki-daki, har randa yabaro k'auyen muka cigaba da binsa, lokacin daya farga damu shine ya gudu Alhaji Auwal Fharuk ya bigeshi da besfa, lokacin da yaranmu sukazo shi Alhaji Auwal Fharuk saiya gudu, dan haka basuga fuskarsa ba, shikuma Badi ya suma, a tunaninsu ya mutu, suka daddike gawarsa suka dawo suka sanar mana babu camera d'in a hannunsa, sannan kuma ya mutu, amma suna k'yautata zaton yabama wani kafin zuwansu, kilama mai besfa d'in daya bigeshine, bamu hak'uraba, mun cigaba da lalube dukda bamusan wanene ba, ana cikin hakane kuma muka samu damar kar6ar mulki, burinmu ya cika, Alhaji Labaran Khacia yazama shugaban k'asa kamar yanda muka tsara, dan dukya fimu arzik'i a lokacin, saidai kuma yana shekara biyu kacal da hawa mulki Alhaji Lawan tanderu ya rasu sakamakon had'in mota, shugabanci k'ungiya yadawo hannuna, Tanderu bai dad'e da rasuwa ba shima Alhaji Labaran yakwanta jiyya, kwanansa baifi 6 ba ya mutu shima, lallai wad'annan rashin sun girgizamu matuk'a, har yanzu kuma mun kasa mantawa. Tun daga wancan lokacin duk Wanda zaiyi shugabanci a k'asarnan da taimakonmu yake yinsa, kuskuren da mukayi shine mantawa da Sarki Saifudden nada d'a namiji, kuma komai Nisan lokacin zai iya Girman da zaibi ba'asin ciwon mahaifinsa, gaba d'aya sai hankalinmu ya k'arkata ga son samun Camera kawai, a tunaninmu damun sameta dukkan magana ta k'are. Har lokacin da muka fahimci Alhaji Rabilu shima munafukinmu ne, shine muka titsiyeshi akan camera, amma yace bai saniba, Alhaji Shehu ya d'auki mataki a kansa, dan dukkan Wanda yasan da zancen camera burinmu mu kaudashi kawai magana ta k'are, Bamu farga da yarima Sameer ba sai lokacin da ya fara bibiyarmu, Ashe a time d'in shi C.I.D nema, mukuma duk bamu saniba, da taimakon d'an waziri Harun muka samu bayanan sirrin Documents d'in shi yarima Sameer, dan haka Kabiru Ibraheem da shima masanin Computer ne ya shiga yimasa kutse, dan munason musan shin yarima Sameer yana sane da mune? Inhar yana sane damu mukaudashi shima. Saidai kuma yaron ya wuce da dukkan tunaninmu, yanda muke bashi wahala haka shima yayta bamu wahalar, aka cigaba da yak'in sunk'uri, kowa baya ganin kowa kenan, kwatsam saiga Alhaji Shehu Darma yazo mana da labarin Camera fa Na hannun Alhaji Auwal Fharuk, wannan yasa muka koma bobiyarsa, mun masa tayin dukiya mai yawa sau babu adadi amma yak'i saurarenmu, munma rayuwarsa barazana nanma a banza, daga k'arshe muka nemi kasheshi shima, amma ya tsira bai mutuba, Yarima Sameer ma ya d'aukeshi zuwa India, dukda a India d'inma bawai mun barsa bane, canma musha bibiyarsa da barazana, amma taurin kansa yahanashi bamu har zuwa yau d'inan, munsha kaima rayuwar Sameer hari shima ta 6angarori da dama amma yana shallakewa cikin tsarewar Ubangiji, wannan shine abinda ya faru yamai shari'a”. Babu abinda kakeji a kotunnan sai sauke ajiyar zuciyar jama'a, alk'ali yace yaje ya zauna. Yad'anyi rubuce-rubucensa sannan yace “kotu tana buk'atar son ganin Waziri a gabanta”. Waziri Munafuki, saikace an tsamo 6era a ruwa haka yafito yana wani kakkange fusaka, shima inda kowa ke tsayuwa yaje ya tsaya, bayan ya fad'i sunansa Alk'ali ya jeho masa tambaya. “humm Waziri, kotu zataso sanin minene ya had'aka da Sarki Saifudden da zafi haka? Harka za6i cutar dashi wajen had'akar wasu bare can?”. Waziri yakuma k'asa da kansa, murya a raunane yace, “maganar gaskiya son zuciyane kawai ba wani abuba, danshi mai martaba ya kasance mutum mai zama akan ra'ayinsa, sannan mai gaskiya da sauk'in hali, nikuma nacika tsugunne-tsugunnen rashin gaskiya, sannan inada sonkai, komai nafison a masarautar gagara badau a fifitani saman kowa, akuma girmamani, wannan halin nawa nason handame komai Na mutane yasaka kullum Sarki kemin nasiha dason gyara halayyata, nikuma nak'i saurarensa, saina kallon hakan danake matsayin cin zarafina yakeyi a kullum, lokacin dana fara ganin take-taken Sarki nason tu6eni sai hankalina ya tashi, nafara Neman mafita, (kusan dai ita sarautar waziri ba gadonta akeba a k'asar Hausa) ina cikin fad'i tashine Neman mafitane wad'annan turawa biyu su Mike sukazo min da tayin mak'udan kud'i da wasu alk'awura, bisa sharad'in sonjin sirrin masarautar gagara badau, babu wani 6oye-6oye Na sanar musu komai, karaf sai'a kunnen wani dogari amintacce ga Sarki, shine yaje ya sanar masa komai, Sarki yakirani har turakarsa ya titsiyeni, yaci mutuncina iyakar iyawarsa, wannan Abu shine ya fusatani, naje Na samu su tanderu muka had'e, dan aganina Sarki ya tozartani a masarauta, tunda gashi yana niyar tu6eni kamar yanda ya fad'amin, nikuma aganina kafin ya tu6eni ya tozartani gara ni nahad'a kai da wad'anda zamu tu6eshi, wannan dalilinne yasakani basu had'inkai, akuma washe garin dana amso allurarna da asuba muna salla, anyi sujudar farko ta sallar asubahi Na kafa masa allurar a cinya Na tsiyaye ruwan kafin a d'ago, amma Sarki dukda nasan yaji zafi, yakumasan cutar dashi akeyi baiko motsaba, saida aka idar da sallar dashi, anayin sallama ya juyo muka had'a ido, baisamu damar min maganaba ya yanke jiki ya fad'i, tun daga wannan lokacin yakoma shida gawa banbancinsu kad'annane, to dama shima wazirin Sarki Abdul-Fatah kuma d'an uwansa shima da nashi shiri akan Sarki Saifudden, dan yanajin haushin ba jikokinsa y'ay'an y'arsa gimbiya Marawuyane (mama Fulani) zasuyi mulkiba, dan lokacin su zaharadeen sunyi had'arin jirgi sun mutu, to burinsa kullum ya durk'usar da Sarki Saifudden jikansa Jalaludden ya gaji mulki, wai tunda gimbiya Kahdija matar Sarki Abdul-fatah ta gaje musu masarauta, shima dolene d'iyarsa mama
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83